Sir Wisdom II

Sir Wisdom II

Share

20/06/2026

Me zai faru idan bam ya shiga cikin jikin mutum sannan kuma yaƙi fashewa?

Duk da cewa abin k**ar almara yake_ amma wannan shi ne abin da sojan Vietnam, Nguyen Van Luong, ya fuskanta a lokacin Yaƙin Vietnam wanda ya gudana a shekarar 1966.

ga yadda lamarin ya kasance:👇

Ana tsaka da rikicin fada, harsashin (mortar) ya daki Luong da ƙarfi inda har ya huda gefen cikin sa, amma abin mamakin a maimakon ya fashe dashi ƙaramin bomb ɗin ya maƙale a cikin jikinsa

Likitoci da s**a duba shi ba suyi imani da abin da s**a gani ba, bomb a jikin ɗan adam kuma bai fashe ba_ 😱

Zasu gabatar da tiyata mai hatsarin gaske ga wannan mutumin, ba wai ga shi kaɗai ba harda su likitocin domin wani kuskuren motsi, ko matsin lamba kaɗan, ko wani ƙaramin abu na iya tayar da bam ɗin da yake zaune cikin jikinsa

Tiyatar da za a yi masa ita ce ɗaya daga cikin mafi haɗari da aka taɓa gwadawa a duniya

Kafin fara aikin, ma’aikatan asibiti sun kwashe marasa lafiyan dake asibitin baki ɗaya, sannan s**a janye kowane abu daga hanya, tare da shirya komai domin duk wani abin da ka iya faruwa.

Likitocin sunyi aiki cikin tsanteni da tsananin natsuwa hannayen su basuyi rawa ba, duk da sanin cewa kuskure guda kaɗai zai iya hallaka kowa a dakin tiyatar.

Aikin yayi nasara, inda likitocin s**a cire harsashin (mortar) ɗin gaba ɗaya, ba tare da fashewa ba, kuma Luong ya tsira tsira daga wani abu da ya fi ƙarfin tunanin likitanci_ wanda sai dai ƙaddara daga Allah (s.w.a)

Labarinsa har yanzu yana daga cikin mafi ban mamaki a tarihin tsira a lokacin yaƙi, inda jarumtaka da sa’a s**a haɗu ta hanya mafi firgitarwa.

Sir Wisdom II

20/06/2026

Wata likita dake ƙasar Saudiya ta bada wani labari k**ar haka:

Wani matashi mai kimanin shekaru 30 Ɗan asalin ƙasar Saudi ya ɗauki mahaifiyar shi ya kaita zuwa ganin likita a wani asibitin dake garin madinah, Yana shiga da ita wajen likitan sai mahaifiyar tashi tana ƙoƙarin fita a guje daga wajen likitan bayan ta kwaɓe niqabinta. Matashinnan ya ɗauki niqabin ya mayar mata, ta ƙara cirewa Ya ƙara mayar mata har sau uku. Mahaifiyar tashi ta gaftaramar cizo a hannun shi, ta tofa mishi yawu a fuska, sai kawai yayi murmushi ya kalleta cikin aminci.

Daga bisani dai sai mahaifiyar tashi ta cire niqabinta da hijabinta tafara zazzagaye table ɗin likitan.

Likitan sai take tambayar wannan Matashin:

Likitan: "wayece wannan matar?"
Matashin yace: "mahaifiya ta ce"

Likitan: "ko menene labarin mahaifiyar taka?"
Matashi yace "an haifeta da matsala na ciwon hauka ne"

Likita ta ƙara da cewar; "ta yaya akayi ta haifeka kuma?"
Matashin: "Kakana ne ya tilista mahaifina ya aureta domin ta samu yaro, Don haka sai mahaifina ya aureta bayan shekara guda sai ya saketa sannan ta haifeni, kuma tun ina shekaru 10, nine nake ɗawainiya da ita na komai da komai, Hasalima koda bacci zanyi saina nemo igiya na ɗaure kafata a jikin kafarta domin kada ta gudu"

Likitan ta sake tambaya "menene dalilin da yasa ka kawota asibiti kuma?"
Matashin: "tana fama ne da ciwon sugar da hawan jini".

Sai mahaifiyar tashi ta tuntsure da dariya tace dashi: "Kabani dankali naci" sai kuwa ya yayi murmushi, ita kuwa saita kara tuntsurewa da dariya. Bayan ta gama sai ya kaita kusada wajen wanke baki a office ɗin likitan ya wanke mata baki ya sanya tsinke ya tsakule sauran abinci dake maqale a a bakinta.

Likitan ta sake jeho wata tambayar: "wannan mahaifiyar taka anya kuwa tasan kai Ɗan ta ne?"
Matashin ya ɗago kai cikin nuna alamun damuwa tare da faɗin cewa: "Billahil Azeem bata saniba, amma wanda ya halittani yasan ita uwa tace".

Sai mahaifiyar tashi ta dak**ar tsawa tace: "kai makaryaci! Meyasa bazaka kaini makkah ba?(lokacin taga an nuno makkah a TV dake office ɗin likitan).
Sai Matashin yace da ita: "sai ranar alhamis, ba nace miki ranar alhamis zan kaiki ba?"

Likitan: "yanxu a hakan zaka kaita tayi aikin umarah a makkah?"
Matashin: "ae nasaba kaita, ko sau nawa takeson xuwa indai inada lafiya zan kaita domin bani buqatar naji ta nemi wani abu ta rasa matuqar inada iko".

Bayan angama dubata s**a fice waje s**a tafi sai likitan ta kulle kofar office ɗin nata ta zauna tana sharan kuka k**ar anmata mutuwa.

Likitan tace: "naji waɗanda ke sauqe haƙƙoƙin iyayen su da yawa sosai, amma tunda nake ban taɓa jin yaron da mahaifiyarshi bata ma sanshiba amma yake ya sadaukar da rayuwarsa gareta domin samun falalar Allah duniya da lahira, yanada wadatar da zai iya kaita asibitin mahaukata amma ya zaɓi ya ɗauki ɗawainiyarta domin samun dacewa duniya da lahira.

Yan'uwa masu hankali da tunani, tabbas sayyidil waraa sallallahu alaihi wasallam yayi gaskiya inda yake cewa: "aljannah tana ƙarƙashin dugadugin kafar mahaifiya". Koda ace kuwa zaka sadaukar da rayuwarka gaba ɗayan ta, billahil Azeem baka yi komai ba ga mahaifanka.

"Rabbanagfirli wal walidayya wal mu'uminina yauma yaqumul hisab.

Allah Ya mana jagora ☺️
Sir Wisdom II pen...🖊️

12/06/2026

Ta roƙi mahaifinta kada ya biya kuɗin fansar… sai s**a harbe ta.

Labari ne mai matuƙar tayar da hankali game da wata budurwa mai shekaru 23, cike da mafarkai da buri da kyakkyawan fata na rayuwa, wadda ƴan bindiga s**a yi garkuwa da ita.

Sun nemi a biya su Naira miliyan 50 domin su sake ta.

Iyalanta sun roƙi sassauci, sun yi kuka, sun nemi a tausaya musu, amma masu garkuwar sun ƙi rage ko naira ɗaya daga abin da s**a nema.

Tsawon makonni biyu masu cike da azaba, mahaifinta ya yi iya ƙoƙarinsa. Ya aro kuɗi, ya sayar da kadarori, ya gwada duk wata hanya da zai iya bi, har daga ƙarshe ya samu Naira miliyan 50 ɗin.

Kafin ya biya kuɗin, ya kira masu garkuwar, ya roƙe su domin ya ji muryar ɗiyarsa..

Sai s**a ba ta wayar.

Maimakon ta roƙi a cece ta, sai ta gaya wa mahaifinta cewa:

“Kada ka biya kuɗin. Idan s**a sake ni, zan kashe kaina.”

Me ya sa?

Domin tsawon kwanaki goma sha huɗu, an ce ta sha fuskantar cin zarafi da wulakanci iri-iri a hannun masu garkuwar. Ta fuskanci azabtarwa da take hakkin ɗan Adam ta hanyar da babu wani mutum da ya k**ata ya fuskanta.

Ƴan bindigar da s**a ji abin da ta gaya wa mahaifinta, sai s**a katse wayar, s**a harbe ta a kai, sannan daga baya s**a aika wa iyalanta hotuna da bidiyon lokutan ƙarshe na rayuwarta.

Ƴan ta'adda sun yi garkuwa da ita, sun azabtar da ita, sun tauye mata mutuncinta, sannan s**a kashe ta.

Wannan al’amari ya wuce siyasa.

Maganar ɗan Adam ce da mutunci.

Maganar iyaye maza ne da s**a sadaukar da komai domin ceton ƴaƴansu amma s**a gamu da baƙin ciki.

Maganar iyaye mata ne da ƴaƴansu mata ba su sake dawowa gida ba.

Maganar matasa marasa laifi ne da ke rayuwa cikin fargabar kada su zama waɗanda za a kai wa hari a gaba.

Babu wata al’umma da ya k**ata ta saba da irin wannan ta’asa.

Babu wata ƙasa da ya k**ata ta ɗauki irin waɗannan labarai a matsayin abu na yau da kullum.

Allah Ya hukunta duk masu hannu a irin waɗannan munanan laifuka.

Kuma Allah Ya kawo ƙarshen garkuwa da mutane, ta’addanci da duk wani nau’in tashin hankali da ake yi wa bayin Allah a Najeriya.

Masu siyasantar da rayukan al'umma da matar da su hanyar tara ƙazaman kuɗi, Allah Ya hana su kwanciyar hankali a duniya da lahira.

10/06/2026

A dai dai lokacin da birrai s**a ji labarin mutumin da ke korar su a gonar masara 🌽 ya mutu, sai s**a k**a murna sosai...👯👯‍♂️

Shekara da ta zagayo, sai s**a samu gonar babu masara, Anan ne fa cikin ƙunci s**a fahimci cewar ashe wannan mai korar su a gonar shine manomin da ke shuka masarar 🌽 da suke ɓarnatarwa.

Don haka Ƴan'uwan masu albarka, a cikin ko wani yanayi, mu koyi zama da abokan adawar mu (Amma zaman ya zamto tamkar mangyaɗa a saman ruwa).👌

Zamu iya ƙyamatar su yanzu, amma bada jimawa ba sai mu gane ashe sune turaku da muke buƙatar takawa don mukai ga nasara.

Ba ko wane abokin adawa bane ya kasance me adawa da mu... Wasu ƴan saka ido ne domin muyi abinda ya dace, wasu kuma masu bamu horo ne da basu gabatar da kansu ba, wasu kuma haka kawai suke jin sun tsane mu ba tare da sun san dalilin hakan ba.

Mu ƙaunaci juna, mu zauna cikin aminci da juna ba tare da gaba ba.

Allah yasa mu wanye lafiya.
Sir Wisdom II

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kano