Sani Shuaibu Suleman

Sani Shuaibu Suleman

Share

01/12/2022

SAHABBAI GOMA DA AKA YI MUSU BISHARA DA ALJANNAH

Daga Abdurrahman bin Auf cewa Annabi SAW ya ce: Abubakar dan Aljannah ne, Umar dan Aljannah ne, Usman dan Aljannah ne, Ali dan Aljannah Ne, Talha dan Aljannah ne, Zubair dan Aljannah ne, Abdurrahman bin Auf dan Aljannah ne, Sa'ad bin Abi wakkas dan Aljannah ne, Sa'id bin Zaid bin Amr bin Nufail dan Aljannah ne, Abu Ubaidah Binul Jarrah dan Aljannah ne.

Ahmad da Tirmidhi S**a ruwaito shi.

01/12/2022

Manzon Allah SAW ya ce: " Na bar muku Abubuwa biyu, ba za Ku bata ba matukar kuna rike da su: Littafin Allah da Sunnar Annabinsa".

Malik ne ya ruwaito.

01/12/2022

FALALAR SALATI GA ANNABI SAW

An kar6o daga fadalah ibn Ubaid RA ya ce, "Manzon Allah SAW ya ji wani mutum yana addu'a a cikin sallah amma bai girmama Allah ba, bai yi wa Annabi SAW salati ba. Sai Manzon Allah SAW ya ce masa ko ya ce wa waninsa: ' wannan (Mutum ya yi garaje , ' Sai ya kirawo shi ya ce masa: " idan dayanku zai yi addu'a sai ya fara da godiya ga Allah, ya kuma yabe shi, sannan ya yi wa Annabi SAW salati, daga nan sai ya roki abin da yake so".

Abu Daud, Nasa'i da Tirmidhi s**a Ruwaito.

01/12/2022

WANDA YA KAR6I DUKIYAR MUTANE YANA NUFIN YA BIYA, DA WANDA YA KAR6I DUKIYAR MUTANE YANA NUFIN HALAKAR DA ITA

Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Wanda ya kar6i dukiyar mutane yana mai nufin maido da ita, to Allah zai ba shi ikon biya. Wanda kuma ya kar6i dukiyar mutane yana nufin halakar da ita, to Allah zai lalata ta".

Bukhari ne ya ruwaito shi.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano