Manara RADIO

Manara RADIO

Share

21/05/2026

LABARUN DUNIYA

HUKUMAR YAKI DA BAZUWAR CUTUKA TA NAJERIYA NCDC TA CE SAM BA EBOLA A NAJERIYA

Hukumar yaki da bazuwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce sam ba yaduwar muguwar cutar nan ta EBOLA a duk fadin Najeriya.

Yanzu haka hukumomin lafiya sun dau matakai a filayen jiragen sama na tantance masu zirga-zirga zuwa Najeriya yayin da cutar ta EBOLA ta bayyana a jamhuriyar dimokradiyyar Kongo da Uganda.

NCDC ta fito da sanarwar don yadda wasu ke yayata cewa cutar ta iso Najeriya alhali hakan ba gaskiya ba ne.

Hukumar ta NCDC ta nuna illar yayata jita-jita kan irin wannan cuta mai kisa da irin haka a shekarun baya ya haddasa rasa rayuka don yadda wasu mutane su ka rika sha da wanka da rowan gishiri a matsayin rigakafin cutar.

Hakanan NCDC ta bambanta cutar EBOLA da HANTA VIRUS wacce ke yauduwa ta hanyar shakar kurar da ke kunshe da bayan gidan ‘yan dabbobi masu buruntu, inda EBOLA kuma sai mutum ya hadu da jiki ko gumin mai cutar.



FUBARA YA JANYE DAGA TAKARAR TIKITIN TAZARCE NA GWAMNAN RIBAS A APC

Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya ayyana janye takarar zaben fidda gwani na tikitin gwamnan jihar Ribas.

Fubara ya ce ya yi hakan ne don muradun zaman lafiyar jihar ta Ribas, ya na mai cewa zaman lafiyar Ribas ya fi muradun kowa.

Duk da janyewar, Fubara ya godewa shugaba Tinubu kan goyon bayan da ya ce ya samu a tafiyarsa ta siyasa ya na mai zayyana APC a matsayin jam’iyyarsu.

Gudun kar a yi ma sa fassarar raurawa ko tsoro, Fubara ya ce ba fargaba ta sa shi saranda ba sai da ya yi tuntuba, kuma ya ba wa magoya bayansa hakuri don ya san zafin da za su ji.

An fahimci cewa APC ta ba ta tantance magoya bayan Fubara a muk**an da su ke nema na majalisa ba, amma magoya bayan ministan Abuja Nyesom Wike sun tsallake.

Ba mamaki ta yiwu ko Fubara ya tsaya ba zai samu tikitin ba don haka da muguwar rawa gwara kin tashi.



MATAIMAKIN SHUGABAN NAJERIYA KASHIN SHETTIMA YA CE WASU SUN KULLA MA SA SHARRIN NEMAN CUTAR DA SHUGABAN KASA DA WASU TUFAFI

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bayyana cewa wasu mutane daga jiharsa ta Borno sun zo sun tseguntawa shugaba Tinubu cewa ya kulla cutar da shi don karbe mulki daga wasu tufafi da ya ba shi a kamfen din 2023.

Shettima ya ce tsegumin ya zo ne watanni 3 bayan fara mulkinsu biyo bayan shan rantsuwa a ranar 29 ga Mayu 2023.

Kashim Shettima na magana ne a taron kaddamar da littafi na tarihin aiki na tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon a Abuja.

Shettima ya ce shugaba Tinubu ya sanar da shi labarin inda ya kuma cigaba da sanya kayan don bai amince da tsegumin ba.

Mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwa cewa hakan samuwar rashin amana ce da ta shigo harkar siyasar Najeriya.

Hakika an yi ta samun jita-jita kan tunanin samun Baraka tsakanin shugaba Tinubu da Shettima har ma a na tunanin zai yi wuya Tinubu ya sake daukar Shettima a mataimaki a takarar zaben neman tazarce.



SAUDIYYA TA YABAWA TRUMP DA BIN MATAKAN DIFLOMASIYYA MAIMAKON SAKE FARMAKI KAN IRAN

Saudiyya ta yabawa shugaban Amurka Donald Trump don yadda ya zabi bin tattaunawar diflomasiyya maimakon cika bazaranar da ya yi ta kai hari mai zafi Iran a ranar Talata da ta wuce.

Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya isar da wannan yabo da Saudiyya ke ganin abun maraba ne.

Bin Farhan ya ce akwai bukatar Iran ta yi amfani da damar wajen samun sulhu da zai tsayar da wannan yaki.

Ministan ya nuna kwarin guiwa matakin ka iya kawo maslaha da ma bude mashigar ruwan teku ta Hormuz don safarar man fetur salun-alun

Iran a yanzu haka na nazartar sharuddan tsagaita yakin da Amurka da kuma Isra’ila don samun matsayar da za ta kwantar da fitinar.

Hakika Iran ta nuna jajircewa a yakin da har ya kai wannan tsawon musamman ba tare da faduwar gwamnatin Tehran ba.

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Utako District
Abuja