Jerry Jackson
14/06/2024
Wannan abun dubawa ne
Kamar yadda na fada a last sentence na wancan rubutun cewa, idan ka rasa ZK airdrop, to kar ka kuskura ka rasa lesson da ya kamata ka koya daga rasawar da kai. Saboda dik wanda ka ga ya fahimci Crypto sosai daga kurakuransa ya koya. Irin wannan kurakuran wani lokacin suna maka amfanin da ko nasara kai ba lallai wannan nasarar tai maka irin wannan amfanin ba. Za ka iya jin maganata kamar almara, amma haka take.
Misali, Renec kadan na tara lokacin da akai mining dinsa. Wannan ya sa na mai da hankali na d'an tara Core, amma da akai listing ina ganin kudin na qi siyarwa. Hakan ya sa shi ma a wancan specific time din ya zamar min kamar failure; na kasa tara Renec da yawa, shi kuma Core na kasa siyarwa. Daga nan sai Renec ya sa na koyi dabarun tara coins na mining da yawa, shi kuma Core ya sa na koyi price prediction sannan na koyi siyarwa lokacin da ya dace da sanin mai ya kamata nai da kudin.
Wannan abubuwan da na koya yanzu sun min amfani mai yawan da ba zai lissafu ba. Will say them some day. Daya daga ciki wanda yake a zahiri kowa zai sani shi ne, Crypto wisdom dina ya qaru sosai, wanda muke tare da su a nan har suna tinanin wani qwaro ne ni alhalin har yanzu yunwar koyo nake. Wannan tinanin ya sa mutane suna iya karbar abu in na zo da shi, sakamakon haka yanzu ina iya tara coins na mining da yawa saboda referral commission. So kai ma ka koya daga Zksync.
Kamata yai ka raba retroactive activities dinka gida 2 ka dau 1. Ko dai ka zama full time retroactive farmer, ko kuma ka zama casual farmer. Full time su ne wanda suke zagewa su yi dik wani activity da ake buqata, dik wani abu da za ka ji jita-jitar ana buqata suna yin su, komai da komai. Wannan yana ba su edge akan gamagarin mutane, shi ya sa dik sanda akai listing yawanci sai sun samu. X influencers ke nan. Amma fa wannan salon ana cin kudi kamar hauka, dan average ana kashe $1k.
Ko kuma ka zama casual farmer, kawai za ka je wani network ka dan yi activity dinka (wanda yawanci ma ba lallai hunting din ne ya kai ka ba), amma kana dan bibiyar project din, idan ka ga an zo yin wani abu haka mai dan muhimmanci kai ma sai ka yi kamar wanda kwanaki akai a Scroll wanda za kai deploying smart contract sai kai minting early user NFT dinsu. Da sauran activity dai qananu marasa cin kudi. Yawanci indai network din na da niyyar actual decentralisation to zai biya ka in lokaci ya yi.
A wannan salon ko an yi disappointing dinku babu abun da za ka ji. Idan kuma har da gaske sun so decentralisation to yana da wuya ba ka zama eligible ba. Wancan salon na farko kuwa aiki ne jaa, sannan da risk. Za ka iya gama zagewar ka qona kudin still su dakko wani abu daban su sa cikin criteria kamar ZK da s**a kawo ERC activity, ko su saka wani tsari da dole tsiraru ne za su samu kamar ZK libratus NFT wanda da gayya s**a kawo shi s**a ba wa tsiraru.
Sai ka za'bi wanda za ka iya. In ka za'ba kuma ka tabbata ka kiyayi zira jika retroactive da ya tara milyoyin farmers. Dik girmansa indai akai yawa to in za ka yi ka yi shi qasa-qasa sosai sosai sosai.
https://t.me/Gocryptoweb3/1
�
BARKA DA ZUWA �
DUK ABINDA BAKA GANE BA KA YAMBAYA CIKIN TELOGRAM GROUP
1 NEWS
2 UPDATE
3 AIRDOP...............
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Jos