Hadejia Emirate Youth Forum

Hadejia Emirate Youth Forum

Share

Guri, Kirikasaamma, Birniwa, Malammadori, Kaugama, Auyo, Kafin Hausa duk Hadejiwane, "tsintsiya madaurinki daya"

Founder
Comrade Muhammad Babangida Muhammad
08064822229, 07052799752
[email protected]
[email protected]

Photos from Hadejia Emirate Youth Forum's post 22/10/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UUN.

GASKIYA MUNA CIN CITTA A ƘASAR NAN. ALLAH YA KAWO MANA SAUƘI.

A zangon farko na shekarar 2023, da kuɗi NAIRA MILIYAN ƊAYA ina sayen buhunan CITTA guda hamsin daga kasuwar Kurmi Kano zuwa Haɗejia, duk mako ina sayarda kamar buhu 100 akan N22,000. Idan aka kawo mini buhunan cittar nan aka jibge mini su a ƙofar shagona kowa yazo shigewa sai ya sake duba kayan nan, ni kaina har wani ƙarfi nake ji a jikina, saboda ina da ƙarfin jari, kuma Alhamdulillah, ana samun ribar Dubu ɗaya zuwa Dubu ɗaya da rabi a kowane buhu duk mako.

A halin yanzu wannan Naira MILIYAN ƊAYAN buhu 3 kacal zata iya saya mini sai a bani chanjin da bai shige Naira Dubu goma ba wanda da su za a biya kuɗin mota da na dako daga kasuwar Kurmi zuwa Haɗejia.

Ku duba bambancin giɓin da kyau kuma da idon basira, Daga buhu 50 zuwa buhu 3 kacal Kuma a kuɗi ɗaya, Subhanalillahi 😭😭😭

A wancan lokacin ɗankoli ɗaya yana sayen buhu 3, 4, 5 har zuwa 10, Amma a yanzu ba wanda yake iya sayen koda rabin buhu, sai dai kwano ɗaya zuwa biyu ga masu ƙarfi kenan a cikin masu sana'ar mu ta KOLI.

Ƙananan ƴan kasuwa da yawa sun karye, sakamakon matsananciyar tsada ta sanya suna yin CINIKI-ƁATAR. Gaskiya ƙananan ƴan kasuwa suna cikin halin ni -ƴasu ga ƙarancin taimako a tsakaninmu, sakamakon kowa-ta-kansa-yake.

CITTA dai ba abinci ba ce, amma SINADARI ce mai inganta ɗanɗanon abinci, sannan kuma ana Sanya ta a magunguna da yawa.

Muna addu'ar Allah ya kawo mana sauƙin wannan tsanani Na tsadar rayuwa, amin.

13/02/2024

Yadda aka yi hada-hadar kudaden waje zuwa Naira a kasuwar sauyin kudi ta Wapa da ke jihar Kano.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Hadejia