Dandume Fb Connect
A Saurari fira Daga bakin Daya Daga chikin shuwagabannin wan nan qungiya Kuma akan program da ake shirye shirye yi.
10/09/2025
Assalamualaikum
Ƙungiyar Ɗandume facebook connect tana sanar da al'ummar garin Dandume cewar gobe zata bada magunguna kyauta ga yara marasa lafiya, ƴan shekara 5 zuwa ƙasa .
Da kuma awo (BP) ga mata masu juna biyu . Program ɗin zai gudana a cikin makarantar modal primary school ta cikin garin Dandume da misalin 9:30am na safe a Gobe idan Allah ya kaimu (11/09/2025).
07/09/2025
Alhamdulillah, yau ma kamar sauran ranaku, Ƙungiyar Dandume Facebook Connect ta dira garin Nasarawa Dandume domin gudanar da shirin ta na bangaren lafiya. ✨
💊 TAIMAKO GA MATA DA YARA A NASARAWA DANDUME 💊
A wannan shiri na musamman:
🌸 Sama da 158 mata masu ciki da kananan yara sun amfana da:
Gwaje-gwaje kyauta 🧪
Magunguna kyauta 💊
Dubawa da aune-aune 🩺
Wannan aiki ya nuna cewa haɗin kai da jinƙai su ne ginshiƙin rayuwa.
Muna godiya ga shugabanni, masu bada gudummawa, da dukkan ƴan uwa da s**a mara baya.
Allah ya saka da mafi alheri, ya kuma sanya wannan aiki cikin mizani. 🤲❤️
DandumeDandume Fb Connect Facebook Connect – , Zumunci, Taimako
06/09/2025
Wasu daga cikin hotunan ayyukan da Ƙungiyar Dandume Facebook Connect ta gudanar a wuraren da aka gayyace mu – Mahuta A, B, C, Dantankari da kuma Tunburkai ward.
Ayyukan sun haɗa da:
✅ Awan maleriya ga mata masu juna biyu da magani
✅ Awan maleriya ga ƙananan yara
✅ Wankin kazuwa ga Almajirai tare da Basu magun guna
✅ Awan hawan jini
✅ Awan cutar hanta
✅ Bayar da magunguna kyauta
Da sauransu.
Wan nan aiki hadin guiwa ne a tsakanin chairman na karamar hukuman Dandume dakuma Qungiyar Dandume Facebook connect ✨
’umma
Dr. Dikko Umaru Radda Dandume Fb Connect
Click here to claim your Sponsored Listing.
Culinary Team
Attire
Telephone
Website
Address
Funtua