Samu da Rashi DG Allah ne

Samu da Rashi DG Allah ne

Share

01/05/2026

'Amurka za ta ɗauki lokaci kafin sake ƙera manyan makaman da ta yi asara a yaƙin Iran'

Karin bayani
BBC HAUSA

07/04/2026

Da Dumi Dumi

Trump ya fasa kai hare-hare da ya yi niyya kan Iran

Shugaban Amurka Donald J. Trump ya ce ya amince da dakatar da kai hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu, domin ba da damar kammala tattaunawar zaman lafiya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social, Trump ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da Firaministan Shehbaz Sharif da kuma babban hafsan sojin Asim Munir na ƙasar Pakistan.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Trump ya ce Iran ta gabatar da shawarwari guda goma, waɗanda ya ce za su iya zama tubali wajen kulla yarjejeniya, ciki har da buɗe mashigin Hormuz cikin gaggawa.

Sai dai ya jaddada cewa wannan tsagaita wuta na ɗan lokaci zai ba ɓangarorin damar kammala tattaunawa da cimma matsaya ta ƙarshe.
Ubangiji Allah ka zaunar damu lafiya.

Photos from Samu da Rashi DG Allah ne's post 07/04/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Yadda dubban al’ummar ƙasar 1ran s**a fito inda s**a cika wuraren da Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare a daren yau, sakamakon kusantowar ƙarewar wa’adin tattaunawar da ya sanya.

Rahotanni sun nuna cewa maza da mata da dama sun taru a waɗannan wurare domin kare ƙasarsu, inda wasu ke bayyana cewa sun fi son fuskantar shahada tare da mutunci fiye da rayuwa cikin ƙasƙanci.

Mene ra'ayinku?

06/04/2026

Jama'a asaka jamhoriyar Musulunci ackin Addu'a.

05/04/2026

🇪🇺🇮🇷 Sun juwa shugaban kasar America baya.

An ruwaito cewa ƙasashen Turai suna tattaunawa da Iran kan hanyar shiga mashigin Hormuz

Rahotannin sun nuna cewa ƙasashen Turai da dama suna shiga tattaunawa kai tsaye da Iran don tabbatar da cewa jiragen ruwansu sun ratsa ta mashigin Hormuz lafiya, yayin da ake ci gaba da samun cikas ga samar da makamashi a duniya.

An ce ƙasashe kamar Faransa da Italiya suna cikin tattaunawa da nufin dawo da cikakken kusuwacin mai da iskar gas ba tare da ƙara ta'azzara rikicin ba.
Allah yasa mudace

05/04/2026

Alhamdulillah Alhamdulillah

30/03/2026

LABARI MAI ƊUMI: Gawuna ya yi murabus daga shugabancin Bankin Lamuni na Gidaje na Tarayya
Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Bankin Lamuni na Gidaje na Tarayya (FMBN), Nasiru Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Mista Gawuna ya kammala shirinsa na sauya sheƙa tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, kuma ana sa ran zai koma jam’iyyar ADC a ranar Talata.

28/03/2026

Ubangiji Allah ka kara mana Nasara

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano