Hadejia People's Union

Hadejia People's Union

Share

Hadejia a farko — ita ce gaba da komai🐎

Muryar al'ummar kasar Hadejia baki ɗaya. 🗣️🤝

Ba don jam’iyya ko siyasa ba — don ƙasar Hadejia da cigabanta.❤️

Hadejia ta kafu saboda sadaukarwar magabatanmu. 🕋⚔️

Za mu bunƙasa ta koda za a zubar da jininmu🩸

Photos from Hadejia People's Union's post 16/05/2026

ALBARKAR HADEJAWA ALQUR'ANI DA SUNNAH ALHAMDULILLAH

Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, ya halarci bikin saukar Alƙur’ani mai girma na Makarantar Markazul Ulumul Qur’an Islamiyya Agumau, Hadejia, wanda ya ƙunshi ɗalibai mata guda ashirin da uku (23), ’yan mata goma sha biyu (12) da matan aure goma sha ɗaya (11),

16/5/2026.

©️ HADEJIA PEOPLE'S UNION ✍️

09/05/2026

KASAR HADEJIA TUSHENA

SARKIN HADEJIA SARKINA

GARIN HADEJIA MAHAIFATA

JIGAWA ABAR ALFAHARINA ✊

26/04/2026

Kasar Hadejia ✊⚔️

Photos from Hadejia People's Union's post 26/04/2026

MUNA ALFAHARI DA ASALINMU ✊⚔️

Ga Hotunan Wasu Daga Cikin Kayan Tarihin Masarautar Hadejia.

1.Bulalar Sarki Buhari
2.Sirdi Talha Na Sarki Abdulkadir
3.Sirdi Bagariye Na Sarki Usman
4.Bindigar Sarki Muhammadu
5.Dala'ilu Na Sarki Usman
6.Kundin Rubuce Rubucen Sarki Abdulkadir
7.Qur'anin Sarki Haruna Wanda Ya Rubuta Da Hannunsa
8.Wasikun Sarki Muhammadu Sarki Haru Babba Zuwa ga Sarkin Musulmi Da Wazirin Sokoto Da Sauran Sarakuna.

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Hadejia