Academic Forum FUD Chapter

Academic Forum FUD Chapter

Share

06/10/2024
02/09/2021

MATASAN MU A YAU

Da farko dai ba komi bane yasa zanyi wannan rubutu mai taken "Matasan mu a yau", sai dan duba da nazari danayi akan wadansu matsalolin da suke damun mu wato mu matasa.

Su wa 'yannan matsalolin sunyi matukar tasiri wajen jawo mana rashin cigaba a cikin al'umarmu da kuma al'amuranmu na yau da kullum..

Ina ta ambatan matsaloli to su wa 'yannan matsalolin yaya suke, a Ina suke kuma guda nawa ne ? To a takaice de kuma a tina nina na zakulo guda uku wanda kuma sune:

> GAGGAWA: Gaggawa tana daya daga cikin matsala dake kawo mana koma baya a cikin al'amuran mu na yau da kullum. Yanzu idan dan adam musamman matsahi ya kasance cikin gaggawa to zaka same shi kullum cikin bacin rai, to miye dalilin bacin ran ? Dalilin shine yanaso yaga ya samu wani abu dayake so to amma yayi gajin hakuri ya manta dacewa Allah shine mai yin komai musamman ga masu hakuri, Ya Kai matashi dan uwa na zamo mai hakuri akowane lokaci to insha Allahu zaka ga dukkanin al'amuranka suna tafiya yanda ya kamata.

> BURI: Buri wani abu ne shima muhimmi dake taka rawa wajen dakile matashi samun cigaba a al'amura musamman idan akace yayi yawa.

Abin da zamu duba a nan shine idan akace kacika buri to fah zaka kare ne kullum cikin cizon dan yatsa. Saboda haka, dan uwana matsahi ka zamto mutum mai karamin buri kada ka zamto mai babban buri ma'ana kar kace baka da gashin wane se kayi kitson wane.

> TSORO: To fah anzo wajen ita wannan kalma ta tsoro da kajita ma kasan ana nufin rashin zuciya. To Kai miye ne amfanin ka zamo mai tsoro ko mai kunyar yin wani abu da zai taimakeka rayuwarka idan fah ka kasance ciki tsoro da shakku to gaskiya bazaka ga wani cigaba bah a al'amuranka..

Zama mai dogaro da kaima baya yuwuwa se mun cire tsoro a zukatanmu dole. A matsayi na na matsahi mai kuma son naga na cika wasu buri ka nawa to kuwa bazan zamto cikin tsoro bah, idan ka zamto a cikin tsoro to fah see hankali, kai shifa tsoro zai iya hana ka fita neman koda na sabulu ne.

Want your school to be the top-listed School/college in Dutse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Telephone

Address


Ibrahim Aliyu Way, Bye-Pass
Dutse