Pi Pro Arewa

Pi Pro Arewa

Share

21/10/2025

MARKET STRUCTURE

Farashi na tafiya ne a yanayi guda uku:

a. Uptrend market
b. Downtrend market
c. Side ways ko kuma Consolidation.

~ UPTREND MARKET.

Uptrend na nufin lokacin da farashi ke tashi sama a hankali, yana ƙirƙiran sabbin ƙololuwa a sama da ƙasa.

Idan kasuwa tana hawa sama (Uptrend), farashi yana yin Higher Highs da Higher Lows.

Galibi farashi yana yin sama ne a lokacin da farashi ke ƙaruwa.

farashin kuma na ƙaruwa ne yayin da masu saye suke sayen adadin da yafi wanda masu sayarwa ke buƙatar su sayar.

Farashi ya dinga hawa sama daga ƙaramin mataki zuwa babban mataki shi ake kira da "Uptrend"

~ UPTREND STRUCTURE

A cikin uptrend, farashi yana gina:

Higher Highs (HH) wato ko wane sabon ƙololuwa yafi na baya tsayi. Sai Kuma;

Higher Lows (HL) wato kowane sabon sauƙar farashi yafi na baya sama.

Misali:
Low →Higher High → Higher Low → Higher High → Higher Low ….

🧠 A irin wannan salon tafiyar farashi na UPTREND buyers suna samun ƙwarin gwiwa akan farashi zai tashi.

Yayin dasu kuma sellers suke jiran tashin farashi domin su fice daga kasuwar.

Wannan yanayin yana ƙara yawan masu sayen coin domin farashi ya tashi sama.

A nan buyers suna shiga kasuwa a lokacin da farashi yake matakin Support Level Sannan su fice a lokacin da yakai matakin Resistance Level.

Note: Always Trade the retracement, not the top🙏

~ DOWNTREND MARKET.

Downtrend yana nufin lokacin da farashin ke sauƙa ƙasa a hankali, yana ƙirƙiran sabbin ƙololuwar ƙasa da matakan sama masu rauni.

Wannan na nuni da cewa masu sayarwa (sellers) sunfi ƙarfin masu siye (buyers) a cikin kasuwa.

Downtrend na nufin lokacin da farashin ke gangarawa ƙasa. Galibi farashi na gangarawa ne idan yana raguwa.

raguwar farashi na faruwa ne a lokacin da masu sayarwa suke sayar da adadin da yafi adadin da masu saye su ke buƙatar su saya.

A irin wannan yanayin sai farashi ya dinga gangarowa daga sama zuwa ƙasa. Wanda hakan a ke kira da "Downtrend"

~ DOWNTREND STRUCTURE.

A cikin downtrend, farashi yan

13/10/2025

TRADING STYLE + TIMEFRAME

Sai DanBaiwa ya shiga Trade da niyyar ya gama ya fita a yau, amma sai Trade din ya dauke shi kwanaki ko sati bai je Profit Target dinsa ya sallame shi ba

Mostly hakan tana faruwa ne saboda din mutum bai yi daidai da Trading Style dinsa ba

Indai ba a samun daidaito tsakanin 'Trading Style' da kuma 'Time Frame' to zakaga hatta Technical Analysis din mutum ba zai rinka fita daidai ba

Saboda k**ar mutum ne yake son zuwa Kano daga Gombe, nan da awa 3 yake son sauka a Kano

Maimakon ya hau motar da zata nufi Kano daga Gombe kai tsaye, a'a sai yaje ya hau motar da sai ta biya ta Bauchi ta sauke wasu sanan daga Bauchi ta nufi Kano

Kaga babu yanda za'ayi yaje Katsina a awa uku.

Domin magance wannan matsalar dole sai kayi abu guda biyu:

1- Kasan wanne ne Trading Style dinka: Scalping za kayi, Day Trading ko Intra-Day Trading, ko kuma Swing Trading Trading za kayi.

2- Kuma kasan wanne Timeframe ne yafi dacewa da Trading Style din naka.

💎 Trading Styles :

1. Scalping shine salon trade din da ake shiga dan ayi agama cikin yan sakanni, ko yan mintuna zuwa yan awanni. Karamar riba ake targeting a Scalping.

2. Day Trading/Intra Day Trading salon trade din da ake shiga dan ayi agama a iya rana daya, ba'a kwana acikin Trade.

3. Swing Trading salon trade din da ake shiga dan ayi a fita na tsawon kwanaki ko ko sati, ko sama da sati.

4. Holding ko Kace Position Trading, yana daukar mutum weeks ko watanni a Trade guda daya.

A sanda kazo za kayi Trading, kai ka san irin Trading kake son yi base on yanda ka tsara Strategy dinka.

Amma dai shawarar da zan baka DanBaiwa indai kana son ka raini karamin jari kuma kwarewarka ba tayi zurfi to Scalping ba naka bane. Ka rinka yin Day Trading da Swing, sune zasu baka damar yin Analysis me kyau a nutse, kuma zaka fi samun riba.

💎 Time Frame (TF) :

~ A kowane time frame daka zaba, duk Candlestick daya yana nuna bayanan abinda ya faru na tsawon lokacin Timeframe din.

Misali Idan ka sa

Want your business to be the top-listed Media Company in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Zaria