Tahoua tech
YADDA AKE BUDE PAYPAL ACCOUNT
Shi PayPal wani app neh wanda ake amfani dashi wajen tura kudi ko karba ma’ana internet banking.
Abinda kake bukata wajen bude PayPal account shine kamar haka:
Da farko zaka je google app store kayi install din PayPal App kuma ya kasu kashi biyu akwae original akwae kuma lite toh duk wanda ka dauko babu matsala domin duk daya neh kuma amfaninsu daya.
Bayan ka dauko wannan app din sae kayi open dinsa wato ka bude shi zaka ga wajen da aka rubuta “sign in” da kuma “sign up” toh sae ka shiga wajen “sign up” anan neh zakaKa tabbatar ka cike komae yadda ya dace.
A wajen zasu bukaci kasa wadannan abubuwan:
+Email
+Your country misali Nigeria
+Phone number misali +2348068…
+Password misali Kee11ma2
+Verifying password irin na sama
+Sign Up
Kana danna sign up zasu tura ma verifying message ta email dinka da kayi register dashi, sae kaje ka bude sakon ka shiga link din da s**a turo ma shikenan zasuyi maka congratulation na kammala bude account dinka.
Zaka iya amfani dashi wajen tura kudinka da ka tara a internet ta yadda zaka samu saukin transfer dinsu zuwa bank account dinka.
ASLM
Yadda Ake Tura Application Na Android Zuwa Katin Ajiya (SD Card)*
Za a iya cewa abu ne mafi dacewa a yi install na apps na wayar Android a cikin katin ajiya (SD Card) maimakon a ajiye apps din a ma'ajiyar wayar.
Shin ko kana tunanin tura (moving) apps din da ka yi install a ma'ajiyar wayar ka zuwa katin ajiyar ka, amma baka san yadda ake yin hakan ba?
A yau, na kawo takaitaccen bayani ne kan yadda mai amfani da wayar Android zai tura 'Applications' din wayar sa zuwa katin ajiya (SD card).
Wayoyin Android suna da hanya mai sauki da ake bi wajen tura Apps daga ma'ajiyar wayar zuwar zuwa katin ajiyar da ke cikin wayar. Kawai bi wadannan matakan domin yin hakan;- » Ka je ' *Settings* ' » sai ka zabi ' *Application settings* ' » sai ka je kan ' *Manage Applications'* » sai ka zabi App din da kake son turawa zuwa *SD card* , ka danna shi » har sai ka ga wani dan window ya fito ( *pop up* ) » anan za ka ga ' *Move to SD card* ', sai ka latsa shi. Shikenan!
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Type
Site Web
Adresse
Tahoua