Singer Market Development Association SIMDA

Singer Market Development Association SIMDA

Share

20/05/2026

PRESS RELEASE

20/05/2026

The Executive Chairman of Singer Market Development Association (SIMDA), Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq.., on behalf of the leadership and entire members of the association, cordially invites members of the press, stakeholders, community leaders, business associates, and the general public to the Opening Ceremony of the Juma’a Mosque jointly built in collaboration with Hamir Global Ventures and Givanas Group of Company.

The event is scheduled to hold as follows:

Date: Friday, 22nd May 2026

Time: 12:00 PM

Venue: Masjidil Imam Malik Rummawa Gabas, Sauna Kawaji, close to National Open University, Ungoggo L.G.A, Kano State, Nigeria.

This occasion marks another significant milestone in community development, unity, and religious advancement within Singer Market and its surrounding communities.

Your esteemed presence and media coverage will be highly appreciated.

Signed:
Amb. Abubakar Usman Ali, Secretary
For: Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq
Executive Chairman Singer Market Development Association (SIMDA)

“Together Towards Progress and Community Development.”

Photos from Singer Market Development Association SIMDA's post 12/05/2026

12/05/2026

Shugaban Gammayyar Kungiyar Cigaban Kasuwar Singa da kewayenta (SIMDA), Barr. Junaidu Muhammad Zakari, Ya Karɓi Bakoncin Sabon Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, a Ofishinsa.

Mai Girma Shugaban Kasuwar Singer (SIMDA), Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq., ya karɓi bakuncin Sakataren Zartarwa na Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, a yau yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai ofishin shugaban da ke Kasuwar Singer a jihar Kano.

A yayin ziyarar, Barrister Junaidu Muhammad Zakari ya taya Dr. Ibrahim Garba Muhammad murnar naɗin da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano ya yi masa. Ya bayyana sabon Sakataren Zartarwan a matsayin mutum mai ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa wajen aiki, wanda shugabancinsa zai kawo ci gaba mai amfani ga kare haƙƙin masu saye da bunƙasa harkokin kasuwanci a faɗin jihar.

A nasa jawabin, Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce samar da haɗin kai da kyakkyawar alaƙa tsakanin Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye na Jihar Kano da Ƙungiyar SIMDA. Ya jaddada muhimmancin yin aiki tare domin dakile matsaloli tare da hana yaduwar kayayyakin da ba su dace da amfanin ɗan Adam ba a kasuwannin jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen wayar da kan ‘yan kasuwa da masu sana’o’i kan ingantattun hanyoyin gudanar da kasuwanci tare da kare muradun masu saye da masu sayarwa baki ɗaya.

A cewarsa, manufar wannan yunƙuri shine tsaftacewa da kare martabar kasuwancin Jihar Kano tare da samar da ingantaccen muhalli mai lafiya ga harkokin kasuwanci.

Haka kuma,Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya tabbatar wa ‘yan kasuwa cewa Gwamnatin Jihar Kano a shirye take domin tallafa wa harkokin kasuwanni da inganta yanayin kasuwanci. Ya buƙaci shugabannin Kasuwar Singer da su yi aiki kafada da kafada da Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye domin cimma manufofin da aka sa gaba don amfanin ‘yan kasuwa da masu saye baki ɗaya.

Sakataren Zartarwan, wanda ya k**a aiki a hukumance a yau, ya bayyana cewa ziyarar da ya kawo ofishin Shugaban SIMDA shine aiki na farko da ya fara yi tun bayan k**a aikinsa.

Taron ya gudana cikin nasara tare da tattaunawa mai amfani tsakanin ɓangarorin biyu. Mambobin tawagar Sakataren Zartarwan sun samu kyakkyawar tarba daga shugabannin SIMDA da s**a haɗa da Alh. Aminu Umar Dogara Mataimakin Shugaba na daya, Amb. Abubakar Usman Ali Sakatare, Barr. Abdullahi Usman Mashawarci kan harkokin Shari’a, Alh. Nasiru Idris Nanu Ma’aji II, da Mal. Bashir Umar Bello PRO II, waɗanda suma s**a bayar da gudummawa mai amfani tare da kalaman ƙarfafawa domin samun nasarar Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye ƙarƙashin sabon jagoranci.

Barrister Junaidu Muhammad Zakari ya kuma miƙa takardar shawarwari a rubuce ga Sakataren Zartarwan.

An kammala taron cikin fahimtar juna da tabbatar da haɗin kai da jajircewa wajen samar da kasuwanni masu aminci, kare haƙƙin masu saye, da bunƙasa harkokin kasuwanci mai ɗorewa a Jihar Kano.

Sa Hannu:
Amb. Abubakar Usman Ali, Sakatare
A Madadin: Alh Junaidu Muhammad Zakari Esq
Shugaban Kasuwar Singa (SIMDA)

Photos from Singer Market Development Association SIMDA's post 12/05/2026

12/05/2026

The Executive Chairman Singer Market Development Asoociation (SIMDA) Barr. Junaidu Muhammad Zakari Receives The New Executive Secretary of Kano State Consumer Protection Council Dr. Ibrahim Garba Muhammad in his office.

The Executive Chairman of Singer Market Development Association (SIMDA), Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq., today received the Executive Secretary of the Kano State Consumer Protection Council, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, during a courtesy visit to the Chairman’s Office at Singer Market, Kano.

During the visit, Barrister Junaidu Muhammad Zakari congratulated Dr. Ibrahim Garba Muhammad on his appointment by the Executive Governor of Kano State. He described the Executive Secretary as a hardworking, dedicated, and committed individual whose leadership would positively contribute to consumer protection and the development of commercial activities within the state.

In his remarks, Dr. Ibrahim Garba Muhammad stated that the purpose of the visit was to establish synergy and cooperation between the Kano State Consumer Protection Council and the Singer Market Development Association (SIMDA). He emphasized the need to work together in curtailing nuisance and preventing the circulation of goods that are not fit for human consumption in markets across Kano State.

He further explained that the partnership would help educate traders and marketers on proper business practices while protecting the interests of consumers, buyers, and sellers. According to him, the initiative is aimed at sanitizing and preserving the commercial heritage of Kano State and promoting a safe and healthy business environment.

Dr. Ibrahim Garba Muhammad also assured traders of the Kano State Government’s readiness to support market activities and improve business conditions. He urged the leadership of Singer Market to work hand in hand with the Consumer Protection Council in achieving its objectives for the benefit of traders and consumers alike.

The Executive Secretary, who officially assumed office today, and that the visit to the Office of the Executive Chairman of SIMDA was his first official assignment since assuming office.

The meeting recorded fruitful deliberations between both parties. Members of the Executive Secretary’s entourage were warmly welcomed by executives of SIMDA, which include Alh. Aminu Umar Dogara Vice Chairman, Amb. Abubakar Usman Ali Secretary, Barr. Abdullahi Usman Legal Adviser, Alh. Nasiru Idris Nanu Tresure II and Mal. Bashir Umar Bello PRO II, who also made valuable contributions and offered words of encouragement toward the success of the Consumer Protection Council under the new leadership.

Barrister Junaidu Muhammad Zakari also presented a written advisory note to the Executive Secretary for guidance and encouragement in the discharge of his official responsibilities.

The meeting ended with mutual assurances of cooperation and commitment toward ensuring safer markets, consumer protection, and sustainable commercial development in Kano State.

Signed:
Amb. Abubakar Usman Ali, Secretary
FOR: Junaidu Muhammad Zakari Esq
Executive Chairman Singer Market Development Association (SIMDA)

11/05/2026

"Idan Allah ya kaimu gobe Talata 12/05/2026 Titin Ado Bayero Road zai kasance a rufe (domin hana Zirga-zirgar ababan hawa) har zuwa tsawon makwanni (5) domin baiwa masu gudanar da aikin t**i damar kammalawa akan lokaci"

Barr. Junaidu Muhammad Zakari.
Shugaban Kasuwar Singa, Kano.
11/05/2026

11/05/2026

✨Saƙo na Musamman daga:

Barr. Junaidu Muhammad Zakari.
Shugaban Kasuwar Singa, Kano.

11/05/2026

07/05/2026

📻📻📻

Ku kasance tare da Mai Girma Shugaban Kasuwar Singa, Barr. Junaidu Muhammad Zakari da misalin ƙarfe 4:30 zuwa 5:00 na yammacin wannan rana domin jin tattaunawa ta musamman akan muhimman batutuwa da s**a shafi Kasuwar Singa da Ƴan Kasuwa daga gidan rediyon Arewa mita 93.1

Dafatan za'a tara domin jin yadda wannan tattaunawa zata kasance.

Sashin Hulɗa da Jama'a na Kasuwar Singa.
07/05/2026

Photos from Singer Market Development Association SIMDA's post 04/05/2026

SAƘON BANGAJIYA DA FATAN ALKHAIRI NA AUREN DAN MAL. HAMISU RABI'U JINGAU (HAMIR GLOBAL VENTURES)

A ranar Asabar 02/05/2026 mai girma Shugaban Kasuwar Singa Barr. Junaidu Muhammad Zakari, ya halarci daurin auren Ɗa a gurin Babban Sakataren Kwamitin Amintattu na Kasuwar Singa Mal. Hamisu Rabi’u Jingau (Hamir Global Ventures) Muhammad Ibrahim Ali Amin da Amaryarsa Fatima Abdullahi Abbas, wanda aka daura a Unguwar Sagagi Gidan Galadiman Kano, Jihar Kano.

Shugaban ya taya amarya da ango murna, yayi musu fatan zaman lafiya, soyayya da albarka mai ɗorewa, tare da addu’ar Allah Ya sanya aurensu ya zama na alheri, kwanciyar hankali da samun zuri’a ta gari.

A ƙarshe "Shugaban kasuwar Singa Barr. Junaidu, ya bayyana saƙon bangajiya ga ilahirin mahalarta wannan gagarumin taro, a madadin Uban ango Mal. Hamisu Rabi’u Jingau (Hamir Global Ventures) inda yace a miƙa masa godiya da fatan Alkhairi".

✍️Sashin Hulɗa da Jama'a na Kasuwar Singa.
Bashir Umar Bello
04_05_2026

Photos from Singer Market Development Association SIMDA's post 01/05/2026

Assalamu Alaikum

Mai girma Shugaban Kasuwar Singa Barr. Junaidu Muhammad Zakari yana miƙo saƙon barka da Juma'a a gareku tare da fatan Allah ya karɓi dukkan ibadunmu, Allahumma Amin.

Haka kuma yana yiwa daukacin mahalarta bangajiya bisa halartar daurin Auren guda cikin masu ruwa da tsaki na wannan kasuwa Alh. Abdulkarim Ibrahim Maizare da ya gudana a garin Bichi cikin makon daya gabata, tare da addu'ar Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Amin.

24/04/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullah

Mai Girma Shugaban Kasuwar Singa, Barr. Junaidu Muhammad Zakari, na mika sakon barka da Juma’a ga daukacin al’ummar musulmi.

Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kurakuranmu, Ya kuma sanya wannan rana mai albarka ta zamo alheri a gare mu baki ɗaya.

Juma’a Mubarak🕌📿

07/04/2026

Mai girma Shugaban Kasuwar Singa.
Alh. Junaidu Muhammad Zakari Esq.

MB Umar Photography📸

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Office Address: Hauwa Sani Marshall Plaza 2nd Floor, Office N0. 266 Malam Kato Opposite Old Union Bank. Fagge LGA
Kano
700001

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00