Kwallon KAFA update

Kwallon KAFA update

Share

Photos from Kwallon KAFA update 's post 01/03/2026

AN GAMA: kasar Iran ta fice daga fafata gasar cin kofin duniya a hukumance kuma ba za ta yi tafiya zuwa Amurka domin fafata wasannin gasar cin kofin duniya ta 2026 ba. ❌

Suna da wasanni uku na rukuni, duk za su gudana a Amurka. 🇺🇸

Iran ta yi imanin cewa rayuwa ba za a iya kwatanta ta da ƙwallon ƙafa ba kuma ba za ta ɗauki haɗarin zuwa gasar cin kofin duniya ba.

● ✔️✔️✔️

28/02/2026

Pep Guardiola a kan magoya bayan Leeds United da s**a k**a ihu bayan an dakatar da wasan su domin ƴan wasa Musulmai su sha ruwa.

“Muna cikin duniya mai ban mamaki. Ku kalli abubuwan da suke faruwa a duniyar nan a halin yanzu, a yau ma gashi ya sake faruwa a wannan filin wasa.

“Ya k**ata mu girmama addinin kowa, ya k**ata mu girmama bambance-bambance dake tsakanin mu. Wannan shine! Dokace aka kafa, Premier League da kansu sune s**a bayar da damar a dakatar da wasa don ƴan wasa Musulmai su sha ruwa a wannan watan na Ramadan, kuma hakan zai iya ɗaukar minti 1 ko 2, domin dai ƴan wasan.

“Haka tsarin abun yake, amma kalli abun takaici.”

• ✔️✔️✔️✔️✔️

28/02/2026

Mafi yawan zura ƙwallaye a Barcelona wannan kakar a gasar La Liga:

17— Lamine Yamal (11 a La Liga)
16 — Ferran Torres (12 a La Liga)

• ✔️✔️✔️✔️

28/02/2026

Antoine Griezmann bai taba lashe gasar La Liga ba duk da ya shafe shekaru 17 a gasar.

A cikin shekaru 3 da ya buga wa FC Barcelona, Atletico Madrid a wannan lokacin Real Madrid ce ta lashe gasar, bayan ya bar Atletico ta lashe gasar, bayan barin Barcelona itama ta lashe gasar.

● ✔️✔️✔️✔️✔️

28/02/2026

Albarkacin wannan watan mai daraja, muna addu'a Allah ta'ala ya baiwa ƙasar Iran 🇮🇷 nasara akan waɗannan azzaluman (America da Isra'ila)

Musulmi sucigaba da addu'a da nemawa al'ummar ƙasar Iran nasara awurin Allah mabuwayi maigirma saboda azzalumai sun sako addinin muslunci da ƙasashen musulmi gaba a duniya

Wajibi ne mu jingine aƙida a wannan gaɓar, saboda bahaushe yace (da baƙi ƙirin - gara baƙi)

Ya Allah ka kare Iraniyawa da ƙasar Iran ameen.ba

28/02/2026

MESSI UPDATE ✔️✔️

Inter Miami CF za ta kai ziyara zuwa White House a ranar 5 ga Maris domin murnar nasarar da ta samu a gasar MLS Cup.

Har yanzu ba a tabbatar ko Lionel Messi zai halarta ba. Idan ya je, wannan zai kasance ziyararsa ta farko zuwa White House.

Kwallon KAFA update

28/02/2026

AKWAI KYAUTA TA KATI ✔️🏆🪴✅

SHIN A GANINKU NAWA DA NAWA KUKE HASASHEN ZA A TASHI? KU RUBUTA MANA A COMMENT SECTION ✔️✔️

Kwallon KAFA update

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Jigawa
Hadejia