Dr Usman Azare

Dr Usman Azare

Share

Photos from Dr Usman Azare's post 21/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA
DARASI NA GOMA (10)
CUTAR TETANUS( LOCKJAW)
Mecece tetanus?
cutace wacce ƙwayar hallita ta bakteriya mai suna Clostridium teteni take haddasawa in ta samu shiga cikin jiki mai zurfi ta gurin rauni/ciwo. Cutace mai tsananin hatsari da ka iya kai ga rasa rayi. Ƙwayar cutar tana rayuwa a cikin ƙasa, ƙura da takin gargajiya ko bayan gari. Tana shiga cikin jiki lokacin da mutane ko dabbobi s**ayi hatsari ko wani abu mai tsatsa ko datti ya yankesu/ soke su.
ABUBUWAN DA KE JANYOWA A KAMU DA CUTAR( PREDISPOSING FACTORS)
*s**a da wuƙa ko wani abu mai tsini
*taka ƙusa ko wuƙa mai tsatsa
*Cizo daga wata dabba k**ar kare
*Hatsari da abin hawa
ALAMOMIN CUTAR AJIKIN MUTANE DA DABBOBI
yawan ci alamun suna farawa k**ar sati daƴa bayan an kamu da cutar kuma sun haɗa da:
*sanƙarewar jiki(muscles stiffness)
*ƙamewar baki(lock jaw)
*karkarwar jiki(muscles spasms)
* gagara cin abinci da shan ruwa
*mimmiƙewar ƙafa(extended limbs)
* gagara miƙewa da takawa
* ƙaruwar bugun zuciya da numfashi
* Zazzaɓi
* Rashin son motsi ko hayaniya komin ƙanƙantar ta

YANDA ZA A GANE AN KAMU DA WANNAN CUTA (DIAGONOSIS)
*tarihin jin ciwo
*alamomin da muka lissafa a sama
*gwajin jini
*zaƙulo ƙwayar hallitar a gurin da a kaji rauni(bacterial isolation)

MAGANI
Idan aka ga alamun wannan cuta ko wasu dalilai s**a faru daka iya haddasa wannan cuta to a yi saurin garzayawa da mutumin ko dabbar asibiti domin taran abin kafin ya kai wani matakin da ba za a iya magancewa ba.
Akwai magunguna masu kyau da ake amfani dasu a asibitoci akan wannan cuta.
MATAKAN KARE KAI DAGA KAMUWA DA CUTAR
*Rigakafi- Ga dabbobin da suke cikin hatsari da kuma mutane
* Wanke ciwon da kyau bayan anji rauni da maganin kashe ƙwayoyin cuta
* Cigaba da wanke ciwon da saka magani akan sa har a warke
*Bada maganin da ake ƙira tetenus anti toxin idan raunin ya shiga cikin jiki sosai
*Tsabtace muhallanmu daga ƙarafa da ƙusosi daka iya raunata mu.
*Tsabtace muhallanmu daga ƙazanta da ƙwatami da datti.

Usman Muhammad Hakimi
21 July, 2023

19/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA
DARASI NA BAKWAI (07)

ZAZZAƁIN JIZON SAURO(MALARIA)
ME CECE MALARIA?
Wata cuta ce da take k**a mutane da dabbobi sanadiya cizon sauro wacce ƙwayar cuta ta protozoa mai suna plasmodium take haddasawa. Macen sauro dangin Anopheles ce ke da alhakin yaɗa wannan cuta ta hanyar cizon mai ɗauke da cutar ta ɗauko ƙwayoyin cutar bayan sunbi wasu matakai zasu kasance a bakin wannan sauro yanda da taje cizon wani zata cusa masa ƙwayoyin a cikin jinin sa. Amfi samun cutar a ƙasashe masu zafi k**ar na Afirika saboda saurro baya iya rayuwa a gurare masu tsananin sanyi.
IRE-IREN ƘWAYOYIN CUTAR
-Plasmodium falciparum
-Plasmodium vivax
-Plasmodium ovale
-Plasmodium malariea
-Plasmodium knowlesi(zoonotic)
ALAMOMIN CUTAR
Wannan cuta tana fara nuna alamomi ne kwana 8-25 bayan mutum ya kamu da cutar alamomin sun haɗa da:
- Ciwon kai(headache)
- Zazzaɓi mai tafiya ya dawo(recurrent fever)
- Rawar ɗari(shavering)
-Ciwon gaɓoɓi(joint pain)
- Amai (vomiting)
-canjawar kalar idanu yayi ruwan ɗorawa(jaundice)
-Ciwon wuya,
-ciki wani sa'in da kumburi.
IDAN CUTAR TAYI TSANANI ANA IYA GANIN WAƳANNAN ALAMUN

-Gushewar hankali,(unconscioness)
-Zafin jiki da ya wuce degree 39 yayin da aka auna da ma'aunar zafin jiki
-jijjiga sama da sau biyu a awa 24(Convulsion)
-Doguwar suma(Coma)
-Canja kalar fitsari,
-Raguwar zuwa yin fitsari(oliguria)
-Haki ko wahalar numfashi,(Dyspnea)
-Yaushin fata,
-Karancin ruwa ajiki(Dehydaration)
Da sauran su.

YADDA AKE KAMUWA DA ZAZZABIN CIZON SAURO
Ana kamuwa da zazzabin ne yayin da
-Sauro ya ciji mutun,
-Tahanyar karin jini,
-Daga uwa zuwa danta alokacin da yake ciki(congenital malaria).

WADANDA SUKAFI SAURIN KAMUWA.
-Yara kasa da shekaru biyar da Manya Yan sama da shekaru 65,
Wadanda garkuwar jikinsu tai kasa k**ar masu ciwon hiv,suga,masu ciki da masu ciwon sikla.
ILLAR ZAZZAƁIN CIZON SAURO
Akowace shekara aƙalla sama da mutane million 300 ke kamuwa da zazzaɓin cizon sauro,aduk cututtukan da ake fama da su a duniya zazzaɓin cizon sauro shine nafarko wajen kawo mutuwar yara kananu kasa da shekarawa biyar. Yara sama da 80,000 ke mutuwa a Africa saboda cizon sauro.Hakazalika Sama da 40,000 cikin wanda ke warkewa na fama da matsalolin kwakwalwa. A nigeria kaso 30 cikin 100 da ake kwantarwa a asibiti adalilin zazzabin cizon sauro ne,sannan kuma kaso 60 cikin dari da ke zuwa asibiti Shima duk dalilin wannan zazzabine.

GAGGAWAR ZUWA ASIBITI
Idan yaronka ƙarami dan ƙasada shekar biyar kaga yana zazzaɓ ko wasu daga cikin alamomin can ko kuma mace mai ciki to kayi gaggawar kaisu asibiti saboda yanda wannan cuta take saurin hallakasu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.
Usman Muhammad Hakimi
29 September, 2022.

Want your practice to be the top-listed Clinic in Azare?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Gombe Road
Azare
751101