WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU
26/08/2022
SHIRIN TAFIYA
Daga
Nasiru G. Ahmad
1. Tsarki ya tabbata gun Tabara Ubangiji,
Ya Rabbi salli alaihi Manzon tsira.
2. Manufa ga baitoci tunatarwa ga mu,
Tafiyar da ke a gabanmu babu matsera.
3. Ya ɗan uwa mai ruɗuwa zam tuntunin,
Tsayuwar ƙiyama wadda ke da haɗurra.
4. In Nura (haske) ke kiran ka a duniya,
Kar ka sake gobe ka zam ba nura.
5. An yi hanin ka giya da cewa kar ka sha,
Ka bi umarnin har ka ce ban ƙara.
6. Amma fa kai tatul kana mayen giyar,
Zaluntakar bayi kana ta gadara.
7. Ba ka sha ta kwalbaye giya a ciki naka,
Ka maƙare shi da cin haram da ka tara!
8. Shin me ka shirya faɗi idan ka wai gari,
Ƙabari gaba naka Munkarin da Nakira?
9. Shin me ka shirya faɗi idan an tsai da kai.
Ƙasƙance nan a gaban Gwani Jabbara.
10. Domin hisabin ayyukan da ka aikata,
Mai kyau da dukkan sharrukan da ka ƙera?
11. Ga masu haƙƙoƙi da kai zaluntaka,
Sun zo biɗa ba za su bar maka zarra!
12. Ba za ka samu abin biya sai ayyuka,
Na ƙwarai da kai ko zunubansu ka ƙara.
13. Da ka mace an zam ƙabarce ka zamo,
Kai kai kaɗai sai ayyukan da ka tara.
14. Duk masu bin ka suna yabo da hidimtuwa,
Sun bar ka can ba wanda zai maka kara.
15. Ranar mutum zai gwammace bai shugaban-
ci ba idan ya ga nauyukan da ya tara.
16. Bayan zamowa mai isa mai ɗaukaka,
Rami abin ƙunci cikinsa ka tura.
17. Ya tashi ran tsayuwar ƙiyama zigidir,
Mai damuwar loton da ya yi asara.
18. Shin za ka yarda rayuwarka a ɗaukake,
Haske na zuci ya tafi ba saura?
19. Wato ya zam bautar jiki aiki naka,
Wannan da tsutsa za ta ci a ƙaburra!
20. Shin za ka yarda waninka ne zai ɗaukaka,
A cikinta Aljanna da matan Hura.
21. Kai ko kana can a ƙuƙumce Zabaniya-
wa na bugu a cikin wuta mai rura?
` 22. Tun fari nan hujja da za ka riƙa zuwa,
Gaban Ilahu don ka san yin tsira.
23. Tsafce abincinka ya zam na halaliya,
Da abin hawanka gida tufar da ka ɗaura.
24. In kai haka sai addu’arka ta karɓuwa,
Ba shamaki ga Ilahu lailu nahara.
25. Zam ba da haƙƙoƙin dukan mai haƙƙuwa,
A kanka zaluntar su kadda ka fara.
26. Fara gidanka ka sauke dukkan nauyuka,
Ka sanar da su Tauhidi don su yi tsira.
27. Haƙƙi na Allah za ya yafe in ya so,
Haƙƙin mutane bai barin ko zarra.
28. Duba Izazul can zuwa ƙarshe nata,
Domin shirin riskar abin da ka ƙera.
29. Ka kyauta hanyoyin biɗarka a kowashe,
Sai Rabbi yai albarkatar su ya ƙara.
30. Kyauta ginin ɗakin da za ka yi kwanciya,
Bayan fitar ruhi jiki bai shura.
31. Yawaita yin Istingifari kowashe,
Zikiri a koyaushe da kyauta ɗahara.
32. Kafin ka tsaftace gaɓɓuwa ya ɗan uwa,
Tsarki na zuci ya kamata ka fara.
33. Tsafce zukata daga dukkan hassada,
Yi da mutane ba shi kai ka ga tsira.
34. Nufi Ilahu da ayyukanka kar ka nan,
Yardar mutane za ta ja ka asara.
35. In ka yi aiki don mutane sui yabo,
Ladanka ke nan gobe ba ka da saura.
36. Allah nufe mu da kyauta aiki ba riya,
Sai don biɗar yardarka ya Gaffara.
37. Allah tsare mu da sharrukan a’ada’u,
Maƙiyanka Rabbi Yahudu har da Nasara.
38. Sanya Shahada ta zamo furucinmu,
Ran tafiyar ruhi da babu matsera.
39. Darajar Rasulu abin yabo albarkacin,
Ƙur’ani wanda muke tila mui tsira.
40. Nasiru G. Ahmad wani almajirin,
Ilimi a kullum baitukan ga ya tsara.
41. Ashirin da ɗai baiti da ƙarin Ashirin,
Ran Juma’a don ni da ku mu yi mora.
Alhamdu lillahi.
21ga Muharram, 1444 (B.H.)
19 ga Agusta, 2022
01/08/2022
WAƘAR KUƊI
Daga
Nasiru G Ahmad
1. Rabbi ban iko na tsara,
Baituka kar nai gazawa.
2. Yau batu zan kan nuƙudu,
Ko ko money ba sakewa.
3.Mallakar su tana da daɗi,
Duniya ba mai musawa.
4. Laƙani na farin jini ne,
Ba ƙiyayya sai biyewa.
5.Maganin huce takaici,
Duniyar ga kana sakewa.
6. Duk batunka abin yabo ne,
Aibukanka suna ɓacewa.
7. Kai da Sarki har su gwamna,
Sai abota ba rabewa.
8. Dukka faɗin duniyar nan,
Za ka je lale anai wa.
9. Dukka yare za ka ji shI,
Don ko Naira ta iyawa.
10. A gida ba babba sai kai,
Duk batunka ba a ƙiyawa.
11. 'Yan uwa su taho gare ka,
Lamarinka suna yabawa.
12. Fa'idojin ba su ƙirgo,
In da money ka hayewa!
13. Aibuka zan bayyana su,
Don dukanmu mu zam kulawa.
14. Kar ka manta akwai hisabi,
Kan abin da ka mallakawa.
15. Shin ta yaya kab biɗe su?
Haka yadda ka zan kashewa.
16. In ka tara sai ka koma,
Fargabar su zamo ɓacewa,
17. Ga ɓarayi na fakon ka,
Ko ina ka yi ba sakewa.
18. Hankalinka yana gare su,
Ko da yaushe kana tunawa.
19. "Ga kuɗina can ga wane,
Gobe haja za ta zowa."
20. To ina nutsuwar ibada,
Gun Tabaraka mai iyawa?
21. Ƙoƙarin tsare dukiya na,
Sa ralala ai biyewa.
22. Sai ka ga an kai ga tsafi,
Sihiri an rungumewa.
23. Har a kai shirka da Allah,
Dukiya don ai tsarewa.
24. Son da kowa ke gare ka,
Ka sani ƙarya sukewa.
25. Don a samu abin riƙa ne,
In fa babu suna bajewa.
26. In ka so ka farar dabara,
Hidimar dini ka yowa.
27. In halal ce dukiyarka,
Rabbi zai karɓa yabawa.
28. Ba a ba Allah haramun,
Ɗayyibun yake bai riƙawa.
29. Don haka mu biɗi halali,
Don haram ba ta daɗewa.
30. Dukiya ta halali za ai
Wa hisabi ran tsayawa.
31. In haram ce sai uƙuba,
Ga Jahannama ke direwa.
32. Dan uwa gode wa Allah,
Lafiya da yake ta baiwa.
33. Sana’arka riƙe da kyawu,
Ƙwadagonka zamo kulawa.
34. Kar ka raina abin riƙawa,
Na halal shi ke daɗewa.
35. Zam ƙana'a kar ka damu,
In asiri yai rufewa.
36. Nemi albarkar Ilahu,
Godiya ka yi zai daɗawa.
37. Ko da yaushe mu roƙi Allah,
Mu yi kyan ƙarshe gamawa.
38. ‘Yan uwa da ka jarrabe su,
Dukiyarsu ta yi yalwa.
39. Rabbi sa su bisa tafarki,
Mustaƙim ba kangarewa.
40. Ba su ikon taimakawa,
Da halal mai tsarkakewa.
41. Mu talakkawa ka ba mu,
Hakuri da kaɗan mu yowa.
42. Zan tsaya haka ‘yan uwana,
Baitukan nai kammalawa.
43. Nasiru G. Ahmadu ne,
Ya yi waƙar don tunarwa.
Alhamdu lillahi.
28 / 4 / 2014
25/05/2022
JAHILCI MUGUN CIWO
Daga
Nasiru G. Ahmad
1. Ilahi makagi da ke da sani,
Na komai da ke ba da dukkan sani,
Ka tsarshe mu jahalu ka ba mu sani.
2. Salati ga Manzo da ya fid da mu,
Duhun jahalu Nuru ya fid da mu,
Abin taƙamarmu a yau ilimi.
3. Batuna a yau jahili zai nufa,
Da ma jahilancinsa ba zan rufa,
Domin ya tashi ya zam rarrafa.
4. Haba ɗan uwa me kake ta jira,
Da ba ka biɗar ilmu kai hattara,
Sai dai yawan ci ba ka haƙura?
5. Ka tashi maza riƙi alƙalami,
Ka je ko'ina ka biɗo ilimi,
Don fid da kanka cikin zulumi.
6. Ina gimbiyar kyau gwanar shakara?
Wajen ilimi babu ko saɗara,
Sai ji-da-kai tafi can amara!
7. A yau ba a yayin ku ke jahila,
Mai kyan ɗabi'a ka so adila,
Mai ilimi da yawan hattara.
8. Ki tashi ki nan ilimi kin jiya,
Ya zam "Make-up" naki duk safiya,
Abin taƙamarki da yin sangaya.
9. A yau ba ka zamto abin fahari,
Gidanku da dangi da ma duk gari,
Sai ka yi ilimu kana nazari.
10. A yau ba ka zamto ka mai unguwa,
Ko kansila har ka zam zaɓuwa,
Sai ka yi ilimu kake karɓuwa.
11. Rashin ilimi shi ka sa ɗimuwa,
A duk lamuran yau ka zam damuwa,
Dukan izgili daɗa kai za a wa.
12. Rashin ilimi shi ka sa kibru,
Da zagin iyaye da yin sihiru,
Da duk ayyukan Iblis makiru.
13. Akwai sad da matar wani jahili,
Ta ɗebo takardunsa jingim tuli,
Ta tura wuta ta dafe dankali!
14. Takardun gidajensa ne dukkani,
Kaza kwangila wadda zai ta gini,
Cakinsa na banki ya kone tuni!
15. A dole ya dauki asara haka,
Rashin ilimi ne ya jawo haka,
Jaahilu kam bai ganin ɗaukaka!
16. Idan jahili yai batu a gwale,
Wurin sanya hannu ko sai dangwale,
Lamurransa za ka ga sun dagule.
17. Cuta mafi munana jahalu,
Da ke sa mutum tsakiyar wahalu,
Da dumbin takaici ga mai hankalu.
18. Kaɗai maganinta biɗar ilimi,
Na boko da Arbi wurin malami,
Domin fita daga duk zulumi.
19. Akwai makarantu mataki-mataki,
Na yara da manya domin a dauki,
Darussa na ilmu bisa ga tafarki.
20. Nan 'yan uwa zan zamo diga aya,
Allah ya ba mu zama lafiya,
Da haske na ilmu a duk safiya.
21. Nasiru Ahmadu ne ya yi ta,
Domin a bar jahilanci ɓata,
A nemo sani ne kawai mafita.
22. Baiti guda sha ɗaya sau biyu,
Ya Rabbi salli ala An-Nabiyyu,
Da ya zo da dinin ƙwarai muka shiryu.
5 ga Mayu, 2002
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano