Ya-Ibadeeh

Ya-Ibadeeh

Share

10/02/2023

*SHIN WAJIBI NE SAI MIJIN KI YA SADU DA KE A DUKKAN ƊARE, WATO JIMA'I.*

*TAMBAYA*
Assalamu alaikum Malam Don Allah sau nawa Miji ya k**ata ya sadu da matar sa, kullum ne ko kuma a'a,domin ina samun matsala da miji na Nagode.

*AMSA*
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu: Toh Malamai Sun Yi Saɓani Akan Wannan Maganar. Akwai Maganganun Malamai Har Guda (4)

(1) Abu Hanifa Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Yana Cewa Jima'i Hakkin Namiji Ne, Mace Tana da Hakkin Jima'i a Wajen Mijin ta a Rayuwar ta Sau 1 tak a Shekara, Sauran Kuma Hakkin Namiji ne Idan Ya Ga Dama Ya Sadu da ita Idan ya Ga Dama ya Bar ta a Haka. Amma Kuma Yace Namiji Yayi Abinda Ya Dace, Yayi Abinda Zai Yi Domin Zaman Auren Su Yayi Ƙyau yayi Ɗaɗi. Abinda Yake Nufi Shine Idan Mijin Ki Ya Sadu dake Sau Ɗaya a Shekara toh Ya Sauke Hakkin ki, Sauran Nashi Ne Idan Ya Ga Dama Ya Sadu dake Idan ya ga Dama Ya Bar ki. Amma Kuma Yayi Adalci Yayi Abinda ya ga Zai iya Domin Auren ku a Samun Zaman Lafiya.

(2) Imamul Shafi'i Allah Ya Kara Yarda Gare Shi Yace Bai Zama Wajibi a Tilastawa Miji Wai Ya Sadu da Matar sa ba, Yace Domin Kamar Misalin ne Mutum Ya Gina Gidan Haya ga Ɗakuna Masu Ƙyau Idan Ya ga Dama ya Sa Masu Haya a Ɗakunan Idan Ya ga Dama Kuma Ya Bar Ɗaukunan a Haka ba Tare da Ya Sa kowa ba Tunda Nashi Mallakin Sa ne. Yace toh Haka Misalin Mace da Mijin ta Yake Idan ya ga Dama Ya Sadu dake idan ya ga Dama ya bar ki. Amma Kuma Shima Yace Namiji Yayi Abinda ya ga Zai iya Domin Samun Zaman Lafiya mai Ɗaurewa a Zamantakewar Auren Su tsakanin Sa da Matar shi.

(3) Imam Malik Allah Ya Kara Yarda Gare Shi, Yana Cewa Namiji Yanada Hakkin Ya Sadu da Matar Sa a Kowanne Bayan Ƙwana (4) Sau 1 Tak, yace Domin Allah Yace Ayi Mata 4 ne, Saboda haka Hakki ne Akan Namiji Duk Bayan Ƙwana 4 yayi Jima'i da Matar Sa. Idan Matan Shi Uku ne toh Duk Bayan Ƙwana Uku ya Sadu da Mace 1. Sannan Shima Yana Cewa Abinda Ya Dace Shine Namiji Yayi Abinda Ya ga Zai Iya Domin Auren Su ya Ɗaure a Samu Zaman Lafiya.

10/02/2023

*ALLAH BAI KAYYADE LOKACIN RAMA AZUMI BA!*

'''Tambaya:'''

_ Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da zasu kai baki gagararsu yake ballatana ta ciyar, Menene mafita? _
'''Amsa:'''

_ Wa alaikum assalam ta jira har Allah ya bata lafiya sai ta rama, Allah madaukakin sarki a cikin Suratul Ba}ara aya ta: (185) ya sanya Ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a bude yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba Allah ta'ala yasan aikin dagangan.

*Allah ne mafi sani*

_ *✍🏼DR. JAMILU YUSUF ZAREWA* _
________________________
*Za'a iya bibiyar darussan mu a👇🏼*

Facebook👉🏼 https://mobile.facebook.com/Ya-Ibadeeh-105630640871237.
_____________________
*»👉🏼DAGA ZAUREN YA- IBADEEH*📖🕋

mobile.facebook.com

Want your organization to be the top-listed Government Service in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


No. 7 Yahya Madaki Way Katsina
Abuja