Nigerian Post

Nigerian Post

Share

Nigerian Post is an independent digital news and media platform committed to delivering credible, timely, and fact-based news from Nigeria and across the globe.

03/06/2026

APC Regret Failure to Grant Pantami Gubernatorial Ticket in Gombe

Read more:
https://nigerianpost.ng/2026/06/03/apc-regret-failure-to-grant-pantami-gubernatorial-ticket-in-gombe/

Photos from Nigerian Post's post 03/06/2026

DA DUMI-DUMI: Masu Ruwa Da Tsaki Na Jam'iyyar PDP A Karamar Hukumar Gombe Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Dan Takarar Gwamnan Jihar Gombe Professor Isa Ali Pantami.

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Gombe sun gudanar da wani muhimmin taron haɗin kai domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma tsara hanyoyin tunkarar zaɓen gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027.

Taron wanda Shugaban PDP na Karamar Hukumar Gombe, Hon. Ibrahim Sa’adu Maifata, ya jagoranta, ya gudana ne a gidan Jagoran PDP na Jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo.

A yayin taron, mahalarta sun sake tabbatar da cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar gwamnan PDP, Professor Isa Ali Ibrahim Pantami, tare da alƙawarin yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Shugabannin jam’iyyar sun yi kira ga mambobi da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai da jajircewa wajen cimma manufar samun nasara a jihar. Haka kuma sun yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa wasu mambobin PDP suna komawa APC, suna masu bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya da kuma siyasar yaudara.

Taron ya kuma karyata jita-jitar ficewar wasu jiga-jigan jam’iyyar, inda wasu daga cikin waɗanda aka ce sun sauya sheƙa, ciki har da Hon. Namanu Commander, Ma’aji na PDP a Karamar Hukumar Gombe, da Hon. Babangida Usman Olchu, Sakataren Kuɗi na jam’iyyar a karamar hukumar, wanda duk sun halarci taron tare da sake tabbatar da biyayyarsu ga PDP.

An kammala taron da addu’o’in neman haɗin kai, ci gaba da kuma samun nasara ga jam’iyyar PDP da ‘yan takararta a zaɓukan da ke tafe.

03/06/2026

Atiku Ya Nuna Alhini Kan Sace Kanwar Adelabu Da ’Ya’yan Dan’uwanta Tagwaye

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sace ƙanwar tsohon minista Adebayo Adelabu da kuma ’ya’yan ɗan’uwanta tagwaye, yana mai nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, tare da yin kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin ceto su da kuma magance matsalar rashin tsaro.

03/06/2026

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, yana mai cewa ayyukan titunan tarayya da na samar da makamashi mai sabuntawa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a jihar sun kawo ci gaba mai ma’ana ga al’umma.

03/06/2026

Tasirin Siyasar Farfesa Isa Ali Pantami Yafi Na Kowa a Jihar Gombe

Daga Barista Yahaya Ibrahim

An gudanar da wani taro a Gidan Gwamnati a daren jiya, Talata 2 ga Yuni, 2026. A cewar bayanan da s**a fito daga taron, babban abin da ya mamaye tattaunawar shi ne Malam Isa Ali Pantami, inda aka mayar da hankali kan muhimman batutuwa uku:

1. Sun sani sarai cewa Malam Isa Ali Pantami bai shiga abin da suke ƙira zaɓen fidda gwani ba. Duk da haka, an yi shawarar cewa a ci gaba da tayar da hayaniya a kan lamarin tare da amfani da wasu da ake ƙira masu ruwa da tsaki daga cikin gida domin jawo ruɗani da tsawaita cece-kuce.

2. Karɓuwar da Professor Isa Ali Pantami da sabuwar jam’iyyarsa ta PDP suke samu a faɗin jihar Gombe na ƙara damun su matuƙa. Shigowarsa ya sake farfaɗo da jam’iyyar gaba ɗaya. A kusan kowane taro da majalisa, Pantami da jam’iyyarsa su ne abin tattaunawa. A cewarsu, bai kamata a bar wannan yanayi ya ci gaba ba.

Abin takaici a gare su, sun manta cewa ikon Allah ne kaɗai ke tabbatar da abin da zai kasance.

3. A yayin da Malam Isa Ali Pantami ke ci gaba da gabatar wa al’ummar Gombe manufofinsa da kuma “Tsarin Sauya Fasalin Jihar Gombe” a fannoni kamar noma, samar da ayyukan yi, tsaro, ilimi, mata, matasa, masana’antu da sauran su, har yanzu ‘yan takarar su ba su gabatar wa jama’a wata cikakkiyar manufa ko tsari ba.

An ce an yi wa dukkan ‘yan takarar da s**a halarci taron tambayoyi kan wannan batu. A yau, Pantami ya zama abin koyi a gare su ta wannan fuska.

Mu ci gaba da lura da abubuwan da suke faruwa yayin da al’amura ke ƙara bayyana.

Allah Ya rushe duk wani mugun nufi da mugun shiri da ake yi wa al’ummar jihar Gombe da kuma duk wani abu da zai hana samuwar shugabanci Nagari a jihar.

Rubutawa:
Barrista Yahaya Ibrahim
03/Yuni/2026

03/06/2026

‎'Yan Majalisar Wakilai Uku Sun Fice Daga APC Zuwa PRP da ADC

‎Mambobi uku na Majalisar Wakilai ta Tarayya sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyun Peoples Redemption Party (PRP) da African Democratic Congress (ADC).

‎Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sanarwar sauya shekarsu a zaman majalisar da aka gudanar ranar Laraba a Abuja.

‎Sanarwar ta nuna cewa sauyin jam’iyyar ya biyo bayan dalilai daban-daban da s**a shafi siyasar cikin gida da kuma muradun mazabunsu.

‎Sauya shekar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa a fadin kasar nan, yayin da wasu ‘yan siyasa ke komawa wasu jam’iyyu gabanin fara shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027.

‎Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugabannin APC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da ficewar ‘yan majalisar ba.

03/06/2026

'Ya'yan ‎Jam’iyyar APC A Jihar Gombe Sun Fara Dana-sanin Rashin Bai Wa Pantami Tikitin Takarar Gwamnan Jihar.

03/06/2026

INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJI'UN: Allah Ya Yi Wa Alhaji Auwal Inwala Rasuwa Yau Talata Sakamakon Hatsarin Mota Da Ya Rutsa Da Shi.

An Gudanar Da Jana'izar Sa Da Misalin Ƙarfe 9:00 Na Safiyar Laraba A Gidan Su Da Ke Gangaran Gangariya, Cikin Garin Funtua Jihar Katsina.

03/06/2026

‎Ranar Dimokuraɗiyya Za a Nuna Nasarorin Gwamnatin Tinubu – Gwamnatin Tarayya

‎Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa bikin Ranar Dimokuraɗiyya na bana zai kasance wata dama ta nuna manyan nasarori da ci gaban da gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta samu tun bayan hawanta mulki.

‎A cewar gwamnatin, an tsara bukukuwan ranar ne domin wayar da kan al’umma game da muhimman sauye-sauye da manufofin da gwamnatin ke aiwatarwa a fannoni daban-daban na tattalin arziki, tsaro, ababen more rayuwa da walwalar jama’a.

‎Gwamnatin ta ce a cikin shekaru biyu da s**a gabata, an samu ci gaba a ayyukan gine-ginen tituna, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma aiwatar da tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa. Ta jaddada cewa waɗannan nasarori ne da ya kamata ‘yan Najeriya su yi alfahari da su yayin bikin Ranar Dimokuraɗiyya.

‎Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da mara wa manufofinta baya domin tabbatar da dorewar ci gaba da bunƙasar ƙasa. Ta bayyana cewa dimokuraɗiyya ba kawai tsarin zaɓe ba ne, har ila yau hanya ce ta samar da ci gaba, adalci da walwalar al’umma.

‎Ranar Dimokuraɗiyya dai na daga cikin manyan ranaku na ƙasa da ake gudanarwa domin tunawa da gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da nazarin irin ci gaban da aka samu a tsarin mulkin farar hula.

03/06/2026

Ƙungiyar Tinubu/Dikko Guaranteed 2027, Ta Ƙaddamar Da Dabarun da Za Ta Bi Don Sake Zabar Tinubu Da Radda a Katsina

Shin zaku iya sake zaɓen 'ya'yan jam'iyyar APC a shekarar 2027?

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Abuja