Comrd Ibrahim
Ibrahim Mahmud Abdullahi📌
Motivational speaker | CEO of MIA footwears | Legit News Spreader | Student | Youth Motivator | Dream Chaser | Writer | Available for Business 🤝
25/02/2026
HANYA ƊAYA TA RAGE MANA DON SAMUN ’YANCI A AREWA:
Ba yaƙi bane.
Ba zubar da jini bane.
Ba kuma tada tarzoma bane.
’Yanci na gaskiya yana farawa ne daga wayewa da haɗin kai.
Lokaci yayi da matasa zasu:
– Nemi ilimi da ƙwarewa.
– Tsayawa akan gaskiya.
– Yin amfani da ƙuri’arsu cikin hikima.
– Neman hakkinsu ta hanyar doka.
– Ƙin sayar da muradinsu saboda kuɗi ko tsoro.
Mu duba misalin India, sun yi gwagwarmaya ta juriya da haɗin kai har s**a samu ’yanci.
Duba South Africa, sun tashi tsaye cikin tsari da jagoranci har aka kawo ƙarshen wariyar launin fata.
Darasi anan shine?
Ƙarfi ba lallai ya zama bindiga ba.
Ƙarfi na iya zama tsari, ilimi, ƙuduri, da haɗin kai.
Matashi, ka kunna wutar neman canji a zuciyarka, amma ka barta ta zama haske, ba gobara ba.
Idan muka gyara kanmu, muka haɗa kai, muka daina tsoron faɗar gaskiya cikin doka – wallahiza a saurare mu.
’Yanci ba'a samun shi kyauta.
Ana gina shine da wayewa, haƙuri, da tsayin daka.
Lokaci yayi da zamu farka – amma cikin hankali. Allah ya daga arewa🇳🇬🔥
Comrade Ibrahim ✍️
25/02/2026
WANNAN YAR AREWA CE… 🇳🇬
An sace ta.
An raba ta da iyayenta.
An jefa ta cikin tsoro da rashin tabbas.
Ka tsaya ka kalli wannan hoton da kyau…
Ba labari bane kawai.
Ba post bane kawai.
Rayuwa ce ta wata baiwa kamar ’yar uwarka.
Yau ita ce.
Gobe kuma wa zai zama?
Arewa, yaushe zamu farka?
Yaushe zamu daina cewa “ba ruwana”?
Yaushe zamu gane cewa tsaro alhakin kowa ne?
Bawai mu tayar da tarzoma ba,
amma mu tashi tsaye da hankali, da haɗin kai, da addu’a, da faɗakarwa.
Domin shiru ba mafita bane.
Tsoro ba kariya bane.
Hadin kai shine ƙarfi.
Ka ƙaddara ’yar uwarka ce a wannan halin… ya za ka ji?
Allah Ya kare mana ’ya’yanmu da iyalanmu. Amma gaskiya akwai aiki a gabanmu 🤲
Comrade Ibrahim ✍️
Allah ga arewa 😭😭🤲
22/02/2026
SIRRIN SAMUN BIYAN BUKATA DA GAGGAWA A WURIN ALLAH:
Mutane da yawa suna cewa:
“Nayi addu’a amma ban ga amsa ba…”
Ka sani, Allah baYa yin sakaci.
Sai dai akwai sirri da mutane da yawa s**a manta:
1. TSARKAKE ZUCIYA:
Ka kawar da hassada, ƙiyayya, da zalunci. Zuciya mai tsabta tana da saurin karɓuwa.
2. GUJE WA HARAM:
Abinci, kuɗi, da rayuwa idan sun tsarkaka, addu’a tana ƙarfi.
3. YAWAITA ISTIGHFARI:
Istigfari yana buɗe ƙofofin alheri. Yana kusantar da bawa da Ubangijinsa.
4. YIN SALLAH DA DARE (Tahajjud):
A lokacin da kowa yayi bacci, kai ka tashi kayi kuka ga Allah, wannan lokaci na Musamman ne, na karɓar addu’a.
5 YAQINI (Tabbacin zuciya).
Kayi addu’a kana da cikakken imani cewa Allah Zai amsa, ko da ba a hanyar daka zata ba.
Ka sani:
Wani lokaci Allah yana jinkirta maka abu ne domin Ya baka mafi alheri.
Wani lokaci kuma yana sauya maka shi zuwa wani abu mafi amfani.
Idan ka gyara dangantakarka da Allah, bukatarka zata gyaru da kanta.
Allah Ya biya mana bukatunmu na alheri, Ya bamu abin da ya fi mana alhairi. Ameen 🤲
Comrade Ibrahim ✍️
Zina tana lalata nasara. Ya Allah Ka tsare mu daga zina. 🤲🏻”
Allah Yasa wannan ya zama Ramadan ɗinka na ƙarshe daza kayi cikin damuwa na matsalar kuɗi. Ameen🤲.
21/02/2026
Musulmai kadai ne zasu fahimta 💔
20/02/2026
ALAMOMIN DAKE NUNA CEWA KANA BURGETA NE KAWAI – AMMA BA SONKA TAKE YI BA:
Wani lokaci namiji yana rikicewa tsakanin sha’awa da soyayya.
Ba duk wadda take nuna kulawa bace take da nufin soyayya ko aure.
Ka lura da waɗannan alamomi:
1. TANA SON LOKACIN NISHAƊI KAWAI:
Idan ana cikin jindaɗi tana nan.
Amma idan ka shiga damuwa ko wahala, sai ta fara yin nisa.
2. BATA SAKA KA CIKIN SHIRIN TA NA GABA:
Bata magana dakai game da makoma.
Bata haɗa ka da burinta.
Kai dai kana cikin “yanzu” ne kawai.
3. TANA SON YADDA KAKE SA TAJI – BA KAI BA:
Tana son kulawarka, kuɗinka, ko yadda kake yabonta.
Amma bata damu da yadda kake ji ba.
4. BATA DAUKAR KA DA MUHIMMANCI IDAN BA KA NEMA BA:
Idan ka daina kira ko saƙo, komai ya tsaya.
Wanda yake son ka, bazai bari kullum kai ka riqa naiman sa ba.
5. TANA ƁOYE KA:
Ba ta son a san kuna tare.
Ba ta son ka kusanci MUHIMMAN mutanen rayuwarta.
6. TANA SON YABON KA – AMMA BATA YABA MAKA
Kana ƙoƙari, amma bata ganin ƙimar tafiyarka.
Sai dai ta karɓi abinda kake bayarwa.
Dan uwa, ka sani:
A burge mutum abune na ɗan lokaci.
Amma soyayya ta gaskiya tana da: –
– gaskiya
– sadaukarwa
– da shiri na gaba
Idan kana jin kullum kana cikin ruɗani,
kullum kana tambayar kanka matsayinka,
to ka tsaya ka sake tunani.
Wadda take son ka da gaske,
ba zata sa ka rikice game da matsayinka a zuciyarta ba.
Comrade Ibrahim ✍️
19/02/2026
A MATSAYINKA NA "NAMIJI", KA RIKA ƊAUKE KANKA DAGA WADANNAN ABUBUWAN:
Namiji na gaskiya ba wai ƙarfi kaɗai yake dashi ba,
yana da tsari, mutunci, da iyaka.
Ka ɗauke kanka daga:
1. WURIN DA BA'A GIRMAMA KA:
Inda ake raina ka, ana wulaƙanta ka, ana ɗaukar ka ba komai,
bar wurin nan. Mutuncinka ya fi zama a inda ake tauye ka.
2. TATTAUNAWAR BANZA DA BATA LOKACI:
Yawan surutu ba alamar hankali ba ne.
Namiji mai hangen nesa yana rage hayaniya, yana ƙara aiki.
3. SOYAYYAR DA TAKE RUSA MAKA NASTUWA:
Inda kullum kake cikin shakku, tsoro, ko ruɗani,
ba soyayya ba ce, damuwa ce.
4. ABOKAI MARASA BURI:
Idan abokanka ba sa magana sai kan shagala,
ba sa maganar gaba, ba sa gina komai,
zaka zama kamar su a hankali.
5. HANYOYIN SAMUN KUƊI NA RASHIN GASKIYA:
Kuɗin da ba halal ba yana sa ka rasa kwanciyar hankali da daraja.
Talauci na ɗan lokaci ya fi kuɗin da zai ɓata maka suna har abada.
6. YAWAN BAYYANA SIRRINKA GA KOWA:
Namiji ba ya zubar da komai a fili.
Akwai abubuwan da ya kamata su zauna a zuciya.
---
Namiji na gaskiya:
– yana da iyaka
– yana da nutsuwa
– yana da tsari
– yana zaɓar abinda ya dace dashi
Ka sani…
Ba duk inda aka kira ka ya kamata kaje ba.
Ba duk zancen da ake yi ya kamata ka shiga ba.
Ba duk soyayyar da tazo ya kamata ka karɓa ba.
Wani lokacin girman namiji yana cikin abinda yaƙi, ba abinda ya karɓa ba.
Ka kare mutuncinka.
Ka kare hankalinka.
Ka kare makomarka.
Domin duniya tana girmama namiji mai tsari…
ba wanda yake bin duk abin da ya gani ba.
Comrade Ibrahim ✍️
Abincin da kaci ka rage, wani yana da bukata. Ka tuna da makubta. Allah ya karbi ibadun mu🤲
Ramadan Mubarak 🕋
18/02/2026
WATAKILA WANNAN SHINE RAMADAN DINKA NA KARSHE…: DAN UWA BANI MINTI DAYA DAN ALLAH
Ka tsaya kayi tunani.
Shekarar data wuce, wasu suna tare da mu.
Yanzu suna cikin ƙasa.
Sun yi shirin ganin wannan Ramadan din, amma basu kai ba.
Kai kuma ka sake ganin wannan wata mai albarka.
Tambaya ita ce:
shin zaka yi amfani da shi, ko za kayi sake ya wuce kamar sauran?
Ramadan wata ne na gafara.
Wata ne da Allah ke buɗe ƙofofin rahama.
Wata ne da ake sassauta azaba, ake ƙara lada.
Idan kana da wani abu a ɓoye,
wannan shine lokacin barinsa.
Idan kana jinkirta tuba,
wannan shine lokacin komawa.
Kada kace kana da lokaci.
Mutuwa ba ta tambayar shekarunka,
ba ta tambayar shirinka.
Kayi istigfari.
Ka gyara sallah.
Ka gyara mu’amalarka da mutane.
Ka bar abinda kake yi na laifi.
Domin wataƙila wannan shine Ramadan ɗin da Allah Ya baka na karshe
domin ka gyara littafinka kafin a rufe shi.
Ka fara yau.
Ba sai gobe ba. 🌙🤍
Ramadan Mubarak!🕋
Comrade Ibrahim ✍️
17/02/2026
ABUBUWA UKU DA KOWANI "NAMIJI" KE TSORO A DUNIYA:
Ba duk namiji bane ke faɗin abinda ke razanasa. Yawanci yana ɓoye tsoronsa a bayan murmushi, shiru, ko tsananin aiki. Amma a zahiri, akwai abubuwa uku da kusan kowane namiji ke tsoro a rayuwa:
1. TSORON GAZAWA:
Namiji na tsoron ya kasa zama abin alfahari ga iyayensa, matarsa, ’ya’yansa ko al’ummarsa.
Yana tsoron ya kasa cika alkawura.
Yana tsoron a ce: “Bai iya ba.”
Wannan ne yasa wasu mazan suke wahala cikin shiru, suna gwagwarmaya ba tare da kuka ba.
2. TSORON TALAUCI DA RASHIN DARAJA:
Ba wai talauci kaɗai ba… amma rasa mutunci.
Namiji na tsoron ranar dazai rasa ikon tallafa wa iyalinsa.
Yana tsoron zama abin tausayi a idanun mutane.
Saboda haka yake neman kudi, yake ƙoƙari dare da rana – ba don jindaɗi kaɗai ba, amma don kare martabarsa.
3. TSORON RASA WANDA YAKE SO:
Koda bai nuna ba, zuciyar namiji tana da taushi.
Yana tsoron rasa mace mai muhimmanci a rayuwarsa.
Yana tsoron cin amana.
Yana tsoron kada a watsar da shi bayan ya saka ZUCIYARSA.
Amma ga gaskiya:
Jarumi ba yana nufin wanda baya tsoro bane.
Jarumi shine wanda yake jin tsoro… amma duk da haka ya cigaba da tafiya.
Kai namiji ne???
Kar ka bari tsoro ya hana ka zama abinda Allah Ya halicce ka domin ka zama.
Kayi aiki. Kayi haƙuri. Kayi addu’a.
Ranar daka shawo kan tsoronka, ka fara zama namiji na gaske.
Comrade Ibrahim ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.