Babangida Maina
10/04/2026
Daya daga cikin rijiyar da Annabi SAW, yayi alwala da ruwan ta dake a garin Madinah.
Annabi SAW ya taɓa yin alwala da ruwan rijiya, kuma ya sanya mata suna Al-Yaseerah. A nan ne aka wanke sahabin nan Abu Salama bin Abdul-Asad Al-Makhzumi (Allah Ya yarda da shi) lokacin da ya rasu sakamakon raunukan da ya samu bayan Yaƙin Uhud. Shi ne ɗan’uwan Annabi ﷺ ta fuskar shayarwa, kuma ɗan goggonsa Barrah bint Abdul-Muttalib.
Masanin tarihi Al-Samhoodi ya ambaci cewa sunan Al-Ahn yana nufin ulu mai launi. Haka kuma Al-Mutari ya ce ya ga a rubuce cewa rijiyar da aka ambata a littattafan tarihin Madina ana kiranta Rijiyar Al-Ahn a yankin Al-Aliyah, kuma ana noma a cikin ta, kuma akwai bishiyar Sidr (magarya) a kusa da ita.
Ya kuma ce: wannan rijiyar sananniya ce a yankin Al-Awali, tana da kyau sosai, an hako ta a cikin dutse, kuma tana da bishiyar Sidr a gefenta. Amma daga baya an yanke wannan bishiyar.
Allah SWT ya kara mana soyayyan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam, ya bamu ikon ziyartan wannan wuri albarkan Annabi SAW. Amiin Yaa ALLAH
Daga: Fityanu Islamic Centre
Rana: April 10, 2026
18/03/2026
Wannan shine masallacin da Manzon Allah SAW ya tsaya tare da sahabbai domin yin Sallah a cikin sa.
Kwayataccen Masallacin Masjid Suleiman wanda aka gyara shi kuma aka sabunta shi. Tarihi ya nuna cewa Annabi Muhammad ﷺ ya tsaya da sahabbai a wannan wuri, ya kuma faɗa musu cewa Annabi Sulaiman dan Dawud ya taba zama a nan, shi ya sa aka sa masa suna.
Masallacin yana da ƙaramin girma, yana ɗaukar kusan mutane 30–36, kuma an gina shi da duwatsu da kayan gargajiya. Yana kusa da Wadi Nakhab a hanyar Taif zuwa Al-Baha. Har ila yau, yana jawo baƙi da masu yawon buɗe ido.
Allah SWT ya bamu ikon ziyartan wannan wuri, albarkan Annabi SAW. Amiin Yaa ALLAH
Daga: Fityanu Islamic Centre
March 18, 2026
RUFE TAFSIRIN AL'QUR'ANI MAIGIRMA DAGA MASALLACIN MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI, TUDUN WADA, KADUNA.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Manawachi Pantami
Gombe
760101