Pharmactivity

Pharmactivity

Share

04/05/2026

Na ga ya dace in sabunta ku.

Ko bayan an yi dashen bargo (stem cell transplant) ko yin CRISPR, yaro na iya gado cutar amosanin jini idan duka iyaye suna da cutar ko kuma suna dauke da kwayar cutar (trait). Misali SS + SS (dukan su suna da cutar amosanin jini) ko AS + AS (kowannen su yana dauke da jinsi daya mai lafiya daya kuma mara lafiya).

Saboda haka, ina ba masu niyar shirin aure shawara da su yi gwajin kafin aure (premarital screening) tare da bin shawarwarin da aka basu.

Abdullahi Musa, RN

25/01/2026

Wayar da Kai Kan Amfani da Allurar Gentamicin‼️

A yau, mutane da dama suna amfani da allurar gentamicin ba tare da shawarar likita ba, musamman idan sun ji abin da suke kira “ciwon sanyi.”

Wannan abu ne mai matuƙar hatsari.

Gentamicin magani ne mai karfi, kuma idan an yi amfani da shi ba daidai ba, yana iya:
❌ Lalata qoda
❌ Lalata ji (kunne)
❌ Rage tasirin magani
❌ Kara tsananta cuta

Na taba ganin mutum yazo shagon magani ya ce:
“Don Allah a yi min allurar ciwon sanyi.”

Ba tare da gwaji ko bincike ba.
Wannan abu ne mai matuqar hatsari.

📌 Shawara;

1. Kada ka yi allura ba tare da rubutaccen magani ba
2. Kada ka yi wa kanka gwaji
3. Ka je asibiti ko wurin ƙwararren likita
4. Masu sayar da magani su ji tsoron Allah.

Gentamicin ba abun wasa ba ne.

Mu kiyaye lafiyarmu ta hanyar amfani da magani yadda ya dace.

Want your business to be the top-listed Health & Beauty Business in Lucknow?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Lucknow
226026