Ibrahimfky

Ibrahimfky

Share

12/04/2026

DA YAWA BASU SAN WANI ABU GAME DA TAURARI BA.

Mutane da yawa suna kallon rayuwa ne ta fuskar abin da ido ke gani kawai. Su kan ɗauka cewa duk nasara tana fitowa ne daga aiki, duk jinkiri kuma daga rashin sa’a ko gazawa.

Amma akwai wani ɓangare na rayuwa da ba a gani da ido kai tsaye.
A ilimin taurari, ana kallon lokaci a matsayin abu mai rai. Kowane lokaci yana zuwa da irin yanayinsa, irin ƙarfinsa, da irin damar da yake buɗewa ko rufewa.

Shi ya sa abu ɗaya idan ka yi shi a wani lokaci zai yi sauƙi, amma idan ka maimaita shi a wani lokaci daban sai ya zama mai wahala.
Ba don ka canza ba. Lokaci ne ya canza.
Akwai lokacin da yanayin taurari ke taimaka wa fara abu. A irin wannan lokaci, ƙananan matakai kan haifar da manyan sakamako.

Akwai kuma lokacin da yanayin taurari ke nuna jinkiri, ruɗani, ko rikici. Idan mutum ya nace a irin wannan lokaci, yana iya gajiya ba tare da ya ga sakamakon da yake so ba.
Ka taɓa mamakin dalilin da yasa
Kana samun kwarin gwiwa a wasu kwanaki ba tare da wani dalili ba?
Kana jin komai ya tsaya cak a wasu lokuta duk da ƙoƙari?
Kana haɗuwa da wasu mutane cikin sauƙi, amma da wasu komai sai ya rikice?
Sau da yawa, akwai abin da lokaci yake faɗa.
Ilimin taurari yana taimakawa wajen gane
Lokacin da ya dace a fara abu
Lokacin da ya dace a jira
Lokacin da ya dace a shiga mu’amala
Lokacin da ya dace a yi hattara
Amma ba za a iya fahimtar wannan ga kowa iri ɗaya ba.
Saboda kowane mutum yana da nasa burji, nasa taswira, da nasa yanayin taurari da ke tasiri a rayuwarsa.

Abin da ya dace da wani, yana iya zama bai dace da kai ba.
Lokacin da ya buɗe wa wani ƙofa, yana iya zama naka lokacin gwaji ne.

Shi ya sa sanin burujinka da yanayin lokacinka ba wasa bane. Yana iya canza yadda kake kallon rayuwa da yadda kake yanke hukunci.
Tambaya ita ce
Shin kana sanin lokacin da ya dace da kai?
Shin kana sanin irin mu’amalar da ta fi anfani a gare ka?

Shin kana sanin dalilin da yasa wasu abubuwa suke maimaituwa a rayuwarka?
Idan baka sani ba, wataƙila kana rayuwa ne ba tare da ka karanta taswirar hanyarka ba.
Wani lokacin, ba ƙarfi ake buƙata ba.
Haske ake buƙata.

Ibrahim fky al-falaky ✍️ 07033105536

07/04/2026

DARASI DAGA SIRRIN TAURARI

A ilimin taurari, akwai wani ginshiƙi da ba kowa ke fahimta ba.
Wannan ginshiƙi yana nuna cewa rayuwar mutum ba ta tafiya akan layi ɗaya , sai dai tana tafiya ne tsakanin ƙarfi biyu masu jan juna.
Akwai lokacin da ƙarfin fara abu yake rinjaye a cikinka. Kana jin ƙwazo, kana son ɗaukar mataki, kana jin cewa lokaci ya yi da zaka motsa rayuwarka gaba.
Sai kuma wani lokaci, wani sauyi ya sauka a zuciya. Ka fara tunani, ka fara duba sakamako, ka fara jin cewa akwai abin da ya kamata ka kula da shi kafin ka yi gaba.

Tambayar ita ce shin wanne ne gaskiya?
Amsar ita ce duka biyun gaskiya ne. Amma ba a lokaci ɗaya ba.

Ilimin taurari yana koyar da cewa kowane lokaci yana da irin ƙarfin da yake ɗauke da shi. Akwai lokacin da ya dace ka yi gaggawa, akwai kuma lokacin da ya dace ka yi haƙuri. Akwai lokacin fara abu, akwai lokacin dakatarwa.

Matsalar yawancin mutane ita ce suna rayuwa ba tare da sanin wane lokaci suke ciki ba.
Shi ya sa mutum zai fara abu a lokacin da bai dace ba, ya kasa kammalawa. Ko kuma ya tsaya a lokacin da ya kamata ya motsa, sai dama ta wuce shi.

Shin ka taɓa tambayar kanka
Me ya sa wasu abubuwa idan ka fara su suna tafiya cikin sauƙi? Me ya sa wasu kuma duk yadda ka yi ƙoƙari sai sun rushe?
Shin ka taɓa tunanin cewa ba lallai matsalar daga gare ka ba ce… watakila lokaci ne bai dace ba?

A ilimin taurari, akwai tsarin da ake bi domin gane lokacin da ya dace a fara abu
lokacin da ya dace a jira
lokacin da ya dace a shiga mu’amala
da lokacin da ya kamata ka kauce gaba ɗaya
Amma wannan ba abu bane da ake gani da ido kawai. Ana buƙatar fahimtar burujinka, yanayin taurarin da suke tasiri a kai, da kuma yadda suke motsawa a halin yanzu.

Idan baka san burujinka ba, kana tafiya ne cikin duhu.
Idan baka san lokacin da ya dace da kai ba, kana iya yin ƙoƙari a lokacin da bai dace ba.
Wannan ne sirrin da yasa wasu suke samun nasara cikin sauƙi, wasu kuma suna wahala duk da ƙoƙari.

Tambayar ita ce
Shin ka san burujinka da yadda yake tasiri a rayuwarka?
Shin ka san wane lokaci ne ya dace da kai ka fara abubuwa masu muhimmanci?
Shin ka san irin mu’amalar da tafi dacewa da kai da kuma wacce zata iya cutar da kai?

Idan baka sani ba, to har yanzu akwai wani ɓangare na rayuwarka da baka gano ba.
Kuma idan ka gano shi… abubuwa da yawa zasu fara sauyawa.

Wani lokacin, ba ƙoƙari ake buƙata ba… fahimta ake buƙata.
ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

25/01/2026

HISAB
shin idan ka ɗebe 9-9 acikin adadin sunanka bayan ka jimlacesu nawa yake ragewa ?

Misali Ni sunana Ibrahim adadin sunana 259
to bari mu dunƙula adadin don lissafin yaimana sauƙi
9×10=90
90×2=180
259-180=79
79-45=34
34-18=16
16-9=7
number 7 shine adadin da yake ragewa bayan an ɗebe 9-9 a cikin adadin sunnan Ibrahim, sannan Akwai sunaye da yawan gaske wanda 7 ke ragewa
haka akwai masu rage 1/2/3/4/5/6/8/ko 9

Sannan kasantuwar sunanka ya rage wata number a cikin 1zuwa 9 hakan baya nufin cewa kazama mai burujin dake ɗauke da wannan number in mun ɗauka daga himlu (Aries♈)

misali ga wasu sunaye da suke rage number dake farkon sunan da kuka gani a rubuce

1Khadijat
2 Muhammad, Aliyu, Hussain, maryam
3 yusuf, hafsat
4 Nuhu, Umar
5 mahdi
6 zainab, Abubakar, hawwa'u
7 Ibrahim, Abdullah Aisha
8 musa, ahmad
9 fatima, Hassan, adam, habiba

acikin sunayen nan duk number da kuka gani a farkon suna to itace adadin number dake ragewa idan an ɗebe da 9/9

wannan adadi shi ke sabbaba sauyawar dabi'ar waɗanda number su ta saɓa da number burujinsu

misali duk mai suna Ibrahim, Abdullahi ko A'ishah da duk wanda sunansa ke rage 7 to dole sai ya tasirantu da dabi'un number 7
ko shi nari ne ko hawa'i ko ma'i ko urabi ne.
wannan nema yasa kakejin an keɓe wassu sunaye sai kaji anace ai duk mai suna kaza yana da zafi ko wayo ko fadɗa ko haƙuri kuma in ka natsu ka duba daƙyau sai kaga lallai akwai hakan

Sannan da waɗannan Numbers ake gane mai rinjaye da wanda ake rinjaye akansa wato (galib wal maglub)

sabida haka dabi'u zahiriyya basu taƙaitu a iya burujin ruhi kaɗaiba.
domin tantance dabi'a ba tare da kuskureba
dole ana bukatar abubuwa kamar haka

1 actual date of birth
2 sunan yanka naka da na mahaifiyar
3 ɗabi'ar harufan sunanka/ki
4 numbers na sirri naka/ baki
5 ranar haihuwar da lokacin.

waɗannan abubuwan suna da matukar muhimmanci ga mai son sanin ainihin kansa
amma ba kowa yakeda wannan damarba
Sannan kuɓucewar wannan dama daga gareka baya nufin bazakasan kankaba.

kwantar da hankula lallai zamusan kanmu amma gwargwadon abinda Allah yaso musani
domin shine mafi sani akan komai.
mu bamusani ba amma muna roƙon Allah ya sanar damu abinda yaso mu sani albarkacin manzon sa(saww) birnin ilimi da imamu Aliyu (kw) ƙofar birnin
ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Gombe

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00