DNN Hausa

DNN Hausa

Share

Ku na iya tuntuɓarmu kai tsaye: 08061341152

23/06/2026

Zan cigaba da yin addu'a kan a samu haɗin kai tsakanin yan Najeriya har zuwa lokacin da zan mutu - Uzor Kalu, tsohon Gwamnan jihar Abia.

23/06/2026

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci dukkan sanatoci su tabbatar da halartar zaman majalisar na ranar Laraba domin kada kuri’a kan kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a fadin Najeriya.

Akpabio ya bayyana kudirin a matsayin daya daga cikin muhimman sauye-sauyen da za su iya canja tsarin tsaro a kasar, yana mai cewa lokaci ya yi da za a bai wa jihohi damar taka rawa kai tsaye wajen kula da harkokin tsaro.

Yayin zaman gaggawa na Majalisar Dattawa da aka gudanar ranar Talata, shugaban majalisar ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro da s**a hada da ta’addanci, garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Kano