Arewa Now
From breaking headlines to in-depth reports, our goal is to keep you informed, connected, and empowered.
12/04/2026
Bismillahir Rahmanir Rahim
Barkanmu da zuwa ArewaNow dandalin da ke kawo muku labarai cikin sauri, gaskiya da amana.
📌 Tsarin Aikinmu:
Muna aiki da ƙa’idojin aikin jarida na gaskiya da sahihanci. Labaranmu na fitowa ne bayan tantancewa, domin tabbatar da inganci da amincewar al’umma. Burinmu shi ne mu zama muryar gaskiya ga Arewa da Najeriya baki ɗaya.
📩 Turo Mana Labari ko Shawara:
Domin turo mana labari, rahoto, ko wata shawara, za ku iya tuntubar mu ta WhatsApp:
09113148323
Dukkanin ra’ayoyin siyasa kyauta ne ba mu karɓar kuɗi domin wallafa ra’ayi ko wani matsayi na siyasa. Muna tsayawa ne kan adalci, gaskiya da daidaito.
🤝 Muna maraba da goyon bayanku, shawarwarinku da addu’o’inku domin cigaban wannan tafiya.
ArewaNow
11/04/2026
Mai girma Jagora, Nafiu Gombe zaka k**a ba mukarraban gwamna ba, domin basu s**a saka ka zanga zanga an Abuja ba, kuma in har mutum zai taba martabar gwamna Abba wallahi zamu taba tashi - Hon. Ishaq idris Alaramma
06/04/2026
A cikin sanarwar da ya fitar, Hamisu ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan fitar mai gidansa, Hon. Abdulhadi Ishaq Gunduwa, daga jam’iyar APC.
Ya kuma yi godiya ga dukkan wadanda s**a yi hulɗa da shi a lokacin da yake APC, musamman wadanda s**a nuna masa goyon baya da kauna, tare da yi musu fatan alheri a rayuwarsu.
Hamisu ya roki Allah ya sa wannan sabuwar tafiyar da ya shiga ta jam’iyar ADC ta zamo masa alheri, inda ya kammala sanarwar sa da kalamai masu cike da farin ciki: “Sabon Dan Jam’iyar ADC”.
Gwamna Radda ya kai ziyara Sayaya, ya ba da umarnin ƙarfafa tsaro bayan harin ‘yan ta’adda
🎥 FB- Ahmed Rabiu
06/04/2026
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature D/Tofa, ya cire mukaminsa a shafinsa na Facebook.
Wannan na zuwa ne bayan da tun daga ranar 31 ga watan Maris ba a sake jin wata sanarwa daga ofishinsa ba, abin da ya haddasa rade-radin cewa mai yiwuwa ya ajiye mukaminsa.
Matakin cire mukami daga shafin sada zumunta na Facebook ya kara karfafa zargin da ake yi cewa Sanusi Bature na iya shirin tsunduma cikin harkokin takara, la’akari da tanadin kundin tsarin mulkin kasa da ke bukatar masu rike da muk**an gwamnati su sauka kafin shiga takara.
Sai dai, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gare shi ko daga gwamnatin jihar Kano da ke tabbatar da saukarsa daga mukamin ko kuma akasin haka.
06/04/2026
Bismillahir Rahmanir Rahim
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai.
A yau muna farin cikin ƙaddamar da sabon shafin mu na yada labarai ArewaNow.
Manufarmu ita ce kawo muku sahihan labarai cikin sauri, gaskiya da kuma tsari mai inganci, domin ku kasance cikin masu sani a kowane lokaci.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya sanya albarka a wannan tafiya, Ya ba mu ikon yin adalci, Ya tsare mu daga kuskure, Ya kuma sa wannan dandalin ya zama alheri ga al’umma baki ɗaya.
Allah Ya sa mu dace, Ya ba mu nasara, Ya kuma sanya wannan aiki ya zama sanadin cigaban Arewa da ƙasa baki ɗaya.
Muna fatan goyon bayanku, shawarwarinku da addu’o’inku.
ArewaNow Team.
Click here to claim your Sponsored Listing.