A R N Hausa

A R N Hausa

Share

27/11/2025

Jibwis Nigeria Sun Miƙa Saƙon Ta'aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta cewa "A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalan Shehu Ɗahiru Bauchi da al-ummar jahar Bauchi dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi.

Allah ka gafarta masa kura-kuransa, ka baiwa iyalansa dangana. Ameen."

Wallafar wacce ta sami sahalewar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Shugaban JIBWIS Nigeria.

A R N Hausa

27/11/2025

Mulkin Soja Ya Ɗauki Iko: Guinea-Bissau Ta Shiga Sabon Yanayi na Tsaka-Mai-Wuya

Guinea-Bissau na cigaba da kasancewa cikin yanayi na tsaka-mai-wuya bayan rundunar sojin ƙasar ta karɓi mulki, ta dakatar da ayyukan gwamnati kuma ta kafa sabuwar majalisar soja wadda ta karɓi ikon gudanar da al’amuran ƙasa. Wannan na zuwa ne bayan rikice-rikicen sak**akon zaɓen da ya haifar da tashin hankali a babban birnin Bissau.

Rundunar sojin ta sanar da Janar Horta N’Ta Na Man a matsayin shugaban rikon-gadin ƙasar, tare da rufe manyan ofisoshin gwamnati da shimfiɗa dokar hana fita yayin dare. Titunan Bissau sun kasance a cece-kuce, inda shaguna da bankuna s**a kasance rufe, yayin da dakarun soja ke sintiri domin hana duk wata zanga-zanga ko tashe-tashen hankula.

Duk da fara rufe iyakoki tun bayan kifar da mulkin, rahotanni sun tabbatar da cewa an sake buɗe su a yau domin sauƙaƙa zirga-zirgar hajoji da taimakon jinƙai. Sai dai har yanzu mutane na cikin fargaba, musamman ganin cewa an dakatar da fitar da sak**akon zaɓe da ake sa ran gabatarwa a yau.

Ƙasashen duniya da ƙungiyoyi k**ar AU da ECOWAS sun yi Allah-wadai da matakin sojojin, suna kiran a dawo da tsarin mulki da gaggawa. Har yanzu ba a bayyana tsawon lokacin da gwamnatin soja za ta yi a mulki ba, lamarin da ya bar makomar ƙasar cikin duhu.

Gidan jaridar A R N na cigaba da bibiyar ci gaban lamarin.

A R N Hausa

26/11/2025

Tirkashi: A Zariya dake jihar Kaduna Nigeria, wasu harsasai na bindiga sun fado daga wani buhu da ya zube daga mota a kusa da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), lamarin da ya tayar da hankalin jama’a a yankin.
Ganau sun ce direban motar ya ƙi tsayawa duk da ƙoƙarin da mutane s**a yi na nuna masa cewa kayansa sun fado. Da aka duba buhun, sai aka tarar da ƙananan al-burushi (bullets) ne a cikinsa.

Hukuma ba ta fitar da sanarwa ba tukuna, yayin da ake tambayar ina ake kai kayan? kuma na wanene su?

A R N Hausa

26/11/2025

Juyin Mulki a Guinea-Bissau
26 Nuwamba 2025

An samu sabon rikicin siyasa a ƙasar Guinea-Bissau bayan da wani sashen sojin ƙasar ya k**a Shugaba Umaro Sissoco Embaló, lamarin da ya haifar da ruɗani tare da tunzura tashin hankali a babban birnin ƙasar.

Rahotanni daga cikin ƙasar sun tabbatar da cewa an ji harbe-harbe a daren Laraba kusa da fadar shugaban ƙasa da kuma ofishin hukumar zaɓe, alamar cewa sojoji sun ɗauki matakin da ya kai ga fatattakar jami’an tsaro da ke gadin wuraren gwamnati.

A cewar majiyoyi, shugaban ƙasar da wasu manyan jami’an gwamnati — ciki har da shugaban ma’aikatan tsaro, mataimakinsa da ministan cikin gida — sun shiga hannun sojoji ba tare da tsayayya ba. Embaló ya bayyana abin da ya faru da shi a matsayin “juyin mulki”, yana mai cewa an k**a shi ne saboda tashin hankali da ya biyo bayan zaben da aka gudanar ranar 23 Nuwamba 2025.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake zaman jiran sak**akon hukuma na zaben shugaban ƙasa, wanda ya gamu da cece-kuce tun kafin a kada kuri’a. Rashin tabbas kan wa’adin Embaló da ƙalubalen siyasa daga manyan jam’iyyu sun ƙara tayar da kura tun watanni kafin zabukan.

Guinea-Bissau dai na daga cikin ƙasashen yammacin Afirka da s**a fi fama da juyin mulki, ko ƙoƙarin yin hakan, tun bayan samun ’yancin kai. Wannan sabon rikici ya sake jefa ƙasar cikin yanayin da ba a san makomarsa ba, yayin da sojoji ba su fitar da cikakkiyar sanarwa kan matsayin ikon mulki ba tukuna.

A halin yanzu, ana ci gaba da samun tsoro da firgici a cikin al’umma, yayin da ake jiran wani bayani daga rundunar soji ko hukumomin ƙasar game da ko an kafa sabuwar gwamnati ko kuma za a komawa tsarin farar hula.

A ƙarshe. Lamarin ya bar Guinea-Bissau cikin yanayin rashin tabbas, inda ake ci gaba da sa ido kan yadda za a warware rikicin, musamman bayan k**a shugaban ƙasa da manyan jami’ansa. Gidan jaridar mu zai ci gaba da bin al’amuran domin kawo muku sabbin bayanai da zarar sun fito.

Hoton dake ƙasa, hoton ƙirƙira ne.

A R N Hausa

25/11/2025

DALIBAN GGSS MAGA SUN KUƁUTA

A yau an samu gagarumar nasara a Jihar Kebbi, bayan da wasu daga cikin daliban GGSS Maga da aka sace s**a bayyana cikin tsaro.

A hoton da ya fito a safiyar yau, an ga ’yan matan suna cikin mota, cikin natsuwa da alamun farin ciki, wanda ke tabbatar da cewa sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa.

Har yanzu ba a samu wata sanarwa daga jami’an tsaro, gwamnati ko mazauna yankin ba game da yadda aka ceto su ko halin da sauran dalibai suke ciki. Haka kuma ba a fayyace hanyar kubutarsu ba tukuna.

Duk da haka, bayyanar hoton ya kawo sauƙi da kwanciyar hankali ga mutane da dama, musamman iyaye da al’umma da s**a shafe kwanaki a cikin damuwa tun bayan sace su.

Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomi a cikin sa’o’i masu zuwa.

A R N Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Abuja