Bauchi post

Bauchi post

Share

31/12/2025

DA DUMI-DUMI: Sanata Abdulaziz Yari, ya sayi hannun jari mafi girma a kamfanin lantarki na Geregu Power, wanda ya siya kimamin Naira Tiriliyan 1.125.

Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ɗan siyasa mai tasiri a Najeriya, ya zama mai rike da kaso mafi rinjaye a kamfanin Geregu Power, bayan wata babbar yarjejeniya ta dala miliyan $750 wadda ta kawo ƙarshen ikon Femi Otedola akan kamfanin.

MA’AM Energy Limited, kamfanin da Yari ke jagoranta, ya sayi kashi 95% na hannun jari a Amperion Power, wanda shi ne ke rike da yawancin hannun jari na Otedola a Geregu Power. Hakan ya bai wa Yari damar samun kashi 77% na cikakken hannun jari a kamfanin.

Yanzu haka, Abdulaziz Yari ne shugaban rukunin kamfanin Geregu Power — daya daga cikin manyan kamfanonin lantarki da ake bibiya sosai a kasuwar hada-hadar hannun jari a Najeriya.

Kamfanin yana da ƙarfin samar da wutar lantarki har megawatt 435. A watanni uku na ƙarshe zuwa Satumba, Geregu Power ta samu karin ribar har Naira biliyan 11.2 kafin haraji — karin kashi 82%. Hakanan, kudaden shigar kamfanin sun karu da kashi 37% zuwa Naira biliyan 43.8.

Wannan sauyi na nuna sabon salo a kasuwar makamashi ta Najeriya, inda 'yan siyasa ke shiga harkokin kasuwanci na babbar riba

Rahoton African billionaire.

Photos from Bauchi post's post 14/04/2025

Muhammad Sani Dattijo Mataimakin Gwamnan CBN, Ya Bayyana ƙoƙarin da suke Don rage Hauhawar Farashin kayayyaki da Inganta Tattalin Arzikin Najeriya a Taron JP Morgan na 2025

A yayin wani taro mai matukar muhimmanci da aka gudanar karkashin inuwar JP Morgan Forum a shekarar 2025, Muhammad Sani Abdullahi, Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Kan munufofin Tattalin Arziki ya bayyana cikakkun manufofi da tsare-tsaren da za su taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

A cikin jawabin nasa mai zurfi da hangen nesa, Muhammad Sani Abdullahi ya tabo batutuwa masu sarkakiya da s**a shafi tsarin musayar kudi, hauhawar farashi, da kuma gina tubalin ci gaba mai dorewa. Ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya na daukar matakai masu karfi domin daidaita musayar kudin waje da na gida, tare da saukaka harkokin kasuwanci da janyo hannun jari daga ketare.

“Manufofin da muke aiwatarwa sun mayar da hankali kan daidaita kasuwar musayar kudi da kuma karfafa gwiwar masu saka hannun jari,” in ji shi. Ya kara da cewa, irin wannan sauye-sauyen na nuni da alamar ci gaba, duba da yadda ake samun cigaba a matsalolin da s**a dabaibaye tattalin arzikin kasar a baya-bayan nan.

Dangane da hauhawar farashi, Sani Abdullahi ya jaddada cewa CBN na aiki tare da sauran hukumomin gwamnati domin rage radadin matsin tattalin arziki da ake fama da shi, Musamman ta fuskar abinci da albarkatun yau da kullum. A cewarsa, an dauki matakan gaggawa wajen kara samar da kayayyaki da tabbatar da daidaito a farashin su a kasuwa.

Jawabin nasa ya samu karbuwa sosai daga mahalarta taron, inda aka yaba da irin hangen nesan da ya gabatar, musamman game da bukatar hadin gwiwar bangaren gwamnati da na masu zaman kansu wajen gina ingantaccen tsarin tattalin arziki.

KBC Hausa

03/08/2024

Kungiyar Matasan Arewa Ta janye Daga Zanga-Zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan

Kungiyar Matasan Arewa a ƙarƙashin Jagorancin AMB Abdul Hameed Danbature. a Hukumance ta bayyana cewa ta janye Daga zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar Saboda shawarwari da s**a samu Daga Malamai da fastoti kan mahimmanci tattaunawa da Gwamnati a maimakon Zanga-Zangar da ake yi

"Kungiyar Matasan Arewa Youth Assembly for Good Leadership ta umurci kodinetocin na jihohi 19 da su dakatar da Gudanar da zanga-zangar lumana da ake yi a fadin kasar nan. "A maimakon haka, Ƙungiyar Matasan ta ba da shawarar yin tattaunawa mai ma'ana da Gwamnatin tarayya don magance matsalolin da ke faruwa a halin yanzu.

Sa Hannu Ambassador Abdul Hameed Danbature Shugaban Ƙungiyar Arewa Youth Assembly for Good Leadership

24/06/2024

Dangote ya zargi kamfanonin mai na kasa da kasa (IOCs) da yin magudin farashin danyen mai tare da ƙoƙarin hargitsa matatar mansa da gangan.

Devakumar Edwin, Mataimakin Shugaban Kamfanin Mai da Gas na Kamfanin Dangote Industries Limited (DIL), ya yi zargin cewa IOCs da ke aiki a Najeriya na yin zagon kasa ga ci gaban aikin matatar mai da man fetur na Dangote.

Edwin ya bayyana haka ne da taron Editocin Makamashi yayin wani taron bita na yini daya da kungiyar Dangote ta shirya.

Yayi nuni da cewa da gangan IOCs na kawo cikas Ga yunkurin da matatar ta ke yi na siyan danyen mai ta hanyar yin tsadar farashi sama da farashin kasuwa. Wannan lamarin ya tilasta matatar da shigo da danyen mai daga ƙasashe masu nisa kamar Amurka, wanda hakan ya haifar da tsadar kayayyaki.

Edwin ya ce, “Yayin da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ke kokarin ganin ta ware mana danyen man fetur, da gangan IOCs na kawo cikas ga kokarin da muke na sayen danyen mai a cikin gida.

“Ya kamata a tuna cewa a kwanan baya NUPRC ta gana da masu hako danyen mai da masu matatun mai a Najeriya domin tabbatar da cikakken bin Domestic Crude Oil Supply Obliging (DCSO), kamar yadda aka bayyana a karkashin sashe na 109 (2) na dokar masana’antar man fetur (PIA). Da alama manufar IOCs ita ce tabbatar da cewa matatar man mu ta gaza.

"Ko dai suna neman kari mai yawa ko kuma suna da'awar cewa ba a samun danyen mai. A wani lokaci, mun biya $6 sama da farashin kasuwa.

"Wannan ya tilasta mana rage kayan da muke hakowa da shigo da danyen mai daga kasashe har zuwa Amurka, wanda hakan ya kara tsadar kayayyakin da muke samarwa."

KBC Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Ran Road Bauchi
Bauchi