Kano Pillars Fans Club Dala Chapter

Kano Pillars Fans Club Dala Chapter

Share

03/06/2023

Wan nan shine gaskiyar batu, Al'uma sunsan manufar mu tunkafin ma su zaɓe mu, kuma saboda suna so muyi rusau ɗin nema s**a zaɓemu.

03/01/2023

A cìkìn littafin "Rayúwa Bayan Mútúwa" bugú na biyu, shafi na 78, marigayi Dr Bashir Usman Tofa yana cewa: "Ni kaina na taɓa yin mafarkin na mutú, kuma babu shakka na ga gawata a cikin likkafani ana tafiya da ni izuwa maƙabarta.''

Allahu Akbar! Sai bayan shekaru 25 da bayar da labarin wannan mafarki na sa acikin littafin sa, sannan sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ransa, a Rana irin ta yau, 3 ga watan Janairu na shekarar da ta gabata ta 2022, wanda a wannan Rana ta yau yake da shekara ɗaya daidai da komawa zuwa ga mahaliccin sa.

Haƙiƙa daga cikin rayuwar wannan bawan Allah, na koyi abubuwa masu tarin yawa, musamman akan abun da ya shafi ƙara mayar da hankali wajen yin takatsantsan, tare da ƙara kiyayewa wajen sabawa Ubangiji na, da kuma tunanin yadda zan kasance bayan na mutu. Wato a duk lokacin da na zauna ina karanta wani littafi na Marigayi Dr Bashir Tofa, na kanji kamar muna tare da shi ne ina yi masa tambayoyi yana bani amsa, saboda tsabar tarin ilimi, da tarin basirar da yake zubawa acikin dukkanin maganganun sa. Tabbas anyi babban rashi a jihar Kano, Arewa, da ma Najeriya baki ɗaya.

Ina addu'a da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafartawa Dr Bashir Usman Tofa, Ya karɓi ayyukan sa na alkhairi, Ya sanya rahama a rayuwar sa ta bayan mutuwar sa, Yasa Al-Jannah ce makoma a gare shi, Amin.

DÁGA Adamu Kazaure!
Ɗan Almajiri.

Want your establishment to be the top-listed Bar/pub in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Goron Dutse
Kano