Sports Hausa News

Sports Hausa News

Share

29/05/2026

🚨🚨 LABARI DA DUMI-DUMI: Ana cikin matakin ƙarshe na tattaunawa tsakanin Enrique Riquelme da Mikel Arteta domin ya zama sabon kocin Real Madrid idan Riquelme ya lashe zaɓen shugabancin kulob ɗin. 🤍👔

📋 Rahoton OKDiario ya ce:

◉ Tattaunawar ta kai mataki mai nisa
◉ Arteta na daga cikin manyan zaɓukan Riquelme
◉ Komai zai dogara ne da sakamakon zaɓen shugaban Real Madrid

👀 Idan hakan ta tabbata, Arteta zai iya barin Arsenal FC domin komawa Santiago Bernabéu a matsayin koci. 🔥⚪

🤔 Shin menene ra’ayinku?

29/05/2026

🚨🇦🇷 Julián Álvarez, Valentín Barco da Nicolás Otamendi sun riga sun fara atisaye a Lionel Andrés Messi Camp. 🏃‍♂️⚽

🏆 Zakarun duniya sun sake haɗuwa, kuma tafiyar kare kambun Kofin Duniya a hukumance ta fara. 🇦🇷✨

❤️ A watan Maris na 2023, Argentine Football Association ta sauya sunan cibiyar atisayen tawagar ƙasar daga Ezeiza zuwa Lionel Andrés Messi Training Centre, domin karrama Lionel Messi bayan jagorantar Argentina zuwa lashe Kofin Duniya na 2022. 🐐🇦🇷👑

🔥 Burin yanzu shi ne kare kambun duniya da s**a lashe a Qatar. 🏆🌍

Photos from Sports Hausa News's post 28/05/2026

🚨🏴󠁧󠁢󠁥󠁮󠁧󠁿Ƙasar Ingila za ta samu wakilcin ƙungiyoyi tara (9) da za su fafata a gasar Turai kakar wasa mai zuwa, wanda hakan ya zama tarihi ga ƙasa guda ɗaya…

𝐔𝐂𝐋 (UEFA Champions League):
• Arsenal
• Manchester City
• Manchester United
• Aston Villa
• Liverpool FC

𝐔𝐄𝐋 (UEFA Europa League):
• AFC Bournemouth
• Sunderland AFC
• Crystal Palace FC

𝐔𝐄𝐂𝐋 (UEFA Europa Conference League):
• Brighton & Hove Albion FC

Wannan na nuna cewa kusan rabin ƙungiyoyin gasar Premier League ne za su wakilci Ingila a gasar Turai 😮‍💨

Ta hanyar [TANGA SPORTS 360]

28/05/2026

✈️ Jadawalin Anthony Gordon na yau:

Zai isa Barcelona da misalin ƙarfe 12:20 GMT cikin jirgin kansa mai zaman kansa daga Newcastle upon Tyne. 🛩️

Da zarar ya sauka, zai yi ɗan cin abinci cikin gaggawa kafin ya wuce asibiti domin yin gwajin lafiya (medical). 🏥

Bayan kammala medical:
✍️ Zai ci gaba da kammala sauran takardu da matakai na ƙarshe kafin sanya hannu kan sabon kwantiraginsa.

🔵🔴 Daga nan ake sa ran FC Barcelona za ta sanar da ɗaukarsa a hukumance. 🔥

[in ji SPORT]

Want your business to be the top-listed Media Company in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

School Of Nursing
Hadejia