Jewel Multimedia

Jewel Multimedia

Share

Jewel Multimedia Services

A modern media platform dedicated to telling stories that create impact through news, digital communication, and community development.

25/12/2025

DA DUMI-DUMI: Ali Nuhu ya zama Ambasadan kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, bayan kulla yarjejeniyar Naira miliyan 30 na tsawon shekara guda

ABBA PANTAMI DATA LTD ya sake rage muku farashin Data zuwa Naira 500 akan kowane 1GB, ku hanzarta ku sauke Application din, domin ku more garabasa.

Duk wanda ya sayi Data mai 30DAYS a Application din ABBA PANTAMI DATA LTD to sai tayi kwanaki 30 sannan za tayi Expired. Akwai bambanci tsakanin Expired da kuma karewa.

Matukar kuna amfani da Application din ABBA PANTAMI DATA LTD da zaran ka hadu da matsalar network ko makalewar kudi kana yiwa customer care dinsu magana anan take zasu gyara maka.

Idan baka taba amfani da Application din ba ka gwada, idan ka dade baka yi amfani dashi ba ka sake gwadawa a yanzu domin tabbatar da ingancin shi.

Kuyi Download din Application din ABBA PANTAMI DATA ta wannan link din a PlayStore da kuma AppStore

👇👇
Ga link din PlayStore
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.abbapantamidata.app

Ga link din AppStore
https://apps.apple.com/us/app/abba-pantami-data-ltd/id6744061271

Mai bukatan karin bayani, ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp;
09138275183
08126081967
07046868000

Abba Sani Pantami
07061347599

Photos from Jewel Multimedia's post 05/12/2025

Jega Ya Gargadi Matasa Su Shiga Siyasa Ko Najeriya Ta Fuskanci Hatsarin Mulkin Danniya

Daga Muhammad Chigari Kumo

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, ya yi kira mai ƙarfi ga matasan Najeriya da su ƙara shiga harkokin siyasa, yana jan hankalin cewa ƙasar na iya karkata zuwa mulkin danniya idan matasa ba su tashi tsaye ba.

Farfesa Jega ya yi wannan gargadi ne a jiya yayin gabatar da takarda mai taken “Zabe da Kyakkyawan Mulkin Dimokuraadiyya a Najeriya” a taron jawabin ilimi da Jami’ar Tarayya ta Kashere (F*K) ta shirya a dakin taronta na Multipurpose Hall.

Ya ce matsalolin mulki da Najeriya ke fuskanta a yau na da alaƙa kai tsaye da matasa, kasancewar su ne ginshikin cigaban kasa. Ya jaddada cewa rashin shiga harkokin siyasa da zabe na barin fagen siyasa a hannun mutanen da ke neman moriyar kansu maimakon cigaban kasa baki ɗaya.

A nasa jawabin, Babban Editan Premium Times, Dapo Olorunyomi, ya soki yadda ake gudanar da zaben fidda gwani ta hanyar kuɗi da kuma dogaro da kotuna wajen tantance sakamakon zabe. Ya ce irin wadannan dabi’u na rage amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa babban kalubalen siyasar ƙasar shi ne tabbatar da cewa tsarin zabe yana amfanar da al’umma.

Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere, Farfesa Umar Pate, wanda ya bude taron, ya bayyana shi a matsayin muhimmin mataki ga jami’ar da ƙasar, musamman a lokacin da ake neman sabunta dimokuraɗiyya da gina cibiyoyin gwamnati masu ƙarfi. Ya ce taken taron ya dace da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.

Farfesa Pate ya kara da cewa jami’o’in gwamnati suna da muhimmiyar rawa wajen gina matasa masu ƙwarewa da kuma wayar da kan jama’a kan dimokuraɗiyya da shugabanci nagari.

Shugabannin jihohin Gombe da Taraba sun aika da sakonnin gaisuwa ta hannun Chiefs of Staff dinsu.

Tun kafin taron, Farfesa Jega ya ziyarci muhimman sassa na jami’ar, ciki har da Kwalejin Kimiyyar Likitanci, dakin gwaje-gwaje na zamani, sabbin dakunan karatu da aka gina, da Gidan Watsa Labarai na jami’ar.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Gombe
1238