Source Atiku forum
17/11/2021
An Kashe Mutane 14 A Sabon Harin Sokoto
Daga Abdul Dan Arewa
Akalla mutane 14 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a kauyukan karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Maharan sun kai harin ne sa’o’i kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sake tura karin kayan aikin soja zuwa jihar domin magance matsalar rashin tsaro.
Wani mazaunin unguwar Sabon Birni wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce ƴan bindiga sun mamaye wasu kauyukan gundumar Unguwan Lalle, a daren ranar Talata.
A cewarsa, sun kashe Abdullahi Usman a garin Unguwan Lalle, tara a kauyen Tsangerawa, hudu a Tamindawa.
Haka kuma sun bude wuta kan wata motar kasuwanci a kauyen Gajid, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku ciki har da direban motar.
Wasu fasinjoji biyar, wadanda s**a samu raunuka a harbin bindiga, a halin yanzu suna samun kulawa a wani asibiti.
An kuma ce barayin sun yi garkuwa da mutane uku a kauyen.
Daga baya dai an sako wadanda abin ya shafa bayan yarjejeniyar da aka yi cewa mutanen yankin za su biya harajin Naira miliyan biyu nan da ƴan kwanaki.
Sai dai kwamishinan ƴan sandan jihar Mista Kamaluddeen Okunlola ya ce maharan sun kashe mutane takwas.
A hirarsa da Aminiya, Kwamishinan ya ce, “Sun far wa wasu kauyuka masu nisa da ba sa isa saboda rashin hanya. Amma da yardar Allah za mu same su. Muna aiki a kansu.
"Ko a daren jiya, shugaban kasa ya ba da umarnin a kara kayan aikin soja zuwa Sokoto," in ji shi
A halin da ake ciki kuma, rundunar tsaro ta farin kaya da Civil Defence reshen jihar Sokoto ta tabbatar da kashe wani direban su da ke aikin ceto a unguwar Running Sambo.
Kakakin rundunar, Hamza Adamu Illela, ya ce ba ƴan bindiga ne s**a kashe jami’in (an sakaya sunansa) ba.
“Mun samu kiran waya cewa, wasu ƴan bata-gari na kai hari a wani gida a yankin, kuma cikin gaggawa jami’an mu s**a amsa kiran kuma ana cikin haka ne aka bindige direban mu,” inji shi.
09/11/2021
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar a Faransa a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2021.
Hoto: Buhari Sallau
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Gombe
00071