Abubakar Umar
A yau da misalin ƙarfe 1 na rana (1:00pm) majalisar wakilai ( House of representatives) zata zauna da CBN akan batun kara wa'adin daina karɓan tsofaffin kuɗaɗe.
Allah yasa muji alheri Allahumma Ameen.
16/01/2023
Abubakar shine ɗa ɗaya tilo a wajen iyayensa. Sun bashi duk wani kulawa. Babu irin gatan da basu nuna masa ba. Sun nuna masa matuƙar soyayya a matsayin shi na ɗa guda ɗaya tak da Allah ya basu. Sun sakashi a makaranta. Yayi karatu matakin primary da secondary ya kammala. Sai dai bai ci gaba da karatun nasa ba sandiyyan rauni na jarabawan shiga babban makaranta da yakai tsahon shekaru 3 yana samu.
Ana cikin wannan tafiyan ne sai Allah ya jarabci mahaifin Abubakar da rashin lafiya wanda akalla yakai shekara yana jinya. A shekaran farko da Abubakar ya samu nasarar cin jarrabawan shiga jami'a, bayan ya fara zuwa makaranta da yan watanni sai Allah yayiwa mahaifin sa rasuwa. Sai ya rage mahaifiyarsa kadai take raye.
Bayan wani lokaci da rasuwan mahaifin sa, ya koma makaranta. Yanzu duk nauyin karatunsa da komai nasa mahaifitlyarsa take dawainiya.
Abubakar dai bayan ya zama cikakken dan makaranta yana gab da kammala mataki na 200 a jami'a sai ya haɗu da wata yarinya mai suna Aisha s**a fara soyayya. Ita wannan yarinyan mahifin ta hamshaƙin mai kudine matuka. Duk da cewa shi Abubakar ya fito daga gidan talakawa duk bai hana Aisha soyayya dashi ba.
Lokaci nata tafiya soyayyan Abubakar da Aisha yana ƙara ƙarfi. Yayin da s**a kai mataki na 400, sai makaranta s**a bukaci wayansu kuɗaɗe waƴanda kimanin su yana da yawa har yakai ga mahaifiyar Abubakar ta gagara biya masa domin kuwa yafi ƙarfinta. Shikenan Abubakar sai ya zabi da ya hakura da karatun duk da kasancewan sa yakai mataki na 400 a jami'a.
Domin kuwa ba yanda basu buga ba shi da mahaifiyansa amma sun gagara samun wayannan kuɗaɗen. Shikenan dai da hakan Abubakar ya yanke shawaran ya haƙura ya dawo gida ya nemi Abunda zai rufa ma kansa asiri shi da mahaifiyarsa.
Tsawon mako 2 Aisha bata ganin Abubakar a makaranta, hankalinta ya tashi matuka, sai taje gidansu nemansa. Tana zuwa kuwa ta sameshi. "Abubakar me ya faru kwana biyu ban ganka a makaranta ba" ta tambayeshi. Abubakar kuwa ya gaya mata duk dalilin sa ya daina zuwa makaranta da kuma niyyan sa na hakura da makarantan gaba ɗaya.
Aisha ta tausayawa Abubakar matuka. Da zuwanta gida ta gayawa mahifinta komai, saboda soyayyan da mahaifinta yake mata sai ya mata alƙawarin da zaiyi duk abunda takeso game da Al'amarin karatun Abubakar da kuma mahaifiyansa.
Sai Aisha ta bukaci da mahaifinta da ya ɗauki nauyin karatun Abubakar da kuma duk wani dawainiyansa dana mahaifiyansa. Nan take mahaifin Aisha ya amince. Shikenan ya biya masa ƙudin makaranta s**aci gaba da karatunsu. Mahifiyan Abubakar taji ɗadi matuƙa ta godewa Aisha da mahaifinta. Tsananin farin cikin da tayi dangane da wannan kyautatawa da Aisha da mahaifinta s**ayi musu ita da ɗanta yasa ta gayawa Abubakar ko bayan babu ranta bata yarda Abubakar ya rabu da Aisha ba Kuma ta umarceshi da a duk lokacin da Aisha zata nemi wani taimako a wajensa koda kuwa da ransa zai taimaka to lallai ya taimaka mata domin rama alakairin data yi musu a rayuwa.
Lokaci na tafiya. Soyayyan Abubakar da Aisha a kullum sai kara karfi takeyi. A kwana a tashi har sun kammala karatunsu, suna shirye shiryen tafiya bautan kasa.
Bayan kwashe watanni suna bautan ƙasa, ya rage musu baifi wata ɗaya su kammala bautan kasan su ba wani al'amari yana nan yana faruwa a gida. Mahaifiyan Abubakar ta kamu da tsananin rashin lafiya.
Bayan Abubakar da Aisha sun dawo daga bautan kasa, kuma sun kammala karatunsu Abubakar sai ya dawo ya taras da mahaifiyarsa babu lafiya. An kaita asibiti lokitoci sun tabbatar da cewa hantar (lung) ta ne guda daya ya samu matsala.
Kuma likitocin sun tabbar da cewa dole sai an chanja mata hanta kuma ba kowane hanta zai mata ba sai na Abubakar domin kuwa shine jininta. Amma dai kafin ayi aikin sai ya ɗauki tsawon wata biyu. Zataci gaba da jinya har na tsawon wannan lokacin.
Wani abun al'ajabi, kafin wa'adin da aka yanke na yiwa mahaifiyar Abubakar aiki sai Aisha itama ta kamu da rashin lafiya mai tsanani wanda likitoci da s**a auna s**a gano cewa ƙodan ta (kidney) guda daya ta samu matsala. idan kuwa.har anason ta rayu dole sai an chanja mata ƙoda (kidney). Kuma shi wannan ƙoda da za'a chanja mata ana bukatan na sabon jini wanda shekaransu yake dai dai ko kuma suke da tazaran shekara 1 koda kuwa ƙodan na miji ne ko mace. Babu wanda kodan sa yazo dai da a sakawa Aisha sai na abubakar.
A yanzu a bangaren mahifiyan sa tana jira lokaci yayi a mata chanjin hanta (lung) kuma itama Aisha ƙoda (kidney) na Abubakar kadai take bukata ta rayu. Kuma bazai yiwu ya bayar da kodan sa da kuma hantansa ba idan kuma hakane sai ya rasa ransa. Dole sai dai ya bayar da daya.
Shine ran mahaifiyansa zai ceto ko kuma ran masoyiyarsa Aisha zai ceto?
Tinatarwa: mahaifiyarsa ta taba ce masa duk a lokacin da Aisha take bukatan taimakon sa koda da ransa ne ya bayar ya ceceta domin domin rama alkairin da ta musu a rayuwa.
©️ Abubakar Umar
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Lafia
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |