IBM Health Talk

IBM Health Talk

Share

🩺 Health Education for Everyone
Nutrition • Disease Prevention • Healthy Living
📚 Sharing reliable, research-based health information
👉 Because your health is your greatest investment.

20/06/2026

Masu cin Apple kullum👇

Kariya Daga Manyan Cutuka.
Cin apple akai-akai na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da wasu manyan cutuka saboda yana ɗauke da fiber, antioxidants da sauran sinadarai masu amfani ga jiki. Bincike ya nuna cewa cin 'ya'yan itatuwa kamar apple na iya taimakawa wajen:
Kula da lafiyar zuciya
Rage haɗarin hawan jini
Taimakawa wajen sarrafa nauyin jiki
Rage haɗarin ciwon sukari nau'i na 2
Inganta lafiyar hanji da narkewar abinci
📌 Ku tuna: Apple ba magani ba ne irin na asibiti, amma yana iya zama wani ɓangare na ingantaccen tsarin abinci da ke taimakawa kariya daga cututtuka.
✍️ RD. Ibrahim A. Bichi, RDN

13/06/2026

"Kwakwalwa tana aiki yayin da kake bacci! 😳"

12/06/2026

"Kunnenka yana canzawa yayin da kake girma! 👂😳"

11/06/2026

Dalilin da yasa kake haki bayan gudu zai baka mamaki!

10/06/2026

Fruits market 😂

10/06/2026

"Na daina cin tuwo amma ban rame ba! 😳"

02/06/2026

Shin ka san cewa Shan LEMU guda ɗaya a rana na iya taimakawa wajen kare jikinka daga cututtuka da dama?

°Lemu na ɗauke da sinadarin Vitamin C mai yawa wanda ke taimakawa jiki ya yaƙi mura da sauran cututtuka.

°Yana taimakawa lafiyar fata Vitamin C yana taimakawa wajen samar da collagen wanda ke sa fata ta kasance mai laushi da ƙyalli.

°Lemu na da fiber wanda ke taimakawa wajen hana maƙarƙashiya da inganta aikin hanji.

° Sinadarai da fiber da ke cikin lemu na iya taimakawa wajen rage haɗarin cututtukan zuciya.

° Lemu na da ƙarancin kuzari (calories) amma yana sa mutum ya ji ya ƙoshi na ɗan lokaci.

° lemu na taimakawa wajen hana bushewar jiki.
Ka tuna: Magani ba ya cikin kwalbar lemo mai zaki (soft drink), yana cikin lemo na gaske da Allah Ya halitta.

✍️ RD. Ibrahim A. Bichi, RDN

27/05/2026

Eid Al-Kabir

25/05/2026

Wannan hadin shine dai-dai shawara kyauta📌

16/05/2026

Dadi a baki… amma jiki na iya shan wahala idan ya yi yawa.

✍🏾RD. Ibrahim A. Bichi, RDN

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Tudun Maliki, Zoo Road
Kano
700224