Bawan Allah

Bawan Allah

Share

07/02/2024

Gare ka abokina: LOKACI YAYI!

Zan fadi maka gaskiya. Ba lallai tayi dadi ba. Amma haka take. Wallahi yanzu lokacin dogara da albashi musamman karamin albashi irin namu ya wuce. Lokaci ne yanzu da mutum zai zage damtse ya cire kasala ya cire jin kai da kunyar mutane ya nemi kuddi. A halin da ake ciki babu wani aikin k’ask’anci. Duk wani aikin da zai kawo maka taro—sisi to wallahi aiki ne me daraja.

Idan Allah be kaddare ka da kwarewa a wata sana’ar hannu ko wani skills da mutane ke bukatar expertise din ka ba, to lallai ka sani cewa lafiyar da Allah ya baka da karfi shi ma jari ne. Kaga duk ayyukan ga da a da baka iya yin su saboda kai ma’aikacin banki ne ko malamin makaranta ko honorable ake ce maka ko kuma office gare ka a ministry? To wallahi lokaci yayi da zaka cire rigar jin kai ka neme su.

Babu sana’ar da ba zaka iya zamanantar da ita ba a matsayin ka na me ilimi. K**a daga wankin mota, wankau, achab’a, noma, leburanci, nomau, dako, tura baro, sayar da ruwa, da sauran su, duk wanda ya fi maka sauk’i, ina kara nanata maka ya kai abokina, duk wanda yafi maka sauki wallahi kayi abinka. A halin hanzu babu issue irin yunwa. Haka kuma babu kaskanci a neman kuddi, duk kaskanci be fi ka tsaya jiran wani yayi maka ba.

Idan kuma Allah ya sa kana iya hakurin koyon skills k**an su walda, dinki, faci, painti, POP, da sauran su, to lallai ka mayar da hankali ka iya su saboda Allah kadai ya san ranar fita wagga cakwakiya. Kun dai ga wahalar lokacin Buhari ta sa mafi yawan mutane k**a online businesses. Wasu sun samu sa’a daga nan liyafa tayi sama. To ina mai nuna maku, wanga lokaci da k’wadago yazo, wato hard labour.

Abokina me karamin albashi, zan kara nanata maka, kada ka bari kunyan makwabta ko yan mata ko tsohhin abokan karatun ka ya hana ka yin sana’ar da aka raina. Babu raini irin ka tsaya jiran ayi maka. Dukkanin wadanda kake jin kunyar suyi gulman ka cewa kana kwadago, babu wanda zai baka idan baka da.

Hasalima still sai sun yi gulmar ka din cewa ka cika rok’e—rok’e. Ka kau ga ai gara ayi gulmar cewa yanzu dako kake yi da ayi gulmar cewa yanzu baka da aiki sai rok’e—rok’e. Tunda ita dai yunwa idan ta kawo visit to ai dole a saurare ta, ka kau ga option biyu ne; ko dai k’wadago a rufa ma kai asiri, ko kuma barace—barace.

Abokina na roki Allah ya rufa maka asiri ya baka mafita a dukkanin tsanani. Ka sani cewa komi yayi zafi maganin shi Allah kuma lallai duk wanda ya nema Allah zai bud’e mashi k’ofofin arzikin sa. Ba sai mun yi kuddi mun tai Makka mun tai Dubai ba, ba sai mun sayi mota ko mun gida katafaren gida ba. A’a in dai mun samu abinda munka rufa ma kan mu asiri, to AlhamdulilLahi🙏

Credit; Unclè Anass Dukura

07/10/2023

✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani
Wanne ne Bidi'a tsakanin Maulidi da Tafsiri a Watan Ramadhan?

Asali 'Yan Bidi'a sun yarda Maulidi Bidi'a ne. Sun san babu dalili na Shari'a da ya yi nuni a kan bikin Maulidin. To ganin Ahlus Sunna sun matsa musu da inkari, saboda Annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya yi bidi'a an mayar masa", kuma ya ce: "Kowace Bidi'a bata ce,, kuma tana wuta", to sai suke neman abokan bata, abokan shiga wuta. Ma'ana su ba za su dena bidi'ar ba, amma ku ma Wahabiyawa kuna yin bidi'a, don kuna yin Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi.

Wannan shi ake kira "Ilzami" a ilimin "Jadal da Munazara", amma sai dai hujja ce mai rauni a wajen "Mu'aradha", sai dai a yi amfani da "Ilzami" don nuna bacin ra'ayi ko bacin dalili, wannan kuma ba shi ne muhallin maganarmu da su ba.

Don haka abin tambaya shi ne; shin da gaske yin Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi bidi'a ne, ko yana da asali a Shari'a?

Lallai ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
«كان رسول الله صلى الله عليه وسلم أجود الناس، وكان أجود ما يكون في رمضان حين يلقاه جبريل، وكان يلقاه في كل ليلة من رمضان فيدارسه القرآن، فلرسول الله صلى الله عليه وسلم أجود بالخير من الريح المرسلة»
صحيح البخاري (1/ 8)، صحيح مسلم (4/ 1803)

"Manzon Allah (saw) ya kasance mafi kyautan mutane, kuma ya kasance mafi kyauta a cikin watan Ramadhan, lokacin da Mala'ika Jibril (as) yake haduwa da shi, ya kasance yana haduwa da shi a cikin kowane dare na watan Ramadhan, sai su yi DARASIN ALKUR'ANI TARE, lallai Manzon Allah (saw) ya fi iska mai kadawa yawan kyauta da alheri".

Wannan Hadisi ya nuna cewa; Lallai Annabi (saw) da Mala'ika Jibril (as) suna haduwa suna yin darasin Alkur'ani a kowane daren Ramadhan har ya kare.

Shi ya sa Ibnu Battal ya ce:
"ومدارسته له القرآن فى كل رمضان. وخص رمضان بذلك، لأن الله تعالى أنزل فيه القرآن إلى السماء الدنيا، ولتتأسى بذلك أمته فى كل أشهر رمضان، فيكثروا فيه من قراءة القرآن، فيجتمع لهم فضل الصيام والتلاوة والقراءة والقيام".
شرح صحيح البخارى لابن بطال (1/ 40)

Sai ya ce: suna yin Darasin Alkur'anin a kowane dare na Ramadhan ne don a Ramadhan din aka sauke Alkur'anin, kuma DON AL'UMMARSA SU YI KOYI DA SHI, su ma suna yin Darasin Alkur'anin a kowane watan Ramadhan.

Malamai masu sharhin littatafan Hadisai sun tabbatar da cewa; wannan Darasi na Alkur'ani a cikin Ramadhan MUSTAHABBI ne, saboda wannan Hadisi. K**ar al-Nawawiy, al-Ainiy, inda ya ce:
"ومنها استحباب استكثار القراءة في رمضان ومنها استحباب مدارسة القرآن وغيره من العلوم الشرعية".
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (1/ 77)

In kun lura shi har ma ya kara da sauran Ilmomin Shari'a, duka dogaro da wannan Hadisi na Ibnu Abbas (ra).

Sannan akwai Hadisin Abu Huraira (ra) wanda Muslim ya ruwaito, wanda ya fadi ladan masu haduwa a Masallaci suna Darasin Alkur'ani: Annabi (saw) ya ce:
«وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله، يتلون كتاب الله، ويتدارسونه بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده،».
صحيح مسلم (4/ 2074)

"Babu wasu mutane da za su taru a daki daga cikin dakunan Allah (Masallaci), suna karanta Littafin Allah, suna Darasinsa a tsakaninsu, face nitsuwa ta sauka a kansu, rahma ta lullube su, Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah zai ambace su a wajen wadanda suke wajensa".

Malamai sun yi sharhin Hadisin inda s**a bayyana cewa; Hadisin yana nufin mutane su taru a Masallaci, sashensu yana koyar da sashe, k**ar yadda Alkali Iyadh ya fada, inda ya ce:
"قال القاضى: قد يكون هذا الاجتماع للتعلم بعضهم من بعض، بدليل قوله: "ويتدارسونه بينهم"، ومثل هذا لم ينه عنه مالك ولا غيره".
إكمال المعلم بفوائد مسلم (8/ 195)

Shi kuma al-Dibiy shi ya fito da ma'anar DARASIN ALKUR'ANIN A FILI, inda ya ce:
"و"يتدارسون" شامل لجميع ما يناط بالقرآن من التعليم والتعلم، والتفسير، والاستكشاف عن دقائق معانيه."
شرح المشكاة للطيبي الكاشف عن حقائق السنن (2/ 665)، وانظر: مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح (1/ 287)

Ya ce: "Ma'anar suna Darasinsa" ya kunshi dukkan abin da yake rataye da Alkur'ani na koyarwa da koyo da TAFSIRI, da kuma binciko boyayyun ma'anoninsa".

Kuma wannan bai takaita ga Masallaci kadai ba, k**ar yadda Imam al-Nawawiy ya ce:
"ويلحق بالمسجد في تحصيل هذه الفضيلة الاجتماع فى مدرسة ورباط ونحوهما إن شاء الله تعالى ويدل عليه الحديث الذي بعده فإنه مطلق يتناول جميع المواضع ويكون التقييد في الحديث الأول خرج على الغالب لا سيما في ذلك الزمان فلا يكون له مفهوم يعمل به".
شرح النووي على مسلم (17/ 22)

Saboda haka idan mun lura da wadannan Hadisai guda biyu za mu ga cewa; MUSTAHABBI ne ana haduwa a Masallaci ko wani wajen daban, a cikin watan Ramadhan ana yin Darasin Alkur'ani, har watan ya fita.

Kuma Malaman sun ce: Ma'anar Darasin Alkur'ani shi ne a samu bangarori guda biyu suna karanta Alkur'ani, suna TAFSIRINSA, suna bayanin ma'anoninsa, sauran mutane kuma suna sauraro suna koyon ilimi.

Da wannan muke cewa; Tafsirin Alkur'ani a watan Ramadha yana cikin Addini, kuma Sunnar Annabi (saw) ne, kuma Mustahabbi ne. Aikin lada ne mai girma. Don Allah zai saukar da Mala'iku su kewaye su, kuma nitsuwa za ta sauka a kansu, rahama za ta lullube su.

Wannan shi yake nuna cewa; Tafsirin Alkur'ani a watan Azumi SUNNA NE BA BIDI'A BA. Ba k**ar Maulidi yake ba, wanda shi kam bidi'a ne da bata mummuna.

* Kun ga dai duka wadannan Malaman da na kawo maganganunsu babu Bawahabiye ko daya.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Kano