Hamza

Hamza

Share

27/04/2026

Tarihin Sahabbai

Mus'ab bn Umayr (RTA). : مصعب بن عمير.

Muṣ'ab ibn ʽUmair (RTA) wanda aka fi sani da Mus'ab al-Khayr sahabi ne na Annabi Muhammad (SAW). Daga Banū ʽAbd al-Dār reshen kuraishawa, ya musulunta a shekara ta 614 miladiyya kuma shi ne jakadan Musulunci na farko. Ya rasu a yakin Uhudu a shekara ta 625 miladiyya. Yana da Shekaru 30. Mahaifinsa shi ne Umair bin Hashim, Mahaifiyarsa kuma ita ce Khunaas Bint Malik.

Ba a san ainihin tak**aiman shekarar haihuwarsa ba; ana kyautata zaton an haife shi ne a tsakanin shekara ta 594 zuwa 598 miladiyya, tun yana karami ya musulunta a shekara ta 614 Miladiyya, iyayensa sun kasance ma su arziki.

Musulmin farko, kafin Musulunci ya yi karfi, sun kasance suna ganawa da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam a gidan Al-Arqam da aka fi sani da Cibiyar Koyon Musulunci. Mus’ab ya yi sha’awa, ya ziyarci gidan domin neman karin bayani game da Musulunci. Sak**akon jin karatun Alkur'ani da wa'azin Annabi Muhammad Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.

Bayan ya musulunta da farko Mus'ab ya buye Imaninsa don yana tsoron ka da mahaifiyarsa ta sani" Sai dai wata rana wani dan kuraishawa mai adawa da Annabi, Uthman bn Talha, ya gan shi ya shiga gidan Al Arqam, yana shiga yayi salla tare da musulmi, sai labarin ya bazu, daga karshe dai labari ya isa wajen mahaifiyarsa, ta daure shi a gidansu da nufin ta sa shi ya ya koma Kafirci, Mus’ab ya kasance mai kwarin gwiwa a kan imaninsa, kuma ba zai barranta daga imani ba. Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya shawarce shi da ya shiga cikin sahabban don yin hijira zuwa kasar Abisiniya, don ka da a sake muzguna masa.

An nada Mus’ab bn Umayr a matsayin jakadan Musulunci na farko kuma an aika shi zuwa Yasriba (Madina) don shirya garin don Hijira. bayan mubaya’ar farko ta ansar (Mazauna Madina), wani mutumin Madina mai suna Asad bn Zurarah ya taimake shi. Bayan sun yi wa'azin Musulunci, mazauna Madina da yawa sun musulunta, ciki har da Sa'ad bn Mu'adh, da Usayd bn Hudayr da Sa'ad bn Ubadah (duka Allah ya kara musu yadda).

Yakin Badar.

Ya halarci yakin Badar tare da sojojin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda su ka hada da Sayyadina Ali (AS) Sayyida Hamza, (AS) sai Az-Zubair bn Al-'Awwam, (RTA) da Ammar bn Yasir, (RTA) da Abu Dharr al-Ghifari (RTA). Haka kuma musulmi sun taho da rakuma saba’in da dawakai biyu, ma’ana ko dai mafi yawansu sun yi tafiya a kasa ko kuma a sanya mutum uku zuwa hudu a kan kowane rakumi. Duk da haka, yawancin musulmi a lokacin basuyi tsammanin za a hwabza wani mummunan yaki ba.

Shahada A Yakin Uhudu

A yakin Uhud an gwabza a shekara ta 624 miladiyya, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya sanya Mus'ab bn Umayr ya dauki tutar musulmi.

A lokacin yakin, da wasu musulmi su ka ga amfara samun nasara akan kafirai, sai su ka bar kan dutsen da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama yayi musu umarni da su tsaya, ashe ba su sani ba Khalid Ibn Alwalid (sannan bai musulunta ba) yana bayan dutsen da shi da wasu dakaru, su na ganin haka sai su ka biyo ta bayan mummunai da sara, kafiran da a ka farawa rararakawa da su ka ga rundunar Khalid daga baya sai s**a juyo su ka sanya Musulmi a tsakiya su ka fara kisa har wasu dakarun kafirai s**a nufi inda Manzon Allah Sallallahu Alaihi yake domin su kai masa hari,

Da Mus'ab yaga haka ya fahimci hatsarin da ke tattare da hakan, sai ya daga tutarsa ​​ya yi ta kabbara (ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR ) da nufin karkatar da hankalin makiya zuwa ga da kansa, don subar Annabi (SAW), cikin hakan a ka kai wa Mus'ab hari, aka yanke hannunsa na dama da ke rike da tuta, amma sai ya ci gaba da maimaita kalmar ALLAHU AKBAR, ya dauke tutar da hannun hagu. Lokacin da aka yanke hannunsa na hagu sai ya k**a ta da Kasangalalin hannayensa amma bai bari tutar ta fadi ba. "Daga karshe dai Ibn Kami’ah ya jefi Mus'ab fa Mashi ya yi shahada.

ALLAHU AKBAR.

Shidai mus'ab Ya taso a cikin jin dadi, gashi dan gata kuma kyakkyawa mai iya ado, dukkan wani taro baya cika idan babu Mus'ab a cikinsa. Yana cikin wannan hali ne ya sami labarin kiran musulunci ta bakin amintacce Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, bai yi jinkiri ba wajen amsa kiran duk da sanin irin matsin da zai fuskanta. Mus'ab ya hakura da dukkan jin dadin duniya, ya maye shi da dandanar kuda da azabtarwa daga mutanensa. Wata rana mus'ab ya taho gurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sahabbai sun kewaye shi, lokacin da s**a hango Mus'ab s**aga irin halin da ya shiga na kunci da takura sai s**a sunkuyar da kawunan su suna kuka saboda tausaya masa. A ranar yakin Badar shine yake rike da tutar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam babbar ta Muhajirun hak**a a yakin Uhudu inda a ranar yai shahada. An ruwaito Annabi sallallahu alaihi wasallam ya tsaya a gaban Mus'ab da sauran wanda s**ai shahada a Uhudu yana cewa: "Lallai zanyi muku shaida cewa ku shahidai ne a gurin Allah ranar Alkiyama"

27/04/2026

Tarihin Annabawa

Tarihin Annabi Ayyub (AS)

Annabi Ayyub (Ayyuba) zuriyar Annabi Ibrahim ne. Mahaifiyar Ayyub diya ce ga Annabi Ludu, kuma matarsa ​​ta kasance zuriyar Annabi Yusuf kai tsaye. Ayyub ya zauna a Roma tare da masoyiyar matarsa ​​Rahma da 'ya'ya goma sha hudu.

Ibn Ishaq yace Annabi Ayyub (Ayyuba) nasabarsa ita ce Ayyub Ibn Musa Ibn Razih Ibn 'Ees bn Ishaq Ibn Ibraheem (amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya).

Sai dai wasu sun ce nasabarsa ita ce Ayyub bn Musa bn Ra'ooeel bn Ees bn Ishaq bn Ya'qub (amincin Allah da amincin Allah su tabbata a gare su baki daya).

Don haka madaidaiciyar magana shi ne cewa ya fito daga zuriyar ‘Ees Ibn Ishaq Ibn Ibraheem (amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya). Dangane da sunan matarsa, an ce ita ce Leea bint Ya’qub (amincin Allah su tabbata a gare shi). Wasu kuma s**a ce sunanta Rahmah bint Ifratheem. Wasu kuma suna da'awar cewa ita ce Leea bint Mansa Ibn Ya'qoob (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Wannan shi ne ra'ayi mafi shahara. Allah Shi ne Masani.

Ayyub Annabi ne wanda Allah ya yi masa ni'ima mai yawa- yana da karfi da lafiya, yana da filaye masu yawa, da dabbobi masu yawan gaske, da iyali na kwarai kuma kyawawa; kana ya kasance shugaban al'umma wanda al'ummarsa ke matukar mutuntawa da kaunarsa.

Duk da matsayinsa da arzikinsa, Ayyub bai taba girman kai ba; ya kasance mai tawali’u a kodayaushe, ya kasance mai saurin taimakon wanda bashi da shi, kuma ya kasance yana gode wa Allah da tasbihi a kan duk abin da ya yi masa na albarka.

Ayuba ko Ayyub (da Larabci: اَیّوب ) Annabin Allah ne, ya sha fama da cututtuka da asarar 'ya'yansa da dukiyarsa. Ya kasance mai hakuri a lokacin jarrabawarsa, bai gushe ba yana yin ibada da godiya ga Allah.

Kur'ani bai ambaci cikakkun bayanai game da jarrabawar da akayiwa Annabi Ayuba ba, amma Littafin Bible da wasu hadisai na musulunci sun ruwaito cewa mutane sun fara nisantar da Ayuba (AS) saboda ciwonsa. Kur'ani bai ambaci komai game da hakan ba sai dai ya yaba masa don haƙurinsa.

A cewar malaman tafsirin, Ayuba (AS) ya yi rantsuwa cewa zai yi wa matarsa ​​bulala dari amma daga baya ya yi nadamar yin irin wannan rantsuwa. Sai aka yi wahayi zuwa gare shi cewa ya buge ta Sau guda ɗaya da tarin Bulalai ɗari, ya kiyaye rantsuwarsa ta aiwatar da haka. Akwai sabani tsakanin masu tarihi kan dalilin rantsuwar Ayuba.

Babu tabbataccen bayani game da wurin da aka binne Ayuba (AS). Sai dai kuma akwai kaburbura da dama a kasashe daban-daban da ake danganta su gare shi, k**ar wani kabari kusa da Hillah a kasar Iraki

An ce Annabi nan aa aka ambata a cikin Al-Qur'ani Dhul-Kifl ɗan Ayuba (AS) ne, wanda sunan sa shi ne Bishr.

Ibn Jareer da waninsa sun ambaci cewa Ayyub (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rasu yana da shekara casa’in da uku. Wasu kuma s**a ce ya rayu fiye da haka.

Kafin ya rasu ya damka wa dansa Hawmal amanarsa dansa Bishr bayansa, Mutane da yawa suna cewa shi ne Zul Kifli, Allah ne Mafi sani. Su ma wadannan mutane suna da’awar cewa shi Annabi ne, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da biyar.

Ayyub (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya rayu a kasar Rum tsawon shekaru saba'in bayan gama jiyarsa. Ya yi musu wa'azi da addini da tauhidin Ubangiji guda. Sai dai daga baya sun canza addinin Ibrahim (AS) bayan rasuwarsa.

Annabi Ayuba A Cikin Alkur'ani

Lalle Mũ, Mun yi wahayi zuwa gare ka, k**ar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũbu da zuriyyaraa da Isah da Ayuba da Yũnusa da Hãrũna da Sulaimãn kuma Mun bai wa Dãwũda littãfi. (Suratul Nisa'i aya ta 161-163).

Waɗanda s**a yi ĩmãni, kuma ba su gauraya imaninsu da zãlunci ba, waɗannan sune amintattu, kuma sũ, mãsu shiryuwa ne. Kuma waccan ita ce hujjarMu, Muka bai wa Ibrãhĩm a kan mutãnensa. Muna ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so. Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Masani. Kuma Muka bai wa Ibrãhĩm da Is'hãƙa da Yãƙũbu, dukansu Mun shiryar dasu. Kuma Nuhu, Mun shiryar da shi a gabaninsu. kuma a cikin zuriyarsa, Dauda da Sulemanu da Ayuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kamar haka Muke sãka wa mãsu da kyautatãwa (Suratul Anam Ayat 82-84).

Kuma (ka ambaci) Ayuba, a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, "Lalle ne, cũta ta shãfe ni, kuma Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama." Sai Muka karɓa masa, kuma Muka kuranye abin da ya sãme shi na cũta. Kuma Muka ba shi iyalansa da kwatankwacinsa tãre da su, dõmin rahama daga gare Mu, kuma da tunãtarwa ga mãsu bauta. (Suratul Anbiya aya ta 83-84).

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani ikon bayar da labarin sahihin Tarihin Annabi Ayuba mai daraja.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Kano