Mufty Bakery
19/09/2025
MUMBARIN JUMA'AH.
LADANKA YANA GA ALLAH
💖- A duk Lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya karbe wani abu daga gare ka, to zai chanja maka da wani abu mafi alkhairi, amma fa idan ka kasance mai hakuri da daukan kaddara sannan kuma ka nemi ladanka a wurin Allah.
🌹- Manzon Allah (ﷺ) ya ce :"Duk Wanda Allah Madaukakin Sarki ya dauke masa ganinsa kuma yayi hakuri, to za a saka masa da gidan aljannah".
💖- A cikin wani hadisin kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce: "Duk Wanda ya rasa wani daga cikin masoyansa a nan duniya kuma sannan ya yi hakuri ya nema ladarsa a wurin Ubangijinsa, za a saka masa da gidan aljannah."
💖- Don haka kar da ka yi bakin cikin a kan wata masifa da ta sameka, saboda wanda ya kaddara maka ya yi maka wani tanadi a gidan aljannah matukar ka yi hakuri: Lallai Allah zai maka sakamako da gidan aljannah. ALLAH YA ƘARA MANA HAƘURI A CIKIN KOMANMU. AMIN...
BARKA DA JUMA'AH🕌
#
17/09/2025
BANGA RICE RECIPE
1- Shinkafa 3 Cups
2- 2 Albasa Manya 2
3- Bushash-shen Kifi ( Daidai Musali )
4- Palmnut Extract 3 Cups
5- 1/4 Ground Crafish
6- Cube Maggi 3
7- Cokali 3 Chili Paper Salt
8- Scent Leafs,Ko Pumpkin (Zabi ne)
9- Banga Spices, kadan
10 Beef, Assorted Meat ETC. ( Zabi Ne )
PROCEDEURE ( YANDA ZA A HADA )
Mataki Na - 1
Idan za a yi dahuwar da Beef ne ko kuma Ganda ( Ponmo) za a wanke sosai da sosai ne sannan sai a zuba a cikin Tukunya. Gishiri, abubuwan sanya dandano da ake so ( Seasonings ) Albasa, Cameroun Paper da kuma ruwa. Sannan sai a rufe Tukunyar, a dafa har zuwa lokacin da Deef din, ko kuma Gandar zaiyi laushi.
Mataki Na - 2
Idan an kammala dahuwar Deef din, sai kuma a dauko Shinkafa a wanke a durata akan wuta, amma a zuba ruwa a ishash-she, kuma idan an zo dafawar za a dafa ta ne bisa rabin kaso na ainahin dahuwarta. Idan za a sauke Shinkafar za a zuba ta ne a cikin abin tacewa ( Sieve ) sannan sai a zuba mata ruwan sanyi daga sama na yanda zata sake wankuwa. Daga nan kuma sai a ajiye ta a gefe guda.
Mataki - 3
Za a yayyanka Albasa, A wanke Crayfish, Sannan Scent Leafs shima a yayyanka. Idan an kammala sai a zuba Banga Extract a cikin Tukunya sannan a dan soya bisa zafin wuta takaitacce.
Mataki - N 4
A cikin Tukunya ko kuma Kaskon da aka Soya Banga Extract sai a zuba, bushash-shen Kifi, Crayfish, Abubuwan sanya Dandanon ( Seasonings ), Chilli Paper, Banga Spices. Sannan sai a juya, kafin daga karshe a zuba gishiri domin daidaituwar dandanon girkiGirkin. Nan ma za a rufe ne, sannan a dafa na kimanin mintuna 5 haka, kafin daga bisa sai a dauko Beef ko kuma Ganda din nan dage gefe sai a zuba a ciki, sannan a zuba ruwa kadan a sake rufewa na tsahon mintuna 5.
Mataki Na - 5
Za a zuba Shinkafar da aka tafasa tun daga farko a cikin wannan hadin na Banga Broth, sannan sai a juya shinkafar su hadu sosai da sosai, daga nan kuma sai a kara rufe Tukunyar har zuwa lokacin da ruwan da aka zuba zai kusan tsotsewa, wanda daga nan ne za a zuba Scent Lv
12/09/2025
Idan Kana Da Mace Me Kirki A Rayuwarka Kada Ka Raina Ta. 😍
Click here to claim your Sponsored Listing.