Guarantee News Update

Guarantee News Update

Share

01/04/2026

Labaran Guarantee

Mawakin Gambara Ya Zama Sabon Firaminista A Nepal

15/03/2026

Labaran Guarantee

NLC Ta Nemi a Ba Ma’aikata Alawus na Tsadar Rayuwa Yayin da Farashin Fetur Ya Kai Naira 1,300

Nigeria Labour Congress (NLC) ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta fara bai wa ma’aikata alawus na tsadar rayuwa (Cost-of-Living Allowance) bayan da farashin fetur ya haura zuwa kusan Naira 1,300 kan kowace lita a wasu sassan kasar.

Kungiyar ta bayyana cewa tashin farashin fetur yana kara jefa ma’aikata cikin wahalar rayuwa, domin farashin sufuri, abinci da sauran kayan masarufi suna ci gaba da tashi.

NLC ta ce duk da karin albashin mafi karanci, har yanzu ma’aikata na fuskantar matsin tattalin arziki saboda hauhawar farashin kayayyaki. Saboda haka ta roki gwamnati da ta samar da wani kari na musamman a albashi domin taimaka wa ma’aikata su iya jure tsadar rayuwar da ake ciki.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano