Zulfiqa Redio

Zulfiqa Redio

Share

17/02/2026

Yanzu-Yanzu.

Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky(H). sun sanar gobe Laraba zai zama 1 ga Watan Ramadana.

04/09/2025

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gayyaci Tsohon Gwamna El-Rufai Bisa Zargin Kalamai Masu Barazana

Kaduna, Najeriya – 4 ga Satumba, 2025
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta aike da takardar gayyata ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, *Malam Nasir Ahmad El-Rufai*, bisa zargin *kalamai masu tayar da hankali da barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

A cewar majiyoyi daga cikin rundunar, gayyatar na da nasaba da wasu kalamai da El-Rufai ya furta a cikin wani taron addini a baya-bayan nan, inda ake zargin cewa *jawabinsa na iya haddasa rikici da rarrabuwa tsakanin al’ummomin jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda, ya bayyana cewa an aike masa da gayyatar don ya bayyana gaban huk*mar domin karin bayani, ba wai an k**a shi ba.

> “Rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci kowanne irin yunkurin tayar da hankali ba, musamman daga manyan mutane da ke da tasiri cikin jama’a,” in ji jami’in hulɗa da jama’a.

Kawo yanzu, El-Rufai bai mayar da martani kai tsaye ba, sai dai wasu daga cikin magoya bayansa na cewa kalamansa an fassara su da wata manufa ta siyasa.

Zulfiqar Redio za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari domin kawo muku cikakken bayani yayin da abubuwa ke ƙaruwa.

---

**

Photos from Zulfiqa Redio's post 24/07/2025

📸Yadda Huda Abu Al-Naja ke kallon hoton ta kafin yunwa ta canza mata halitta 🥲

Kamar yadda kuke gani cikin hotuna wannan yarinya mai suna Huda Abu Al Naja mai kimanin shekaru 12 a duniya ke riƙe da hoton ta da aka ɗauka kafin Isra'ila ta jefa su cikin ƙangin azababbiyar yunwa.

Huda ƴar yankin Al-Mawasi ce dake Kudancin zirin Gaza, tana fama da matsananciyar yunwa wadda a yanzu ake tsammanin har ta kamu da cutar "Celiac disease".

Huda ɗaya ce daga cikin dubbunnan Palasdinawa da yunwa ta illata sak**akon toshe hanyoyin shiga da abinci zirin Gaza da Isra'ila ta yi.

Zulfiqar Redio - Daga Gaza

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Kano Kofar Waika
Kano
NAIBAWA