KMGA
Together for Truth 🗣️ and Awareness 💪
Empowering💪 voices🗣, inspiring 🙌 changes✊
ZINA TA YI ARHA, AURE YA YI TSADA.
Yau idan kana da N500,000 a aljihunka, da wuya wannan kuɗin su ishe ka ka yi aure saboda tsadar al'ada, kayan lefe, da shirye-shiryen biki da muka kakaba wa kanmu. Amma abin takaici da tashin hankali; da N50,000, N10,000, ko ma kalaman daɗin baki kawai, zaka iya kai yarinyar mutane ɗakin hotel domin ka biya buƙatar haram. Subhanallah...
Mun wayi gari a cikin wata al'umma da muka tsananta abin da Allah Ya sauƙaƙa (Aure), sannan muka sauƙaƙa abin da Allah Ya haramta (Zina).
Wannan gaskiya ce mai ɗaci wacce dole ne mu fuskance ta ta fuska uku:
1. Zuwa Ga Iyaye:
Don Allah a duba tsarin da ake ɗora wa matasa masu neman aure. Yawan buƙatun maƙudan kuɗaɗe da gasar biki sune suke tsoratar da samari masu kishi da natsuwa. Wannan matsin lissafin shine yake sa yara mata su daɗe a gida har shaiɗan ya samu damar jefa su a halaka. Sauƙaƙa aure shine babbar garkuwar al'umma daga rushewa.
2. Zuwa Ga 'Yan Mata:
'Yar uwa, ki san darajar kanki, Jikinki da mutuncinki sun fi ƙarfin N50k, shawarma, ko sayen sabuwar wayar hannu. Kada ki yarda wani ɓataccen namiji ya sayi lahirarki da ɗan abin duniya da zai ƙare a rana ɗaya. Duk namijin da ba zai iya zuwa wajen iyayenki ya neme ki da aure ba, baya ƙaunarki, yaudararki kawai zai yi ya watsar.
3. Zuwa Ga Samari:
Dan'uwa, ka ji tsoron Allah, Kuɗin da kake ɓatarwa wajen kai matan mutane hotel, idan ka tara su wallahi zasu iya yi maka aure na halas ka samu natsuwa a rayuwarka. Ka tuna cewa duk abin da ka yi wa 'yar wani, akwai wanda shima yake jiran 'yarka ko ƙanwarka a gaba.
Dole ne mu farka daga wannan baccin, mu koma kan tsarin addininmu kafin musiba ta gama mamaye mu gaba ɗaya.
Allah Ya sauƙaƙa mana al'amuran aure, Ya raba mu da kowace irin hanyar alfasha.
https://www.facebook.com/profile.php?id=61581150117790
���� Facebook link
https://chat.whatsapp.com/H9Xo9QyTmFVHu5vfWluXL6?mode=wwt
����WhatsApp group chat
Follow us on
�KMGA
together for Truth and awareness ��
Aduba wnn karamar hukuma tamu saboda gyararraki d yawa d s**a addabi alumma
KMGA together for Truth and awareness ✊💪
Aduba mu
Together for Truth and awareness ✊💪
Ta Yaya Muke Zaton Samun Sauqin Fadan Daba' Da Siyar Da Miyagun Qwayoyi Da Qwacen Waya Da Babura Alhalin Masu Yi Kusan Duk Yaran Ýan Siyasa Ne Da Masu Mulkin Sarauta'
Gwamna Ko Sanata Ko Ďan Majalisa Ko Sarki Ko Chiairman A Cikin Tawagar Sa' Zaka Samu Fiye Da Ýan Daba Sama Da Guda Hamsin Yana Ďaukar Nauyin Su'
Duk Wata An Saka Masu Alawus Sannan Ga Kayan Abinchi Da Ake Tura Musu Gida' Idan S**a Aekata Mummunan Laefi Shi Wannan Ubangidan Nasu Shine Zai Tsaya Masu A Fitar Dasu A Qasa Da Kwana Uku Kowanne Irin Laifi S**ayi' Har Ikrari Suke Ko An K**a Su Ma Sai An Sake Su" Dan Haka Sun Chi Banza' Amman Mutumin Kirki A Anguwa Ko Tuhuma Ce Ake Masa Akan Gaskiya Ta Kae Shi Gaban Hukuma Sai Yasha Wuya Har Ya Doshi Kusan Sati Ana Azabtar Da Shi'
Qarshe Dae Idan An Salwantar Da Rayuwar Ďan Daba A Wajan Kare Darajar Mae Gidan Sa Da Wuya Ka Gansu Gurin Jana'izar Sa' Ko Zuwa Ta'aziyya' Sai Dai Su Aikawa Iyalan Sa Buhun Shinkafa Da Dubu Ďari' Daga Nan Kuma Bazasu Qara Bibiyar Takan Iyalan Ba' Wasu Za'a Qara Nemowa'
Da Yawa Yanzu Ďan Daba Yafi Malami Da Mutan Kirki Daraja A Gurin Wasu Masu Mulkin'
Kenan Shugabannin Mu Sune Suke Daurewa Ýan Daba Gindi Suke Aekata Miyagun Laefuka A Cikin Society Ďin Mu'
Shin Bazamu Hankalta Bane Mu Tashi Tsaye Mu Magance Wannan Matsala Da Hannun Mu Tunda Masu Fada Aji Sun Zuba Idanu Ba Kuma Ranar Da Zasu So Adaina Hakan Saboda Biyan Buqatar Kan Su'
Ya Jama'a Dole Fa Sai Mun Cire Tsoro Sannan Zamu Samar Wa Kan Mu Tsaro' Muyi Qoqarin Magance Matsalar Mu Da Kan Mu' Allah Ka Bamu Ikon Gyarawa Ya Muzillu.
Matashi, ka tsaya ka saurara:
– harshenka yana iya gina ka ko rushe ka
– post ɗinka na iya ilimantarwa ko lalatawa
– abokanka na iya kai ka aljanna ko wuta
Idan ka raina tarbiyya yau,
rayuwa za ta raina ka gobe
Together for Truth and awareness ✊💪
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano