Albarka Reporters Hausa
11/03/2026
Ƙungiyar ɗaliban ƙaramar hukumar Alkaleri, wato Alkaleri Local Government Student Association of Nigeria (ALSAN) a turance, ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Comrade Abdurrazak Gambo Musa, ta ƙaddamar da rabon kayayyakin makaranta ga ɗalibai da makarantu a ƙananan hukumomin Alkaleri da Kirfi na jihar Bauchi.
A yayin rabon kayayyakin, ƙungiyar ta raba littattafan rubutu guda dubu biyar (5,000), jakunkunan makaranta guda 200, lunch box guda 100, allunan rubutu na white board guda 100, tare da fensir, biro, marker da sauran kayan da ake buƙata a makaranta.
An raba kayayyakin ne ga makarantu sama da sittin (60) da ke cikin ƙananan hukumomin Alkaleri da Kirfi, inda ɗalibai da malamai s**a amfana da tallafin.
Da yake jawabi yayin rabon kayayyakin, shugaban ƙungiyar ta ALSAN Comrade Abdurrazak Gambo Musa ya bayyana cewa shirin na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na tallafa wa harkar ilimi domin inganta koyarwa da karatu a yankin.
A cewarsa, “Manufar wannan rabon ita ce taimaka wa ɗalibai su samu kayan rubutu da sauran kayayyakin makaranta domin ƙarfafa musu gwiwar neman ilimi.”
Ya kuma bayyana cewa rabon kayayyakin ya samu ne bayan tallafin da ƙungiyar ta samu daga ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Alkaleri/Kirfi, Hon. Alhaji Kabiru Yusuf Alhaji (Makaman Duguri), wanda ya bayar da gudunmawar kayayyakin da aka raba.
Taron rabon kayayyakin ya samu halartar shuwagabannin ilimi na ƙaramar hukumar Alkaleri, wakilan ɗan majalisar na Alkaleri da Kirfi, da kuma ɗalibai daga makarantu daban-daban a yankin.
Masu halartar taron sun yabawa ƙungiyar ta ALSAN da kuma Hon. Kabiru Yusuf Alhaji bisa wannan tallafi, inda s**a bayyana cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa ilimi tare da ƙarfafa gwiwar ɗalibai a yankin.
01/03/2026
Almajiran Shaikh Zakzaky Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Ƙasar Iran A Garin Bauchi.
A ranar lahadi almajiran Shaikh Zakzaky na garin Bauchi sun fito domin nuna goyon bayansu ga ƙasar Iran tare da Allah wadai da kashe jagoran juyin juya halin Musulunci ta Iran Sayyid Khamene'i.
Gangamin ta samu halartar maza da mata inda ta karaɗa wasu daga cikin titunan cikin garin Bauchi a yammacin yau lahadi, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi jagoran tafiyar a Bauchi shi ya jagoranci gangamin, wanta aka fareta daga unguwar Shagari zuwa Masallacin Ajiya duk a cikin garin Bauchi.
08/10/2025
SANARWA TAREDA CIKIYA
Wani matashi ɗan asalin ƙaramar hukumar Alkaleri mai suna Hamza, ya bar gida tun shekaru 15 da s**a gabata da niyyar zuwa aikin tuka mashin (achaba) a Bauchi, amma har zuwa yanzu ba a sake jin duriyarsa ba, kuma ba a san inda yake ba.
Iyayensa da ‘yan uwansa suna cikin damuwa matuƙa, saboda haka ana roƙon al’umma da idan Allah Ya sa wani ya gan shi a wani wuri, ya taimaka a kawo shi Alkaleri gidan sarki, ko kuma a tuntubi ‘yan uwansa ta waɗannan lambobin:
📞 07068226224
📞 08035198814
Allah Ya taimaka a samu shi lafiya.
Ameen. 🙏
Daga Ina Kuke Bibiyar Ƙafar Albarka Reporters Hausa ?
11/05/2024
Masha Allah: Musulunci ya samu karuwa
Tun ba yau ba wannan matashiya 'yar kabilar 'Igbo' ke son komawa addinin musulunci amma mahaifiyarta ta ki amincewa. Cikin ikon Allah, yanzu haka mahaifiyarta ta amince da hakan wadda tuni har ta karbi kalmar shahada kuma aka gabatar da ita ga al'ummar da ke barikin sojoji na Ojo da ke jihar Lagos, inda take da zama.
Albarka Reporters Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Bauchi