Sir Wisdom II

Sir Wisdom II

Share

18/05/2026

A cikin Kruger National Park a ƙasar South Africa

wani gogaggen mai kula da namun daji mai suna Sipho Nkosi ya sami bugawar zuciya (heart attack) yayin da yake sintiri shi kaɗai.

An gano motarsa babu kowa a ciki, lamarin da ya sa aka fara neman sa.

Abin da kyamarorin sa ido da ke cikin dajin s**a nuna ya taɓa zuciyar duk wanda ya kalli bidiyon.

Wani tsohon toron giwa wanda masu kula da dajin ke kira “Mnumzane” (kalma ce ta harshen Zulu wadda ke nufin “Yallabai”), shi ne ya gano gawar Sipho.

Na tsawon kwanaki uku da dare uku, giwar ta ƙi barin wajen, yayi tsaye tare da gadin gawar, tana shafa Sipho a hankali da hancinta (trunk), tana korar kuraye da sauran dabbobin da s**a kusanci gawar, har ma tana rufe wasu sassan gawar da rassan itatuwa da ganyaye.

Har a daren rana ta uku giwar tana wurin, tana nuna alamar baƙin ciki, tana karkada jikinta a hankali kusa da mai kula dasu da ya rasu.

Sai bayan tawagar ceto ta iso da motoci ne Mnumzane ta ja baya, tana kallo cikin nutsuwa yayin da ake ɗaukar gawar Sipho...😭

Daga baya, jami’an gandun dajin sun tabbatar da cewa Sipho ne ya ceci wannan giwa tun tana ƙaramar jaririya, bayan mafarauta sun kashe mahaifiyarta shekaru da s**a wuce, Giwar ba ta manta da wannan alheri ba... 🐘

Ɗaya daga cikin abokan aikinsa da ya kalli bidiyon ya ce;
“Ba ta zo domin yin bankwana ba, tazo ne domin tabbatar da cewa babu wanda zai wulaƙanta gawar wanda ya ceci rayuwar ta tun tana ƙarama

Har yanzu Mnumzane yana yawan dawowa wannan wuri, wanda yasa masu kula da gandun dajin suke ajiye ruwa da ‘ya’yan itatuwa a wurin domin girmama su duka biyun.

Sir Wisdom II

07/05/2026

Anyi wani Sarki a wata masarauta wanda yake da ido ɗaya da ƙafa ɗaya amma kuma ya kasance mai basira da tausayin talakawa..👌

Kowa a masarautar yana rayuwa ta jin daɗi saboda yadda sarkin ke kyautata musu.

Wata rana, sarkin yana wucewa a cikin fadar tashi sai yaga zanen hotunan Iyayen shi da kakanin shi a parlour, sai yayi tunanin shima ya k**ata yasamu ayi zanen shi domin shima ƴaƴan shi da jikokin shi suna tuna shi da wannan zanen.

Sai Sarkin yasa aka gayyato dukkanin masu zane na garin hadda maƙwabta domin suzo su zana hoton shi

Sarki ya bada shelar cewa duk wanda ya zana hoton shi mai kyau, zai samu wasu kyaututtuka na musamman daga fada

Duk masu zanen sai s**a fara tunanin ae sarki idanun shi ɗaya ne kuma ƙafar shi ɗaya ce, yaya za'a yi ace an zana shi Hoto yayi kyau kuma? 🤔. Hakan bazai yiyu ba, kuma idan akayi zanen baiyi kyau ba kowa yana tsoron hukunci daga fadawan sarki.

A sabo da haka ɗaya bayan ɗaya duk sai s**a fara bada uzuri suna ɓacewa domin kada suyi zanen.

Ana cikin hakan, sai wani mai zane ya ɗaga hannun shi yace: "Ranka shi daɗe zan jaraba zana hoton ka yayi kyau sosai in Allah Ya yadda". Sarki sai yayi farin ciki da hakan.

Mutumin ya k**a zane har ya gama, sannan ya lulluɓe zanen sai ya sanar da cewa ya kammala.

Dukkanin masu zanen Garin dana maƙwabta kowa yazo yana jira yaga yaya akayi aka zana Sarki mai ido ɗaya da ƙafa ɗaya kuma yayi kyau? 🤔

Yanzu idan sarkin baiyi kyau ba yaya kenan zaiyi? 🤔.

Lokacin da mutuminnan ya buɗe zanen, ae kuwa fada sai ta cika da mamaki da murna.

Abinda yayi shine:

Ya zana Sarkin a zaune akan doki (ƙafar shi ɗaya za'a gani), yana riƙe da 🏹 kwari da baka yayi saitin abinda zai harba yana leƙawa da ido ɗaya a kulle.

Sarkin kuwa sai ya kamu da farin ciki yadda yaga mutuminnan yayi zanen da kyau sosai ya kuma qayatar, sarkin sai yabashi kyauta masu yawan gaske.

Yan'uwa masu hankali da tunani, abun lura anan shine:

Wajibi ne garemu mu kasance masu nufin wasu da alhkhayri da kuma ɓoye aibun wasun mu.

Yak**ata muna ɓoye inda s**a gaza muna maida hankali akan inda s**ayi daidai.

Maimakon kuma ɓoye aibun nasu kawai, sai mu samu mu ɓollowa aibun ta gefe mai kyau domin gyara shi.

Allah Ya sa mu wanye lafiya.
Alƙalamin Sir Wisdom II ....🖊️🖊️

04/05/2026

The revenge...😂🐂🐂

Want your school to be the top-listed School/college in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Zaria