Fim Magazine

Fim Magazine

Share

09/05/2026

Ganawar Ribaɗu da JD Vance: Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa alaƙar tsaro
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar ƙara zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afrika.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Asabar.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka, inda ya gana da manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar.

A yayin ziyarar, Ribaɗu ya isar da saƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen ɗorewar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Ribaɗu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, da sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaro na Amurka.

Babban maƙasudin wannan ganawa shi ne duba yadda za a inganta raba bayanan sirri da kuma ƙarfafa ayyukan soji na haɗin gwiwa.

Ribaɗu ya jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da s**a addabi yankin Sahel, musamman Ayyukan ta’addanci da tsageranci, safarar miyagun ƙwayoyi da mak**ai da laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.

Hukumomin Amurka sun jinjina wa Nijeriya a matsayin ta na jagora a yankin Afrika, musamman wajen jagorantar yaƙi da ta'addanci a tafkin Chadi.

A nata ɓangaren, Nijeriya ta bayyana cewa tana amfani da dabarun ƙarfin soja da kuma tattaunawa da inganta rayuwar jama'a don magance tushen matsalar rashin tsaro.

"Nijeriya tana godiya ga Amurka bisa taimakon da take bayarwa a ɓangaren horar da jami'ai, ba da bayanan sirri, da kuma tallafin jinkai," inji Ribaɗu.

A ƙarshen taron, ɓangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntuɓar juna a kai a kai ta hanyar haɗin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla sun fara aiki yadda ya k**ata.

05/05/2026

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma kiyaye ka’idojin kashe kuɗi. Shugaban ya kuma bayyana dalilan da s**a sa aka aiwatar da garambawul ga tattalin arziki cikin gaggawa.

A yayin taron, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana nasarorin da Nijeriya ta samu, inda ya ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kashi 11.2% (idan aka lissafa da dalar Amurka) a shekarar 2025.

A cewar sa, wannan ci gaba ya nuna cewa burin Nijeriya na ganin tattalin arzikinta ya kai darajar dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030 zai iya tabbata. Oyedele ya kuma lashi takobin cewa gwamnati za ta riƙa wallafa bayanan kuɗi na kowane bayan watanni uku domin tabbatar da gaskiya.

Muhimman Abubuwan Da Aka Tattauna:

• Bashin Ƙasa: Shugabar Ofishin Kula da Basuss**a (DMO), Patience Oniha, ta tabbatar wa masu zuba jarin cewa gwamnati tana amfani da bashi ta hanyar da ta dace kuma za ta tabbatar ba a jefa ƙasar cikin halin kaka-ni-ka-yi ba.

• Tsaro da Man Fetur: Tinubu ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin gyara harkar mai don daina tafka asara, sannan ana shirin rarraba ikon rundunar 'yan sanda (decentralisation) don magance matsalar tsaro da kuma toshe hanyoyin samar wa 'yan ta'adda kuɗi.

• Makomar 2027: Lokacin da aka tambaye shi game da shirinsa na bayan shekarar 2027, Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa tsarin tattalin arziki da tabbatar da cewa ba a canza manufofin da aka sa gaba ba.

Taron ya samu halartar wakilai daga manyan kamfanoni na duniya, ciki har da:

1. Citibank da Amundi (Faransa) karkashin jagorancin Valerie Baudson.
2. BlueCrest da Ninety One (Biritaniya da Afirka ta Kudu).
3. Kirkoswald Capital, Principal Finisterre, da PGIM (Amurka).

Masu zuba jarin sun yaba da matakan gyara da Shugaba Tinubu ya ɗauka, inda s**a nuna kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya.

Photos from Fim Magazine's post 05/05/2026

Tinubu ya taya Murtala Garo murnar zama Mataimakin Gwamnan Kano
​Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a yau Talata.

​Gwamnan ya naɗa Garo ne domin cike gurbin da Comrade Aminu Abdulsalam ya bari, bayan murabus ɗin da ya yi biyo bayan sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

​Murtala Garo, mai shekara 48, gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da ​Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo,​ Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

​Shugaban Ƙasa ya jinjina wa Gwamna Yusuf bisa wannan naɗin, yana mai bayyana cewa matakin zai ƙarfafa haɗin kan da ake buƙata a cikin sahu da jerin membobin jam’iyyar APC a Jihar Kano.

​Haka kuma Shugaban ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnan da mataimakin sa baya domin ciyar da jihar gaba.

Ya buƙaci sabon mataimakin gwamnan da ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamna domin samar da shugabanci na gari da zai bunƙasa jihar.

​A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Garo fatan alheri a wannan sabon nauyi da aka dora masa.

Hotuna:
Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a fannin yaɗa labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, tare da sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, Barista Sunusi Musa, SAN, da sauran jigajigan 'yan siyasa da manyan jami’an gwamnati, suna cikin shirye-shiryen rantsar da Garo a yau a Kano.

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


19 Chelsea Chibuzor Street Off NICON Junction Maitama
Abuja