Jangebe
26/08/2025
Ranar Hausa ta duniya 26/08/2023. Ga gudinmawarmu ta ranar Hausa ga Hausawa.
1 - Wane ne Bahaushe?
2 - Ina ne ƙasar Hausa?
3 - Mene ne harshe?
4 - Hausa harshe ne ko ƙabila ce?
5 - Ina ne asalin Hausawa?
1- Wane ne Bahaushe?
Bahaushe shi ne wanda ya kasance mahaifinsa da mahaifiyarsa s**a kasance Hausawa, yake magana da harshen Hausa, kuma ya yarda da al'adu da ɗabi'un Hausawa sannan yake a ƙasar Hausa.
2- Ina ne ƙasar Hausa?
Shehun Malami Farfesa Bunza ya ce, “Ƙasar Hausa ba daga wani guri s**a ta zo ba, nahiyar Gobir nan ce tushen ƙasar Hausa. A yau ma iya cewa Arewacin Najeriya da kuma wani ɓangare na Jamhuriyyar Nijar nan ne ƙasar Hausa”
Daura
Kano
Gobir
Katsina
Zazzau
Rano
Biram
Amma da akwai wasu Malamai masu ra’ayi saɓanin wannan.
3- Mene ne harshe?
Harshe wata baiwa ce mafi tsada da Allah maɗaukakin sarki ya yi wa bayinsa, ta silar hakanne Ɗan'adam yake iya yin magana har a fahimta, har ma yake iya banbance abubuwa daban-daban.
4- Hausa yare ne ko Ƙabila?
Hausa yare ne na Hausawa, su kuma Hausawa Ƙabila ce da suke magana da harshen Hausa waɗanda suke zaune a ƙasar Hausa.
5 - Ina ne asalin Hausawa?
Asalin Hausawa shi ne yankin tafkin chadi, dalilin da yasa wasu masana s**a yi hujjah da hakan shi ne, dukkannin harsunan afrika sun samo asali ne daga yankin tafkin chadi.
Daga ɗalibin nazarin kimiyyar harshen Hausa.
Malam Bilal Bako.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Website
Address
Anka Road
Abuja
872101