Muazu messenger

Muazu messenger

Share

07/05/2025

Idan namiji yana tsananin son mace da gaske,wato son gaskiya bawai na yaudara ba.

1.farkon abinda yake so wanda bai da burin daya wuce yaga ya aure ta, domin auran ta yake son yi da gaskiyar sa.

2.duk son dayake mata idan tayi kuskure bazai fasa gaya mata gaskiya ba,wannan shine soyayyar gaskiya, saboda idan kana son mutum koda zaiyi kuskure zaka gaya masa gaskiya,amma bawai mutum yyi kuskure kaki fada masa gaskiya ba.

3.akwai son kyautata daidai karfin sa.

4.kulawa da tausayin ta ,daidai iyawar sa zaina kulawa da ita yadda bazai takura mata ba.

5.akwai son iyayen ta da yan uwan ta don, namiji idan son gaske yake yiwa mace yakan dauki iyayen ta nasa hakama dangin ta komai duk abinda ya shafe ta zai zama yana girmama abin nan.

6.ba zai taba neman wani abu daga gare ta ba wanda yasan bai dace ba.

7.ko zance wanda babu amfani irin kazamar soyayyar nan bazaiyi da ita ba, saboda shi don Allah yake son ta.

8.kokarin sa a kullum ganin yadda zata tsira da mutuncin ta a ko ina ma.

9.zai gaya mata gaskiyar sa bazai gaya mata abinda yasan cewa baya dashi ba.

10.duk wani matsalar ta zaina kokarin ganin ya mata maganin wannan matsalar nata koda ace bata hanyar kudi ba, zaiyi kokarin yi mata addu'a.

Muazu messenger

07/05/2025

Duk yadda ka kai ga jarabtuwa da son wani (mace ko namiji), shi kuma bai yinka ba, KA HAƘURA!

Idan ka kamu da son wani — mace ko namiji — amma ya nuna maka cewa ba ya sonka ko yana da wani zaɓi, ka haƙura! Kada ka nace ko ka wahalar da kanka. Kada ka ɗauka cewa dole sai ka samu shi/ita, ba wata bajinta da za ka nuna domin ka tabbatar sun amshi soyayyarka. Wahalar da kanka kawai za ka yi. Kuma, BA LAIFI BA NE DON WANI YA CE BA YA SON KA!

SOYAYYA JARRABAWA ce, kuma wacce take da lada idan aka jimre ta da haƙuri da tsoron Allah. Shaykhul Islam Ibn Taymiyah رحمه الله ya ce:

فأما إذا ابتُلى بالعشق وعف وصبر فإنه يثاب على تقواه لله

"Wanda aka jarrabe shi da soyayya, sai ya kiyaye mutuncinsa, ya yi haƙuri, to lallai yana da lada bisa tsoron Allah da ya nuna" (Majmu’ al-Fatawa 10/133). Ai "إنما يوفى الصابرون أجرهم بغير حساب".

Babu bajinta a bin wanda bai sonka. Babu ladar wahalar da kanka a kan abin da ba naka ba. Allah yana sane da zuciyarka, kuma zai saka maka da mafi alheri idan ka jure, ka kasance cikin masu haƙuri.

Wani irin abu makamancin haka ya faru a zamanin Manzon Allah ﷺ. A cikin Sahih al-Bukhari, Hadisi mai lamba 5283, Ibn Abbas رضي الله عنه ya ba da labarin Mughīth, mijin Barīrah (wata baiwar da Nana A’isha ta ‘yanta).

Duk da an ɗaura aurensu, Barīrah ta ƙi shi saboda ba ta sonsa. Mughīth ya shiga cikin damuwa da kuka yana bibiyarta saboda ƙaunarta.

Manzon Allah ﷺ ya kira Barīrah, ya tambaye ta: "Me yasa ba zaki koma gare shi ba?". Sai ta ce: "Ya Ma’aikin Allah, umarni kake bani ne na koma gare shi?" Sai ﷺ ya ce: "A’a, kawai ina son na sasantaku ne". Sai ta ce: "To gaskiya bana son sa". Manzon Allah ﷺ ya bar ta ta tafi. An ce har zuwa ƙarshen rayuwarsa, Mughīth yana kuka akan soyayyarsa ga Barīrah.

Ka sani! Ba kowace soyayya ce za ka samu ba. Idan ta kasance jarrabawa, ka ɗauke ta a matsayin ƙaddara. Kamar yadda Barīrah ba ta mayar da soyayya ga Mughīth ba, haka rayuwa take. Kayi haƙuri, ka nemi lada a wurin Allah. Zai baki/zai baka mafi alheri. Rashin

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Telephone

Website

Address

Jos