USMAN USI
04/08/2025
SHUGABANNIN NIGERIA KU JI TSORON ALLAH
Yanzun nan na kai matata asibiti saboda tana labour zata haihu, muna zuwa sai muka tarar wai babu Likitoci Nurses sun tafi yajin aiki
Har ga Allah raina ya bacci sosai, kuma babban asibiti muke zuwa, yanzu bamu da wani zabi sai dai mu tafi private hospital
Wani irin sakaci ne zai sa Shugabannin Nigeria su bari Likitoci masu kula da lafiyar mutane su tafi yajin aiki?
Wannan zai iya zama mugunta, saboda su masu iko da Nigeria basa jinya a asibitocin Nigeria sai Kasashen waje, shiyasa sukayi watsi da kula da harkan kiwon lafiya a Nigeria
Ya ake son talaka yayi ne a Kasar nan?, ai ko ba komai bai kamata ayi wasa da harkan kiwon lafiya ba, tunda an gaza wajen samar mana da tsaro to bai kamata ace an gaza wajen kula da harkan kiwon lafiya ba
Gashi labour ya kamata matata gadangadan, kuma asibitin muke zuwa awo ance mana babu Nurses, dole a sake lissafi a kasarnan, zalunci da tauye hakki da ake mana talakawa yayi yawa
Don Allah ku sa matata a cikin addu'ah, Allah Ya sauketa lafiya
Su kuma Shugabannin Nigeria Allah Ya shiryar dasu wadanda ba zasu shiryu ba Allah Ya kawar da su
Datti Assalafiy
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Website
Address
Kano