Aminu Muhammad

Aminu Muhammad

Share

25/12/2024
02/12/2024

Akwai wani Talaka da ya buga wani littafi lokacin yana da shekaru 40, sai ya ƙudiri aniyar bikin ƙaddamar da littafin a ranar murnan zagowar haihuwar shi.

Ba shida kuɗin da zai ɗauki ɗawainiyyar hakan, don haka sai ya yanke shawarar neman taimako daga wani attajiri dake unguwar su.

Ya kawo wa attijirin ziyara gida, bayan sun gaisa yake sanar dashi maƙasudin ziyarar tashi.

Attajirin sai yace dashi ya ɗauki paper da biro. Bayan ya ɗauka sai yace dashi: "zan baka wani gwaji, idan ka tsallake zan baka kuɗin, idan ma baka tsallake ba zan baka Kuɗin". Sai yace Dashi ya rubuta mishi sunayen mutane 10 waɗanda zasu iya bashi 10k yayin ƙaddamar da wannan littafin....👌

Abun mamaki Mutuminnan ko sunan mutane 3 bai iya rubuta wa ba...🥺

Sai Attajirin yace dashi: "sha ruwa". Bayan ya sha sai yace dashi: "wai don kanada ilimi da basira, hakan bai wadatar ba. Dole ka fahimci karfin ƙulla alaƙa mai kyau da mutane...🙏

Wani mai iya magana yana cewa: "network ɗin ka is directly proportional to net worth ɗin ka"...🙅 Alaƙa dukiya ce_!

Muyi nazari da kyau, waɗanda suke ƙaunar ka a wannan rayuwa abun dubawa ne...💯🩵

Waye Kasani waye ya sanka yana da matuƙar tasiri a wannan rayuwar...✅

Akwai matakai da dama da kuma wassu damammaki da ba zaka taɓa samu ba ko kaiwa idan baka fahimci ƙarfin dake tattare da ƙulla alaƙa mai kyau da mutane ba..🙅

Wannan wanda kuke zaune dashi a aji, ko kuma wanda kuke aiki dasu a waje guda, ko kuma wasu wanda kuke group ɗaya kake ƙasƙantarwa, ta yiyu sune silar kai ka ga inda ƙaddarar ka take saboda bakasan waye su ba

Kada ka wulaƙanta mutum, zaka buƙace shi watarana.

Wasu lokuta masu naɗa sarki basa k**a da sarki, amma sukan taimaka masa ya zama sarki

ka ƙulla ƙofar Alaƙa da mutane nagari koda kun samu saɓani da mutum, domin ta yiwu ka buƙace shi domin amfani gobe..💯

Allah Ya mana jagora ☺️ ✍️

pen 🖊️

30/11/2024

Alhamdulillah Allahumma sali,Alah MUHAMMADUN WASALIM
Assalamu alaikum warahamatullahi wabara katuhu yan uwana inayiwa kowa barka da safiya da fatan kowa ya waye gari cikin koshin Lafiya da fatan Allah Ya bamu yini Lafiya

29/11/2024

Assalamu alaikum warahamatullahi wabara katuhu yan uwana inayiwa kowa barka da safiyar juma ah Allah Ya sadamu da alhairan dake cikin wannan kyakyawar safiya

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Nakasarin Barebari Area
Sokoto