TUKA

TUKA

Share

23/09/2025

Alamomi 5 da Suke Nuna Abokin Soyayyarka Ya Gaji da Kai
1. Sadarwa ta Zama Aiki Mai Wahala:
Wannan ita ce alama ta farko da za ka lura da ita. Sadarwar da a da take da daɗi kuma take gudana a sauƙaƙe, yanzu ta zama kamar aiki ne na dole.

-Ya daina fara kiranka: Kai ne kullum mai fara kira ko tura saƙo.
-Amsoshinsa sun zama gajeru: Amsoshinsa sun koma "Ok," "Toh," "Babu komai." Ya daina ba da labari ko kuma nuna sha'awar jin naka.
-Ya daina sauraronka: Ko da kuna waya, za ka ji hankalinsa baya tare da kai. Yana yawan katse ka ko kuma yana son ya yi sauri ya yanke wayar.

2. Yawan Kawo Uzuri da Guje-guje:
-Mutumin da ya gaji da kai, zai fara guje maka a hankali.
-Kullum yana "Busy": A duk lokacin da ka nemi ku haɗu ko ku yi wata magana, sai ya ce yana da aiki, ko ya gaji, ko kuma ba shi da lafiya. Uzurinsa zai yawaita fiye da da.
-Yana soke alƙawari: Zai iya yin alƙawari da kai, amma a minti na ƙarshe sai ya soke shi ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba.
-Ba ya son ku fita tare: Ya daina son ku fita tare zuwa wuraren da kuka saba zuwa.

3. Yana Fara Neman Laifinka a kan Ƙananan Abubuwa:
Wannan dabara ce da mutum yake amfani da ita idan yana son ya kawo ƙarshen alaƙa. Zai fara neman laifinka a kan abubuwan da a da ba su dame shi ba.

-Yawan S**a: Zai fara sukar yadda kake magana, ko yadda kake shiga, ko kuma halayenka.
-Yana Tada Rigima ba Dalili: Zai iya tada babbar rigima a kan wani abu ƙarami wanda bai taka kara ya karya ba.
-Manufarsa: Yana son ya sa ka ji ba ka daidai, don ya samu dalilin da zai ce ku rabu, ko kuma don ya sa kai da kanka ka gaji ka ce kun rabu.

4. Ya Daina Nuna Damuwa da Kulawa:
Dukkan wata kulawa da ya saba nuna maka a da, za ta gushe.
-Ba ya tambayarka game da rayuwarka: Zai daina tambayarka "Ya ka yini?" ko kuma yadda al'amuranka suke tafiya. Ko ka ce masa: “Ya kake?” zai ce: “lafiya.” Amma kai ba zai tambayi lafiyarka ba.
-Ba ya damuwa da damuwarka: Idan ka faɗa masa wata matsala, ba zai nuna damuwa sosai ba, kuma ba zai ba ka shawara ba.
-Ya

23/09/2025
23/09/2025

Ka saurara

23/09/2025

Maulud

23/09/2025

Ku saurara kuji

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Road
Kano
700252