VON Hausa

VON Hausa

Share

Kafar yada labarai mai zaman kanta, tana kawo labarai kai tsaye daga Arewacin Najeriya zuwa duniya - VON Hausa Muryar Arewa

Zaku iya samun mu ta Whatsapp: 08104257364

04/05/2026

Tsohon dan takarar majalisar tarayya na Kano Municipal Engr. Yusuf Da’awah, ya fice daga jam'iyyar ADC zuwa NDC tare da Sanata Kwankwaso.

04/05/2026

Tsohon Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali, ya ki amincewa da zabin ’yan takara ta hanyar yarjejeniya da Jam’iyyar APC ta yi a Jihar Gombe.

03/05/2026

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun koma sabuwar jam’iyyar NDC, ƙasa da sa’o’i 24 bayan sanar da ficewarsu daga jam’iyyar ADC.

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kano da Anambra sun karɓi katin shaidar zama mambobin jam’iyyar ne a ranar Lahadi a sakatariyar NDC da ke Abuja.

Kwankwaso da Obi dai na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya da s**a fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, inda Kwankwaso ya tsaya takara karkashin jam’iyyar NNPP, yayin da Obi ya tsaya a LP.

Sai dai daga bisani dukkansu sun fice daga jam’iyyunsu sakamakon rikice-rikicen cikin gida da s**a dabaibaye su.

Bayan haka sun shiga ADC, amma rikicin shugabanci da matsalolin shari’a da s**a kunno kai a cikin jam’iyyar ne s**a sa s**a sake ficewa.

Shigarsu NDC na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaɓen ƙasa mai zuwa.

03/05/2026

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana matsayar tasa ne a wani sako daya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya bukaci shugaban ksa Bola Ahmed Tinubu ya soke masalahar fidda dan takarar gwamna a jihar Gombe.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Kano