CTV Hausa
19/05/2026
Shugaban K/H Kumbotso Hon Ali Musa Hardworker ya nada Hon Sadiq Saha mukamin mai bashi shawara akan harkokin kungiyoyin kare hakkin al'ummar da sauran kungiyoyi.
16/05/2026
Ambasada Habib Wada Salisu ya sayi fom din takarar majalisar tarayya mai wakiltar Gumel a Jigawa a Jam'iyyar NDC ta Kwankwaso da Obi.
12/05/2026
Dan Majalisar Jiha na Bebeji a majalisar dokokin Kano Hon Alin Tiga Dan Aljannah ya sake gwangwaje 'yan gwagwarmayarsa da sabbin babura goma a Bebeji - Alin Tiga Youths Development Forum.
12/05/2026
25/04/2026
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN...
Allah ya yiwa Dan Gwagwarmaya Kwamared Nura Darakta Tukuntawa rasuwa.
25/04/2026
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN...
Allah ya yiwa Magaji Gefen Kwari Gidan Maza rasuwa.
Za'ayi Jana'izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a yau Asabar a Unguwar Gidan Maza Tukuntawa
21/04/2026
Gwamnan Kano ya miƙa sunan Honourable Murtala Sule Garo domin tantance shi a zauren majalisar dokokin jihar Kano, a matsayin mataimakin gwamna.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin sa na Facebook.
17/04/2026
Wannan shine babban Asibiti da Bandakin da al'ummar Mazabar Garin Gawo da sauran Garuruwa 10 a karamar hukumur Gezawa a Kano suke amfani dashi a halin yanzu.
Kuma a wannan halin lalacewar da Asibitin ke ciki da kuma lalataccen Bandakin nasu, amma a haka ake amfani dasu saboda babu yadda za suyi a wadannan garuruwa.
Muna kira ga wadanda lamarin ya shafa musamman Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf daya kawo musu dauki.
Kimanin Garuruwa 11 ne suke fama da matsaloli daban - daban a garuruwan da s**a hada da: Talawa, Nahuce, Andawa, Yafata, Walawa, Baburko, Kadewa B, Jilmawa, Kadewa A, Hayin Jama'a da kuma Marayar Mai Kwai dake karamar hukumur Gezawa.
Sai dai babban abunda yafi ci musu Tuwo akwarya shine rashin kyawun hanyarsu da take hada wadannan garuruwa, wadda a yanzu suke kiran hanyar da suna Sambisa saboda yadda ake hallaka mutane akan hanyar.
15/04/2026
Masu Gonaki a Garin Zarah dakewaye a yankin karamar hukumur Dawakin Kudu a Kano sun bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf, daya sanya baki game da yunkurin kwace musu Gonoki da ma'aikatar kasa da Safiyo take shirin yi musu.
A cewar su abun ya shafi sama da mutane dari shida wadanda suke da Gonaki da Fulotai, kuma tunda ma'aikatan Land suke zuwa Gonakin nasu babu wanda ya taba tuntubarsu domin shaida musu abunda suke shirin yi.
Kiraye - Kirayen wasu daga cikin masu Gonaki da iyalan wadanda s**a mallaki Gonaki a Garin Zarah dakewaye kenan, wadanda suke mika koken su zuwa ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf game da shirin kwace musu Gonaki da ma'aikatar kasa ta Kano take shirin yi acewarsu.
Tunda fari, masu korafin sunce, sunyi mamakin yadda aka fara wannan aiki ba tare da sanin su ba a matsayinsu na mamallaka wadannan Gonaki da Fulotai, sai dai kawai umarni aka aiko musu da cewa kada wanda ya siya kuma kada wanda ya siyar, kamar yadda shugaban kwamitin mamallaka Gonakin Alhaji Sabo ya shaida mana.
Wasu daga cikin masu Gonakin da suke korafi sun shaida mana cewa, ko kadan basuji dadin wannan al'amari ba domin anyi irin haka a kusa dasu sunga yadda masu Gonaki da Fulotai s**a shiga damuwa saboda yadda aka kasa yi musu adalci.
Game da korafin mutanan, munyi kokarin jin tabakin Dagacin Garin Zarah Alhaji Abubakar Zarah sai dai yace ba zai ce mana komai ba akan batun.
Koda muka tuntubi Murtala Shehu Jami'in hulda da Jama'a a ma'aikatar kasa da Safiyo ta Kano ta wayar tarho, ya bukaci mutanan Garin Zarah dasu kwantarda hankalin su, domin a halin yanzu sunyi wata ganawa da Jagororin su domin samun daidaito a lamarin.
Wadanda lamarin ya shafa dai sun roki Gwamna Abba Kabir Yusuf daya shiga tsakani domin tabbatarda adalci akansu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
700224