Excellency DailyTrust
09/03/2026
A LAHADI......
Ga halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya........
IRAN
Wani harin jirgi maras matuƙi na Iran yayi ajalin sojin Amurka 7 a Kuwait, tare da jikkata wasu da dama da lalata dukiya mai yawa ( Iran Military )
MALAYSIA
Firaministan Malaysia yace hare haren da Amerika da Isra'ila suke kaiwa Iran, take hakkin dan Adam ne da kuma keta dokokin ƙasa. ( Irna News Agency )
IRAN/KUWAIT
Iran ta kai wani mummunan harin jirgi maras matuƙi zuwa ginin social building dake Kuwait, da kuma na'urar kare harin sama a sansanin Al'salam na Amurka dake Kuwait ɗin. ( Iran English )
SOUTH KORE/SPAIN
Dandazon masu zanga zanga a biranen Seoul da Malaga a ƙasashen sun fito kan tituna suna nuna adawa ga Amurka da Isra'ila, suna dauke da kwaleyen da aka rubuta Iran tana da ikon kare kanta. ( Irna News Agency )
US/ISRAEL
Sun kaddamar da hari kan wata matatar mai a birnin Tehran na Iran, abinda ya haddasa malalar man fetur a kan tituna tare da tashin gobara. ( Al'Arabiyya News )
IRAN
Ana hasashen ƙasar Iran ta zaɓi sabon shugaban addini a hukumance sai dai har yanzu bata bayyana sunan sa ba. ( Gulf News )
AMURKA
Trump yace yanada hujjar tura dakarun ƙasa zuwa Iran domin cimma burin sa na hamɓarar da gwamnatin kasar. ( Donal Trump )
US/BRITISH
Trump yace Ingila ta bashi kunya akan matsayar data ɗauka a yaƙin Iran, bayan da Birtaniya tace dole ne ayi taka tsantsan domin gudun keta dokar ƙasa. "amma masu sharhi na ganin Ingila tana gudun asarar ne bayan da Iran ta kaddamar da hari akan sansanin sojojin ta dake Cyprus" ( Pentagon News )
UAE
Daular Larabawa tace Amurka ta kakkaɓo mizayil 16 na Iran data harba Abu Dabi ( Gulf News )
IRAN
Ta sake kai harin mizayil sansanin sojin saman Amurka a Bahrain, ana fargabar mutuwar gomman sojoji da jikkata wasu da dama ( TRT Word )
Idriss M Idriss Damaturu Ɗan jarida ✍️
04/07/2025
Memories♥️📌
01/10/2024
2nd
25/05/2024
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Address
Kanawa, Kirfi
Bauchi