Hausa Global Update

Hausa Global Update

Share

11/08/2025

Ogan Boye

Photos from Hausa Global Update's post 10/08/2025

EFCC ta k**a wasu mutane a otal din Green Legacy na tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, bisa zargin damfara a intanet.

An kwace manyan motoci sama da 20 da sauran kayayyaki masu daraja.

Bayan kwanaki biyu, jami’an EFCC na Ibadan sun kuma k**a wani mutum a wani otal din Itori, inda s**a samu kananan bindigu guda biyu.

Wadannan samame na nuna kokarin hukuma na yaki da masu yaudarar mutane ta hanyar intanet.

10/08/2025

Matar da ta kashe mazajenta 11 don mallakar dukiyar su.

Kulthum Akbari, 'yar shekara 56, ta amsa laifin kashe tsofaffin mazajenta 11 sama da shekaru 22 don mallakar dukiyarsu.

An yanke mata hukuncin kisa bayan ta yi amfani da magungunan s**ari da kwayoyi wajen kashe su. Masu gabatar da kara sun ce tana canja dukiyar mazajen zuwa asusun 'yarta k**ar yadda jaridar Gulf News ta ruwaito.

06/08/2025

Kwamishinan sufurin jihar, Ibrahim Namadi ya ajiye muƙaminsa kan zargin alaƙarsa da mutumin da ake tuhuma da safarar miyagun ƙwayoyi a Kano.

Photos from Hausa Global Update's post 06/08/2025

Wannan sune fuskokin waɗan da ishirwa ta kashe a yayin ƙoƙarin su na tsallakawa Ƙasashen Algeria da Libya don neman na kansu.

Dole masu fita ƙasahen waje don neman abinci musamman yankin Sahara, su rinƙa kula da kyau, domin wannan ya nuna mana cewa ba Mota ce ta lalace ba, Dauko su akayi aka zubar dasu a cikin Sahara aka gudu aka barsu, har Ishirwa tayi sanadiyyar Mutuwar su.

05/08/2025

Ishirwa da yunwa sunyi suna zama sanadiyyar mutane akan hanyar su ta Algeriya ko Libiya,

Yadda ake samun asarar rayukan al'ummar Najeriya da Nijar wajen shiga ƙasar Libya da Algeriya, inda mutane ke mutuwa sak**akon lalacewar mota.

05/08/2025

Ambaliyar Ruwa Himalaya ta ƙasar Indiya ta yi sanadiyar mutuwar mutane 4, 50 sun ɓata.

A ƙauyen Himalayan na Uttarakhand, arewacin Indiya, ambaliyar ruwa da ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi ta yi sanadiyar mutuwar mutane huɗu, yayin da wasu 50 s**a ɓace. Ana ci gaba da bincike don ceto waɗanda s**a maƙale.

05/08/2025

Rano Rice, Shinkafar Kamfanin AA Rano Rice Mill.
Siyen nagari Mai da kuɗi Gida.

05/08/2025

Wata ƴar Jihar Yobe dake Arewacin Najeriya Nafisa Abdullah Aminu, da ke da shekara 17 a duniya, ta fafata da ɗalibai 20,000 daga ƙasasher 69, inda ta zo ta ɗaya a duniya a gasar iya Turancin Ingilishi, wato English language skills 2025 TeenEagle Global Finals da aka gudanar a birnin London.

04/08/2025

Jirgin ruwa ya kife da Ƴan Gudun Hijira a Gabar Tekun Yamen.

Akalla 'yan gudun hijira da bakin haure 68 daga Afirka sun rasa rayukansu yayin da wasu 74 ke bace bayan wani jirgin ruwa ya kife a gabar tekun Yemen, in ji Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM).

Shugaban IOM a Yemen, Abdusattor Esoev, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Lahadi cewa jirgin ya ƙunshi mutum 154 ‘yan asalin ƙasar Habasha (Ethiopia), kuma ya kife a gundumar Abyan da ke Yemen.

Esoev ya ce mutum 12 ne s**a tsira daga hadarin, kuma an ga gawarwakin mutane 54 a yankin Khanfar, yayin da wasu 14 aka tsinta a wani wuri daban, aka kai su dakin ajiye gawa a asibiti.
A baya, hukumomin lafiya na Yemen sun ce mutum 54 ne s**a mutu.

A cikin shekaru 10 da s**a wuce, mutane 2,082 aka ruwaito sun ɓace a hanyar, ciki har da 693 da aka tabbatar sun nutse a ruwa.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Hotoro, Nasarawa Local Government, Kano, Nigeria.
Kano
700281