Gombawa
Gombawa TV is a digital television platform that broadcasts a wide range of content, including news, entertainment, and cultural programs, with a focus on Northern Nigeria.
05/06/2026
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.
Allah Ya yi wa Malam Abubakar Sadiq Pharmacy rasuwa a yau a garin Kano.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya sa wannan ya zama ƙarshen wahalarsa, Ya ba iyalansa, abokansa, da al'ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.
Allahumma-ghfir lahu warhamhu wa 'afihi wa'fu anhu.
Ameen.
03/06/2026
Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Nuna Matuƙar Damuwa Kan Sace Ɗaliban Federal Polytechnic Kaura Namoda A Jihar Zamfara
…Ƙungiyar ta ce cigaba da hare-haren ‘yan bindiga kan ɗalibai na barazana ga ilimi da zaman lafiyar al’umma a Arewacin Najeriya.
Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”
Ƙungiyar "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin shugaban kungiyar na ƙasa Comr Haidar H Hashim, ta bayyana matuƙar damuwa da alhini kan rahotannin da ke nuna cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai guda bakwai na Federal Polytechnic Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace ɗaliban ne daga matsuguninsu da ke yankin Low-Cost a garin Kaura Namoda, lamarin da ya sake jefa iyayen ɗalibai da al’ummar yankin cikin fargaba da rashin tabbas.
Ƙungiyar ta bayyana wannan hari a matsayin wani babban abin takaici da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a wasu sassan Arewacin Najeriya, musamman a wuraren da ya kamata ɗalibai su kasance cikin kwanciyar hankali suna gudanar da karatunsu.
A cewar ƙungiyar, yawaitar hare-haren da ake kaiwa makarantu da matsugunan ɗalibai na iya haifar da koma baya ga harkar ilimi, tare da kara tsoratar da iyaye daga tura ‘ya’yansu neman ilimi.
Ƙungiyar ta jaddada cewa akwai buƙatar jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban da aka sace tare da tabbatar da kamo waɗanda s**a aikata wannan ɗanyen aiki, domin su fuskanci hukuncin da ya dace.
Haka kuma, "Arewa Media Writers" ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Zamfara da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro a cibiyoyin ilimi da matsugunan ɗalibai, domin hana sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya kare rayukan waɗanda aka sace, Ya ba jami’an tsaro nasarar ceto su cikin koshin lafiya, tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Director, Media and Publicity I
"Arewa Media Writers"
03/06/2026
'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Bakwai a Zamfara
Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace dalibai bakwai na makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da daliban ke zaune a wajen harabar makarantar, a yankin Low-Cost da ke garin Kaura Namoda.
Lamarin ya haifar da fargaba da tashin hankali tsakanin ɗalibai da mazauna yankin, yayin da jami'an tsaro s**a fara bincike da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Ana ci gaba da jiran ƙarin bayani daga hukumomin da abin ya shafa game da wannan al'amari.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Gombe
741212